2025-10-13@13:41:37 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2345

«nasara a wasan»:

    Wani mummunan rikicin ƙabilanci a ƙaramar hukumar  Birniwa ta jihar Jigawa ya yi ajalin mutane biyu, yayin da wasu bakwai suka samu munanan raunuka. Kakakin ’yan sanda ta jihar, DSP Lawan Shiisu Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin yayin da yake zantawa da manema labarai. Ya ce tawagar jami’an tsaro ƙarƙashin Operation Salama sun garzaya wurin domin dawo da zaman lafiya tare da cafke wasu mutane bakwai da ake zargi da hannu a rikicin. Ganau sun ce lamarin ya faru ne lokacin da wasu da ake zargin Fulani ne suka kai farmaki ƙauyen Dagaceri, inda suka ƙona gidaje tare da kai wa mazauna garin hari da kibau a lokacin da suke barci. Rahotanni sun ce gidaje da dama sun ƙone...
    “Shekaru goma da suka wuce, gudummawar da ma’adanai ke bayarwa ga GDP na kasarmu bai wuce 0.5% ba, amma a yau ya karu zuwa 1.8% – alkalumman NBS suka nuna a cikin rabi na biyu na 2025 wanda ba a taba ganin irinsa ba”.   Da yake tsokaci kan ci gaban fannin, Ministan ya bayyana cewa, makon hako ma’adanai na Nijeriya ya yi nuni da yadda masana’antar ke sauya tunani zuwa tsari mai kyau, da sabbin abubuwa, da ke lalubo masu zuba jari na kasa da kasa.   Ya bayyana cewa, sauye-sauyen sun tattara ne a kan gaskiya, rage haɗari, da inganta masana’antar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane 236 A Jihohi 27...
    An bayyana katin zabe a matsayin sheda da za a iya amfani da shi a muhimman wurare, kamar yadda ake amfani da fasfo da katin dan kasa a manyan kasashen duniya. Tsohon wakilin mazabar tarayya ta Birnin Kudu da Buji, Engineer Magaji Da’u Aliyu ya yi wannan tsokaci new a wata tattaunawa da manema labarai a Dutse. Ya bayyana bukatar aiki tukuru a tsakanin masu ruwa da tsaki dan tabbatar da cewar dukkan wadanda su ka cancanta sun karbi katin zaben. Engineer Magaji Da’u Aliyu ya yabawa gwamnatin Malam Umar Namadi bisa kafa kwamati na musamman a karkashin mai bada shawara kan harkokin siyasa, Alhaji Lawan Garba Bullet, domin zaburar da kananan hukumomi su bada gudummawar da za ta taimaka...
    A cewar NEMA, mutane 135,764 ne suka rasa matsugunansu, yayin da 115 aka bayyana bacewarsu, yayin da wasu 826 suka samu raunuka sakamakon ambaliyar. Bugu da kari, gidaje 47,708 sun lalace, yayin da gonaki 62,653 suka lalace a fadin jihohin da abin ya shafa.   Hukumar ta kara da cewa, daga cikin wadanda abin ya shafa sun hada da yara 188,118, mata 125,307, maza 77,423, tsofaffi 18,866, da kuma nakasassu 2,418. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ta’addanci: Ana Fuskantar Ƙarancin Man Fetur A Mali Sakamakon Datse Hanyoyin Shiga Bamako October 13, 2025 Manyan Labarai Tinubu Ya Isa Birnin Rome Don  Halartar Taron Tsaro Na Aqaba October 12, 2025 Manyan Labarai An Sauya Kwamishinan Ƴansandan Abuja Saboda Rashin...
    Shugaban kasar Amurka ya yi barazana ga shugaban kasar Rasha na aike wa Ukraine makamai masu linzami kirar Tomahawk Shugaban Amurka Donald Trump ya ce: Zai gargadi takwaransa na Rasha Vladimir Putin cewa: Akwai yiwuwar Ukraine za ta iya samun makamai masu linzami kirar “Tomahawk” idan Rasha ba ta kawo karshen yakin Ukraine ba. Da aka tambaye shi a cikin jirgin Air Force One da ke kan hanyarsa ta zuwa haramtacciyar kasar Isra’ila da Masar da yammacin ranar Lahadi ko shi da kansa zai tattauna da Putin kan batun, Trump ya ce, “Yana iya magana da shi. Yana cewa: Idan ba a warware wannan yakin ba, zai aika wa Ukraine da makamai masu linzami na Tomahawk.” Trump ya kara da...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Tinubu Ya Isa Birnin Rome Don  Halartar Taron Tsaro Na Aqaba October 12, 2025 Manyan Labarai An Sauya Kwamishinan Ƴansandan Abuja Saboda Rashin Tsaro October 12, 2025 Tsaro Sojoji Sun Kashe Kwamandan IPOB ‘Alhaji’, Da Wasu 26, Sun Kama 22 October 12, 2025
    Gwamnatin Tarayya, ta gargaɗi Ƙungiyar Malaman Kami’o’i ta Ƙasa (ASUU), cewa za ta aiwatar da dokar “babu aiki, babu albashi” idan malaman suka ci gaba da yajin aikin da ka iya zai kawo cikas ga harkokin karatu. A wata sanarwa da ma’aikatar ilimi ta fitar da yammacin ranar Lahadi, Ministan Ilimi, Maruf Tunji Alausa, da Ƙaramar Ministan Ilimi, Suwaiba Sa’id Ahmed, sun ce gwamnati tana da niyyar magance ƙorafe-ƙorafen ASUU ta hanyar tattaunawa cikin lumana. Mutumin da ya sayar da ɗansa kan N1.5m ya shiga hannu a Ebonyi Egbetokun ya sauke kwamishinan ’yan sandan Abuja “Gwamnati ta nuna gaskiya, haƙuri da kyakkyawar niyya a tattaunawarta da ƙungiyar,” in ji sanarwar. Ministocin sun bayyana cewa yawancin buƙatun ASUU, kamar ƙarin kuɗin...
    Sufeton ƴansanda na Ƙasa, IGP Kayode Egbetokun, ya maye gurbin Kwamishinan ƴansandan birnin tarayya, CP Ajao Adewale, sakamakon ƙaruwar matsalolin tsaro a Abuja. Wannan mataki ya biyo bayan matsin lamba da yake fuskanta saboda rashin gamsuwa da aikinsa tun bayan karɓar ragama daga CP Benneth Igwe. Majiyoyi daga cikin rundunar sun bayyana cewa sauya shi ya shafi yadda matsalolin tsaro ke ƙaruwa a Abuja, musamman bayan harin fashi da makami da ya yi sanadin mutuwar mai gabatar da shirye-shiryen gidan talabijin ɗin ARISE, Somtochukwu Maduagwu, da mai gadi Barnabas Danlami, a Katampe, ranar 29 ga Satumba, 2025. Gwamna Sani Ya Gana Da Ministan Ayyuka Domin Ganin An Kammala Aikin Titin Abuja Zuwa Kaduna  NAFDAC Ta Rufe Manyan Shaguna 2 Na...
    Kotun daukaka kara ta Marseille ta tabbatar da soke dokar da ta bayar da umarnin rufe makarantar sakadare ta Musulinci da ke birnin Nice. A cikin wata sanarwa da ya fitar, lauyan makarantar, Sefen Guez Guez, ya yaba da nasarar ta uku a jere” tare da bayyana fatan cewa “za a daina tsananta wa wannan makaranta gaba daya. Takadammar data shafi makarantar ta hana da Rashin haske kan kudadenta, wanda hukumomjin yankin ke zargin makarantar da ta ina take samun kudadenta kamar yadda doka ta tanada. ” An bude makarantar ne a cikin shekarar 2016 a gundumar Ariane, kuma makarantar mai zaman kanta a halin yanzu tana da dalibai 130. Rahotanni sun ce makarantar, wadda wata kungiya ce mai alaka...
    Kasashe hudu da suka fi kokari a cikin wadanda suka kare a mataki na hudu za su fafata wasannin raba-gardama, sai wadanda suka samu nasara su sake raba-gardama da wasu kasashen na waje.   A yanzu daI manyan kasashen nahiyar ta Afirka irin su Kamaru da Nijeriya suke fuskantar barazanar rasa gurbi, duk da haka suna da wasu damarmakin da idan suka yi sa’a za su iya tsintar kansu a gasar a badi.   Kasar Masar ta wuce Burkina Faso da maki biyar, sannan idan ta samu nasara a kan Djibouti shikenan ta samu tikiti. Ita kuma kasar Djibouti tana can karshen teburi ne, domin maki daya tak take da shi a wasa takwas da ta buga.   Idan ma...
    Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), ta sanar da fara yajin aikin gargaɗi na tsawon mako biyu a dukkanin jami’o’in gwamnati da ke Najeriya. Shugaban ASUU, Farfesa Chris Piwuna ne, ya bayyana hakan a ranar Lahadi yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Jami’ar Abuja. Egbetokun ya sauke kwamishinan ’yan sandan Abuja Gwamnan Kebbi ya bai wa sojoji kyautar motoci 6 da babura 30 don inganta tsaro Ya ce yajin aikin zai fara ne da tsakar daren ranar Litinin, 13 ga watan Oktoba, 2025. ASUU, ta riga ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwanaki 14 wanda ya ƙare a ranar 28 ga watan Satumba, 2025. A cewar Farfesa Piwuna, babu wani abu da aka yi don dakatar da...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya ce kasar Iran ta yi maraba a tsagaita wuta a Gaza da kuma kawo karshen kisan kiyashi wa Falasdinawa, amma ya kara da cewa HKI ba abar amincewa bace, don haka tana iya yaudara da kuma kawo karshen tsagaaita budewa junan wutar gaba daya. Abu ne da saba yi don haka Falasdinawa su yi hattara. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a jiya Asabar ya kuma kara da cewa, Iran tana maraba da dukkan abinda zai kai ga kawo karshen kisan kiyashi a gaza, wanda ya dau shekaru 2 ana yi. Ministan ya jawo hankalin Hamas da sauran Falasdina kan amincewa da duk abin HKI...
    Kasar China ta maida martani kan kasar Donal Trump na kasar Amurka, wanda ya karawa kasar kudaden fito 100% na kayakin kasar da ke shigowa Amurka. SHafin yanar gizo na ArabNews ya nakalto kasar China a jiya Asabar tana cewa zata dauki matakan da suka dace kan Karin kudanen fito na 100% wanda shugaban Trump yayi. Kuma ta yi kira ga Trump kan cewa ya rungumi tattaunawa da kasar China ya fi masa kan barazana gareta. Ma’aikatar kasuwanci na kasar China ta bayyana cewa, basa son yakin kudaden fito amma basa tsoronta. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name*...
    Irabor ya ce, littafin nasa na ƙoƙarin kawo tarihin “tasirin Boko Haram a Nijeriya ta fannoni daban-daban” da kuma “hakikanin gaskiya a kan Boko Haram, wanda na samo a lokacin ina matsayin kwamandan soji na yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya.”   Tsohon babban hafsan tsaron ya ce, babban abinda ya fi tayar da hankali a yaki da Boko Haram shi ne yawan rayukan da aka rasa. A cewarsa, “irin rayukan mutanen da aka kashe a rikicin Boko Haram yana da yawa kuma ana iya kwatanta shi da annoba.” ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwamna Sani Ya Gana Da Ministan Ayyuka Domin Ganin An Kammala Aikin Titin Abuja Zuwa Kaduna  October 12, 2025 Manyan Labarai Shugaba Tinubu Ya Yi...
    Gwamna Uba Sani ya jaddada cewa wannan titin ba na yankin Arewa kadai ba ne, ya bayyana shi a matsayin jijiyar ƙasa da ƙasa ne wadda ke haɗa yankuna daban-daban tare da ƙarfafa haɗin kai da bunƙasar tattalin arziki.   Ya kara da cewa titin Abuja- Kaduna da Kano na ɗaya daga cikin manyan ayyukan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a ƙarƙashin Manufar Sabon Fata na (Renewed Hope Agenda), wadda ke nufin sabunta manyan gine-ginen ƙasa da inganta tattalin arziki.   Yace “Wannan titi ba hanya ce kawai ba inda yace wata hanya ce ta tattalin arziki wadda ke haɗa mutane, kasuwanni, da dama a fadin Arewacin Nijeriya da ma bayan haka,”   A nasa jawabin, Sanata Umahi ya yaba...
      Ba abin mamaki ba ne cewa tsaro shi ne babban ƙalubalen da jihar Zamfara ta daɗe tana fama da shi. Daga Maradun zuwa Shinkafi, daga Anka zuwa Zurmi, matsalar ‘yan bindiga ta yi ƙatutu na tsawon shekaru.   Da yake karɓar mulki, Gwamna Dauda Lawal ya sanar da cewa “ba za a iya gina tattalin arziki ba idan tsoro ya mamaye ƙasa.”   Tun daga farkon watannin mulkinsa, ya kafa Kwamitin Tsaro na Musamman, wanda ke haɗa jami’an soja, ‘yan sanda, NSCDC da ‘yan sa-kai. Gwamnatin ta samar da motocin sintiri sama da 500, da kayan aikin zamani ga jami’an tsaro.   Har ila yau, an kafa Command and Control Centre a Gusau domin sa ido kan al’amuran tsaro...
    Al’ummomin dake garin Warwade da kewaye a karamar hukumar Dutse ta jihar Jigawa sun yi kira ga gwamnatin jihar da ta yashe madatsar ruwa ta Warwade wanda ta kasance daya daga cikin hanyar samun aikin dogaro da kai ga Mazauna yankin. Wakilinmu Usman Mohammed Zaria ya ziyarci al’ummomin da ke zaune a kusa da mmadatsr ruwan wanda aka gina ta sama da shekaru hamsin da suka gabata. Madatsar ruwan ta Warwade ta kasance hanyar samun sana’o’in dogaro da kai ga mazauna yankin, wadanda suke kamun kifi da noman rani domin samun na yau da kullum. Malam Umar Sani, wanda masunci ne a Warwade, yace da abin da yake samu daga kamun kifi yake kula da iyalan shi da kuma sauran...
    Ministan gidaje da raya birane da karkara na kasar Sin Ni Hong, ya ce yanayin sashen samar da gidaje na Sin ya kara inganta tsakanin shekarar 2021 zuwa 2025, yayin aiwatar da manufar raya kasa karo na 14, inda jimillar adadin sayar da sabbin gidaje na kasuwa ya kai fadin sakwaya mita biliyan biyar.   Ni Hong, ya bayyana hakan ne a yau Asabar, yayin wani taron manema labarai. A cewarsa, sama da Sinawa miliyan 110 sun amfana daga babban tsarin gyaran tsofaffin gidaje cikin shekarun biyar. Kazalika, tsofaffin gidaje dake unguwanni sama da 240,000 a sassan biranen Sin, sun mori shirin gyaran fuska cikin wa’adin. Don haka gaba daya, yanayin ingancin muhallin biranen Sin ya kara inganta yadda ya...
    Kwamishiniyar Ilimi ta Jihar Gombe, Dokta Aishatu Umar Maigari, ta ce talauci da nuna bambanci na daga cikin manyan dalilan da ke hana yara mata damar samun ilimi a jihar. Ta bayyana hakan ne a wajen bikin Ranar Yara Mata ’Yan Makaranta ta Duniya ta shekarar 2025, wanda Shirin AGILE tare da Access Initiative Africa da Nudge Initiative suka shirya a Gombe. Gwamnan Kebbi ya bai wa sojoji kyautar motoci 6 da babura 30 don inganta tsaro ’Yan ta’adda sun kashe sojoji 4 a wani sabon hari a Borno A wajen bikin, Uwargidan Gwamnan Jihar Gombe, Asma’u Inuwa Yahaya, ta yaba da yadda gwamnatin jihar ke ƙoƙarin tabbatar da cewa ba a bar wata yarinya a baya wajen samun ilimi....
    Baya ga Maryam Sanda, Shugaba Tinubu ya kuma yafe wa wasu mutane da dama, ciki har da Janar Mamman Vatsa, Herbert Macaulay, da Faruku Lawan, wanda tsohon ɗan majalisar tarayya ne daga Jihar Kano. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Sanatan Bauchi Ta Arewa Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP October 11, 2025 Manyan Labarai Ƴansanda Sun Ceto Mutane Uku Da Aka Sace A Kano October 10, 2025 Manyan Labarai Matsalar Tsaro: Tinubu Ya Karyata Batun Yi Wa Kiristoci Kisan Ƙare Dangi October 10, 2025
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Sanatan Bauchi Ta Arewa Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP October 11, 2025 Siyasa Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu October 9, 2025 Labarai Kotu Ta Yi Watsi Da Ƙarar Da Aka Shigar Da Tinubu Kan Sanya Dokar Ta-Ɓaci A Ribas October 2, 2025
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ƴansanda Sun Ceto Mutane Uku Da Aka Sace A Kano October 10, 2025 Manyan Labarai Matsalar Tsaro: Tinubu Ya Karyata Batun Yi Wa Kiristoci Kisan Ƙare Dangi October 10, 2025 Manyan Labarai Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC  October 9, 2025
    Ya bayyana cewa an riga an hada wadanda aka ceto da iyalansu, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike da aikin ceton domin gano wadanda suka aikata laifin da kuma kubutar da sauran wadanda ake tsare da su, idan suna nan.   A halin da ake ciki kuma, kwamandan Runduna ta 6 ta Sojan Nijeriya, Birgediya Janar Kingsley Chidiebere Uwa, ya yaba da saurin daukar mataki da hadin kai tsakanin sojoji da ‘yansanda wanda ya kai ga nasarar aikin ceton.   Ya sake jaddada kudirin rundunar wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a a Jihar Taraba.   Sai dai, ya bukaci jama’a da su ci gaba da bai wa sojoji da sauran hukumomin tsaro goyon baya ta hanyar...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Guguwar Ritaya Na Barazana Ga Ayyukan Hukumar Kwastam Yayin Da Jami’ai 825 Za Su Yi Ritaya October 10, 2025 Labarai Haramcin Haƙar Ma’adanai: Majalisa Za Ta Kawo Ƙarshen Asarar Dala Biliyan 9 Duk Shekara October 10, 2025 Manyan Labarai Ƴansanda Sun Ceto Mutane Uku Da Aka Sace A Kano October 10, 2025
    A cewarta, shirin ya taimaka wajen noman shinkafa da ta kai kimanin tan 99,452, wacce kuma kudinta ya kai kimanin Naira biliyan 13.527 tare kuma da noman rogo da ya kai kimanin tan 87,237, wanda kudinsa ya kai Naira biliyan 3.925, musamman domin a kara samar da wadataccen abinci da kuma kara bunkasa fannin tattalin arzikin jihar.   Sai dai, ta bayyana cewa; har yanzu a jihar ba a samar da wani cikakken tsari a hukumance ba, a kan tsarin na shirin na CAF wanda hakan ke haifar wa da shirin koma baya a jihar.   Ta yi kira ga sauran masu ruwa da tsaki a fannin bunkasa aikin noma, domin samun riba a jihar da su bayar da hadin...
    Duk da Najeriya na cikin yanayin damina, wanda ake ganin a lokacin ta fi samar da wutar lantarki ga ’yan ƙasarta, amma jama’a a jihohin Kaduna da Kano na ci gaba da kokawa kan ƙarancin wutar. A duk shekara jama’a na more wutar lantarki a Nijeriya a lokacin damina saboda tashoshin ruwa na samar da wutar lantarki suna aiki da cikakken ƙarfinsu. Amma, wasu masana a ɓangaren wutar sun shaida wa wakilinmu cewa duk da matsalolin masu nasaba da lalata kayan aiki da kuma ƙin biyan kuɗin wuta da wasu masu amfani da ita ke yi, kamfanonin rarraba wutar (DisCos) suna yin iya bakin ƙoƙarinsu wajen cike giɓin. Masu ruwa da tsaki sun bayyana cewa ana ƙoƙarin daidaita rarraba wuta...
    Ya kara da cewa, ana ci gaba da kokari don ganin an iske masu yin kiwon shanu a kasar nan, domin fadakar da su kan muhimmancin rungumar wannan tsari na zamani.   Sai dai, ya yi nuni da cewa; wasu al’adu na haifar da tarnaki a tsakanin wasu masu kiwon a kasar na rungumar wannan tsarin.   “Na ga wasu gidajen gona da ake yin irin wannan dabara ta zamani, sannan kuma ana bayar da kulawar da ta kamata; wanda hakan ya sanya ake iya samar da litar madarar shanu daga tsakanin lita 15 zuwa 30,” in ji Jatau.   “Akwai wasu Fulani Makiyaya ‘yan kalilan da suka rungumi wannan tsari, misali a Jihar Bauchi; inda wani makiyayi ya rungumi...
    Kasar Venezuela ta yi kira ga Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya da ya tabbatar da cewa Amurka tana yin barazana zaman lafiyar duniya Kasar Venezuela ta yi kira ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya amince cewa; Lallai Amurka tana yin barazana ga zaman lafiya da tsaro na kasa da kasa, saboda yadda sojojin Amurka suke shisshigi a tekun Caribbean, wannan batu ya zo ne a yayin zaman gaggawa na majalisar a jiya Juma’a. Wakilin dindindin na Venezuela a Majalisar Dinkin Duniya, Samuel Moncada, ya ce: “Suna ba da shawarar ayyuka uku ga kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya: Na farko, amincewa da barazanar zaman lafiya da tsaro na kasa da kasa da sojojin Amurka suka haifar a cikin...
    Shugaban ya ci gaba da cewa, a karkashin shugabancinsa, Hukumar za ta yi namijin kokari wajen bayar da goyon bayanta, wajen fitar da kayan da ba su shafi dangogin Mai ba, zuwa kasar waje, musamman ta hanyar cin giyar albakatun yanayin na Abuja da kuma na bangaren aikin noma, da birnin ke da shi. Ya kara da cewa, ta hanyar wadannan alkatun kasar da birnin ke da su, Hukumar za ta kara bayar da gudunmwarta, wajen kara bunkasa fannin tattalin arzikin kasar nan da kuma kara fitar da kayan da ba su shafi Man ba, zuwa ketare.   A cewarsa, domin Hukumar ta tabbatar da na kara mayar da hankalin wajen ganin ana bin ka’ida da kuma tabbatar da ingancin...
    “Ta yaya Jonathan zai zama barazana? Mun doke shi a baya lokacin da PDP take kan mulki.   “Idan mutum yana ganin cewa PDP ita ce kololuwar jam’iyya a Nijeriya, kuma ya sha kaye a lokacin da yake ganiyarsa, ina ganin sai makiyinsa ne kawai zai tilasta masa ya kara tsayawa takara a zaben 2027,” in ji shi.   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa ya ce a yanzu haka Jonathan ya kasance dan siyasa mai daraja, yana mai cewa komawa fagen siyasa na iya rage masa kima da kuma zubar masa da darajar da yake da shi a idon duniya.   Ya jaddada cewa Jonathan ya samu damar nuna cewa mulki bai tsole masa ido ba, domin haka ne...
    Yan sa’o’ii da janyewar sojojin HKI a wasu yankunan Gazaa aka fara gano gawakin Falasdinwa wadanda HKI ta kashe su a kan tituna da kuma karkashin burbushin gine-gine. Ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza, ta bada danarwan gani gawakin shahidan Falasdinawa 17 a cikin dan karamin lokaci da janyewar sojojin yahudawa daga wasu yankuna  A Gaza. Ma’aikatar ta ce an kawo gawaki 17 da wasu 71 da suka ji rauni, a cikin sa’o’ii 24 da suka gabata. Zuwa yau jumma’a ma’aikatar ta bayyana cewa yawan mutanen da HKI ta kashe a gaza sun kai 67,211 da wasu 169,961 na wadanda suka ji rauni daga ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023. Labarin ya kara da cewa masu neman tallafin abinci...
    Falasdinawan da HKI ta kora daga gidajensu a birnin Gaza sun kama hanyar komawa gidajensu a birnin Gaza dake arewacin yankin Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran reuters na cewa ya zuwa tsakiyar rana a yau jumm’a sojojin HKI sun janye makamansu daga babban titi wanda ya taso daga arewacin zirin Gaza zuwa kudancin yankin , wanda kuma ake kira Titin Rasheed. Sun janye zuwa inda aka amince zasu koma a wannan matakin na sabon yarjeniyar.  Hotunana daga yankin ya nuna falasdinawa gungu-gungu suna takawa da kafa zuwa arewacin zirin Gaza, daga inda sojojin yahudawan suka koresu a farkon watan da ya gabata, suka kuma hana kowa bin kan titin Rasheed. A wani bangare...
    Wannan lamari ya haifar da tambaya kan yiwuwar dorewar shirin sauye-sauye da na zamani da ake gudanarwa a karkashin jagorancin Babban Kwanturola Janar, Adewale Adeniyi.   Adewale Adeniyi, wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kara wa wa’adin mulki na shekara guda, shima zai yi ritaya daga hukumar a watan Agusta, 2026.   A halin yanzu, za a dauki babban mataki kafin a cike gibin ma’aikata da ake bukata a hukumar kwastam, musamman idan aka yi la’akari da cewa jami’ai 825 za su bar aiki ba tare da sabon daukar ma’aikata ba.   Binciken da leadership Hausa ta gudanar ya gano cewa ritayar ta shafi kowane mataki a hukumar daga manyan shugabanni, zuwa matsakaita, har da kananan jami’ai.   Daga cikin...
    Ana fargabar sojoji da dama sun rasu yayin da mayaƙan Boko Haram suka kai hari sansanin soji da ke Ngamdu, a Ƙaramar Hukumar Kaga a Jihar Borno. Rahotanni sun nuna cewa mayaƙan sun kai wa sojojin hari a sansanin da ke kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu. Ɗan Majalisa ya nemi ɗaukar mataki kan dorinar ruwa a Gombe Kwastam ta kama buhunan lalatacciyar fulawa 10,000 ana ƙoƙarin shigo da ita Najeriya Biyo bayan harin, sojoji sun rufe hanyar Ngamdu har zuwa ƙarfe 11:20 na safe, wanda hakan ya sa matafiya suka maƙale na tsawon lokaci. “Na tashi daga Damaturu da sassafe ina fatan isa Maiduguri kamar ƙarfe 9 na safe, amma da na isa Ngamdu sai muka tarar da hanya a...
    Bugu da kari, an rufe shafukan hakar ma’adanai haramtacce 98 a fadin kasar.   “An kiyasta cewa Nijeriya na asarar kusan Dala biliyan 9 a kowace shekara sakamakon haramtacciyar hakar ma’adanai. Wannan sata ta albarkatunmu da ya kamata ta bunkasa kasarmu ta wuce kima, kuma lokaci ya yi da za a kawo karshensa,” in ji Abdulraheem.   A cewar sa, kwamitin na da alhakin hana asarar kudaden shiga, tabbatar da gaskiya da adalci a harkokin hakar ma’adanai, da tabbatar da cewa dukiyoyin ma’adanin kasar suna ba da cikakken gudunmawa ga ci gaban tattalin arziki.   “Yayin da muke ci gaba, daya daga cikin manyan manufofin wannan kwamitin shi ne hana asarar kudaden shiga da haramtacciyar hakar ma’adanai da ayyukanta ke...
    Rahotanni daga Gaza na cewa Isra’ila ta fara janye sojojinta daga wasu yankuna na zirin Gaza. Wannan dai na zuwa ne bayan da gwamantin Isra’ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta dake kunshe a shirin zaman lafiya na Trump da ta cimma da kungiyar Hamas. Daraktan Hukumar Ba da Agajin Gaggawa da Hadin Kan Kasa da Kasa ta Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Gaza Mohammad Al-Moughayyir, ya ce sojojin Isra’ila sun janye daga yankuna da dama a cikin birnin Gaza da arewacin zirin da kuma wasu yankunan kudancin yankin. A Khan Younis da ke kudancin zirin Gaza, Motocin Isra’ila sun janye daga kudancin birnin da tsakiyar birnin zuwa yankunan gabashi. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of...
    Gwamnatin jihar Zamfara ta yi gargadin cewa ba za ta lamunci duk wani aiki na sakaci ko zagon kasa da zai iya kawo cikas ga kokarin da take yi na gyara da inganta harkar ilimi.   Shugaban hukumar kula da ilimin bai daya ta jihar Zamfara (ZSUBEB), Farfesa Nasir Garba Anka ne ya yi wannan gargadin a wata ziyarar bazata a makarantar firamare ta UBE, Low Cost da ke Gusau, biyo bayan rahotannin sace-sace da kuma lalata kadarorin gwamnati.   Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Ibrahim Maizare ya bayyana haka a wata sanarwa da ya ba rediyon Najeriya a Gusau.   Farfesa Nssiru Anka ya nuna matukar damuwa kan rashin kyawun kayan aiki, ya kuma bayyana lamarin a matsayin...
    Wata kafar labarai daban, Peoples Gazette, tun da farko a shekarar 2024, ta ruwaito labaran da ke zarginsa da yin jabun takardar shaidar NYSC.   Sai dai Nnaji ya karyata labarin da Premium Times ta wallafa, yana mai cewa zargin aiki ne na abokan hamayyar siyasa a Jiharsa ta Enugu.   Tsohon ministan, wanda aka nada a watan Agusta 2023, ya mika takardar murabus dinsa a ranar Litinin ga Shugaban Kasa, inda ya nuna godiyarsa kan damar da aka ba shi ta yi wa kasa hidima.   A cikin wasikar tasa, tsohon ministan ya bayyana cewa ya zama abin kai hare-hare na “tsananin batanci” daga abokan hamayyar siyasa da ke neman bata masa suna.   “Ina gode wa Shugaban Kasa...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Cutar Kwalara Na Ci Gaba Da Yi Wa ‘Yan Nijeriya Kisan Mummuƙe October 10, 2025 Manyan Labarai Matsalar Tsaro: Tinubu Ya Karyata Batun Yi Wa Kiristoci Kisan Ƙare Dangi October 10, 2025 Labarai ‘Yansanda Sun Kama Motar Hilux Ɗin Da Aka Sace A Kano A Hanyar Zuwa Nijar October 9, 2025
    Yawan mace-mace ta hanyar cutar kwalarar, na faruwa ne duk da biliyoyin Nairori da aka ce gwamnati da abokan huldar kasa da kasa suna kashewa, domin kokarin ganin an dakile ta.   Wadannan kudade sun hada da kason kasafin kudi na shekara-shekara, wanda ya kunshi miliyoyin Nairori; akwai dala miliyan 700 da bankin duniya ya bayar domin samar da tsaftataccen ruwa sha, tsaftar muhalli a fadin kasa baki-daya, tallafin dala miliyan 2 daga Majalisar Dinkin Duniya, dubban daruruwan allurar rigakafin cutar kwalara da asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) suka bayar da sauran makamantansu. Alkaluman da aka samu daga cibiyar NCDC, sun nuna cewa a cikin 2020, kasar ta samu rahoton...
    “Jami’an ‘yansanda na SIS, suka fara bincike kan rahoton, ta hanyar amfani da kaifin basira da fasaha, a hanyar filin jirgin sama, karamar hukumar Nassarawa, jihar Kano, jami’an sun kama wata mata mai suna Adama Hassan, ‘yar shekara 35 da ke da zama a karamar hukumar Deba, jihar Gombe, a ranar 6 ga Oktoba, 2025, yayin da take tuka motar da aka sace a kan hanyarta ta zuwa Jamhuriyar Nijar.   Rahotanni sun bayyana cewa, wacce ake zargin ta amsa laifin karbar motar ne daga hannun wani mutumi da ke karamar hukumar Lafiyan Lamurde, jihar Adamawa, wanda a yanzu ake nema ruwa a jallo. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Jami’an Tsaro Sun Cafke Ɓarayin Kayayyakin Turakun Wutar Lantarki Na Hanyar...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Nijeriya Ta Yi Asarar Ganga Miliyan 13.5 Na Ɗanyen Mai Ta Hanyar Sata Da Zagon-ƙasa – NEITI October 9, 2025 Labarai Batun Umarnin Kotu Na Kama Tsohon Shugaban INEC Ƙage Ne Kawai – Shugaban Jam’iyyar AA  October 9, 2025 Manyan Labarai Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC  October 9, 2025
    Gwamnatin tarayya ta yi asarar jimillar gangar danyen mai miliyan 13.5 wanda kudinsa ya kai dala biliyan 3.3 sakamakon sata da fasa bututun mai tsakanin shekarar 2023 zuwa 2024, in ji wata kungiya mai fafutukar kare masana’antu ta Nijeriya (NEITI). Sakataren zartarwa na NEITI, Dokta Ogbonanya Orji, ne ya bayyana hakan a Legas a taron kungiyar masu ba da rahoto kan makamashi ta Nijeriya (NAEC) na 2025 a Legas ranar Alhamis. Ya koka da cewa, rashin gaskiya da rikon amana ne ya dabaibaye masana’antar mai da iskar gas, yana mai cewa akwai bukatar yin gaskiya da aiwatar da sabon tunani na fasaha wajen tafiyar da harkar mai da iskar gas a kasar. Orji ya lura cewa, kudaden da aka yi...
    A bana, bikin Tsakiyar Kaka da Ranar Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin sun hadu, inda suka haifar da hutun tsawon kwanaki takwas. An yi hasashen cewa, adadin mutanen da suka yi tafiya a yankuna daban daban na kasar zai kai biliyan 2.432, tare da karuwar kashi 6.2% a kowace rana idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata. Adadin ribar da aka samu a manyan kantuna da gidajen abinci a cikin kwanaki hudu na farkon hutun ta karu da kashi 3.3% idan aka kwatanta da na bara, kuma har zuwa karfe 4:00 na yammacin ranar 8 ga watan, kudin shiga da aka samu daga kallon fina-finai yayin wannan biki ya wuce RMB Yuan biliyan 1.8 kwatankwacin fiye da dala miliyan 252....
    Rahotanni sun bayyana cewa, karar mai lamba FHC/OS/194/2024, ta nemi umarnin tilastawa INEC da shugabanta na lokacin da su sanya sunayen wasu jami’an Jam’iyyar AA a shafin hukumar na yanar gizo bayan an cire su.   Sai dai Udeze ya ci gaba da cewa, babu irin wannan hukunci ko umarnin kama shi (Yakubu), yana mai tabbatar da cewa, rahotannin ƙage ne kawai. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC  October 9, 2025 Labarai SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati October 9, 2025 Labarai An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba October 9, 2025
    Wata majiyar Falasdinawa ta bayyana cewa bayan amincewa da kawo karshen yakin Gaza,da ake tattaunawa a Sharem-Shiekh na kasar Masar, an fara aiki da tsagaita wuta a hukumance. Raidiyon HKI ya sanar da cewa, da karfe 12;00 na rana a yau Alhamis ne aka fara aiki da tsagaita wutar, don haka babu wani hari da sojojin HKI za su kai a yankin na Gaza. Majiyar Radiyon na HKI ya kuma ce; ‘Yan aiken Amurka biyu da su ne, Steven Charles Witkoff da Jared Corey Kushner sun halarci taron na Sheram-Sheikh a yau Alhamis. Jami’an Falasdinawa dai sun bayyana cewa aiki da wannan yarjejeniyar dai yana da alaka ne da yadda jami’an Haramtacciyar Kasar Isra’ila za su yi aiki da ita....
    Mai Martaba Sarkin Nafada, Alhaji Dadum Hamza ya ƙaddamar da sabuwar doka ta rage tsadar aure a masarautarsa, a Jihar Gombe domin sauƙaƙa wa matasa yin aure da kuma magance matsalolin da ke hana sauƙin yin aure a cikin al’umma. Wakilin Sarkin, Alhaji Umaru Muhammad Baraya (Madakin Nafada), ne ya gabatar da dokar yayin taron ƙaddamarwa da aka gudanar a Unguwar Madaki da ke Nafada ta Tsakiya, tare da halartar jami’an gwamnati, Alƙalan kotun majistare da jami’an tsaro. ’Yan sanda sun kama waɗanda ake zargi da kashe ma’aikaciyar Arise TV a Abuja Najeriya ta tafka asarar tiriliyan 14.5 sakamakon rikicin Boko Haram – UNICEF Dokar za ta fara aiki daga wannan shekara ta 2025, inda aka gargaɗi matasa da su...
    Shugaban ƙaramar hukumar Oredo, Hon. Gabriel Iduseri, ya ziyarci kasuwar da safiyar ranar Alhamis.Yayin ziyararsa, Iduseri, ya bayyana lamarin a matsayin babban iftila’i ga ‘yan kasuwa, tare da alƙawarin cewa za su ba su tallafi.“Wannan lokaci ne na matuƙar baƙin ciki ga mutanenmu, musamman ma ‘yan kasuwar da suka dogara da wannan waje don samun abincin yau da kullum. Ba za mu bar su su fuskanci wannan asara su kaɗai ba,” in ji shi.ShareTweetSendShareMASU ALAKA SiyasaNi Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu October 9, 2025Manyan LabaraiTattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya October 9, 2025Manyan LabaraiTinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A...
    An shawarci mata a karamar hukumar Kirikasamma da ke jihar jigawa da su kawo ‘ya’yansu domin yi musu rigakafin cutar shan inna, kyanda, da Gaida da sauran cututtuka masu ban tsoro.   Uwargidan Shugaban Karamar Hukumar, Hajiya Fatima Maji Marma ta ba da wannan shawarar a lokacin kaddamar da shirin rigakafin cutar kyanda da na rigakafi na yau da kullum a fadar Hakimin Marma.   Ta kuma jaddada aniyar karamar hukumar na bayar da tallafin da ake bukata domin samun nasarar gudanar da aikin rigakafin.   Hajiya Fatima ta kuma yabawa gwamnatin jihar Jigawa bisa bullo da inshorar lafiya ga marasa galihu a matakin unguwanni a kananan hukumomin jihar 27.   A nasa jawabin manajan hukumar kula da lafiya matakin...
    Kwamishinan kasuwanci da masana’antu na jihar Zamfara, Abdulrahman Muhammad Tumbido, ya yabawa gwamna Dauda Lawal bisa jajircewar sa wajen tallata jihar Zamfara a matsayin cibiyar zuba jari.   Kwamishinan, wanda ya bi sahun gwamna Lawal a wata tawaga ta hukuma zuwa bikin baje kolin kasuwanci da zuba jari na Canada–Africa da aka gudanar a Toronto, Canada, ya ce halartar gwamnan ya bude wa jihar sabbin damammaki na kasuwanci da bunkasar tattalin arziki.   A wata sanarwa da jami’in yada labarai na ma’aikatar, Jamilu Bello, Tumbido ya fitar, ya tabbatar da cewa ma’aikatar kasuwanci da masana’antu za ta ci gaba da bin diddigin ayyukan hadin gwiwa da yarjejeniyoyin da aka kulla a wannan tafiya.   A cewarsa, Gwamna Lawal ya baje...
    Gwamnatin jihar Neja ta bayyana shirinta na yin hadin gwiwa da kungiyar injiniyoyin ma’adanai ta Najeriya a matakin jiha da tarayya domin tabbatar da aiwatar da kudurorin da aka cimma a karshen taron kasa da kasa karo na ashirin da hudu.   Gwamnan jihar Mohammed Umar Bago ya bayyana haka a lokacin da yake bayyana bude taron shekara-shekara da taron kasa da kasa na shekara ashirin da hudu da aka gudanar a Minna babban birnin jihar Neja.   Gwamnan wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikata Injiniya Idris Abubakar ya bayyana cewa hakan ya zama dole domin dorewa da aikin hakar ma’adanai na da matukar muhimmanci wajen kare shirin makamashi maras illa a matsayin Jigon gwamnatin sa.     A nasa...
    An kashe wani yaro ɗan shekara 13 mai suna Abubakar Wada da shanu 36, yayin da wasu ’yan bindiga sun kai wa makiyaya hari a kusa da ƙauyen Inzon da ke yankin Fan, a Ƙaramar Hukumar Barkin Ladi a Jihar Filato. Aƙalla shanu 49 kuma sun ɓace ba tare da sanin inda suka shiga ba. ’Yan sanda sun kama ɗan bindiga a kan iyakar Najeriya da Kamaru Kamfanonin rarraba lantarki sun tafka asarar biliyan 358 a cikin wata uku – NERC Shugaban ƙungiyar makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN), a Jihar Filato, Ibrahim Yusuf Babayo, ya bayyana cewa harin ya faru ne da yammacin ranar Talata lokacin da wasu makiyaya uku ke dawowa daga kiwo. Ya ce ’yan bindigar sun buɗe...
    Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne, sun tare hanyar Gusau zuwa Gummi a Jihar Zamfara, inda suka sace mutane da dama. Wata majiya ta bayyana cewa, maharan sun tare motoci sannan suka yi awon gava da fasinjojin da ke ciki. Yadda Obasanjo ya ƙaddamar da cibiyar taron ƙasa da ƙasa a Bauchi Ban yi murabus don ina da laifi ba — Nnaji Wani shaida ya ce ’yan bindigar sun ɗauki lokaci suna sharafinsu kafin daga bisani suka tafi da mutanen da suka kama. Daga cikin waɗanda suka sace akwai Malam Sadis Isa, shugaban Majalisar Malamai ta Ƙaramar Hukumar Gummi, abin da ya jefa al’umma cikin tsoro da damuwa. “Da yammacin ranar Talata, ’yan bindiga sun tare hanyar Gusau zuwa...
    “Yanzu muna kammala sabbin sharuɗan aikin da ASUU ta gabatar, kuma za mu bayyana amsar gwamnati nan ba da jimawa ba,” in ji shi.“Shugaba Tinubu yana da niyyar kawo ƙarshen wannan matsala gaba ɗaya.”Ya roƙi ASUU da ta ci gaba da tattaunawa maimakon fara yajin aiki, yana mai tabbatar da cewa gwamnati na da niyyar gaskiya da jajircewa wajen warware matsalar.LEADERSHIP ta ruwaito cewa ASUU ta fara shirin tursasa wa mambobinta fara yajin aikin gargadi, yayin da wa’adin kwanaki 14 da ta bai wa gwamnati zai ƙare a ranar Lahadi mai zuwa.ShareTweetSendShareMASU ALAKA Manyan LabaraiBoko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung October 8, 2025Labarai‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato...
    Shugabar Cibiyar Nazarin Karatu da Ci Gaban Ilimi ta Najeriya (NCRRD) da ke Jami’ar Bayero Kano (BUK), Farfesa Amina Adamu, ta bayyana damuwa kan yadda dalibai ke ƙara gujewa amfani da dakunan karatu, tana danganta hakan da dogaro da kirkirarriyar fasaha ta AI. Da take jawabi a taron ƙasa da ƙasa karo na biyar kan nazarin karatu da nazari da aka gudanar a Jami’ar Bayero Kano, Farfesa Amina ta ce da dama daga cikin ɗalibai yanzu suna kammala karatun jami’a ba tare da sun taɓa shiga ɗakin karatu ko sau ɗaya ba. Yadda zargin mallakar takardun bogi ya yi awon gaba da kujerar Ministan Tinubu Joash Amupitan na iya zama sabon shugaban INEC “Muna da daliban da ke yin rajista...
    Ya buƙaci jama’a suke bambanta “gaskiya da siyasa.”ShareTweetSendShareMASU ALAKA Manyan Labarai‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio October 8, 2025Manyan LabaraiDa Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo October 7, 2025Manyan LabaraiYa Kamata Nijeriya Ta Ayyana Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda — Tsohon Hafsan Sojin Ƙasa October 7, 2025
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A zamanin nan, ana alakanta almajirai da bara – hasali ma a lokuta da dama akan yi amfani da kalmar “almajiri” idan ana nufin mabaraci. Amma a da ba haka lamarin yake ba – almajiri baya bukatar yin bara ko roko kafin ya sami na sakawa a bakin salati. NAJERIYA A YAU: Tasirin Takardun Shaida Na Bogi Ga Rayuwar Al’umma DAGA LARABA: Tasirin Bambance-bambance Tsakanin ‘Yan Najeriya Shekara 65 Da Samun ‘Yancin Kai Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi nazari ne a kan yadda almajirci ya sauya salo a wannan zamani da ma irin halin da almajirai suka tsinci kan su a ciki. Domin sauke shirin, latsa nan
    A cewarsa, gyaran yana taimakawa wajen samun bayanai daidai domin tsara ci gaba da kuma rarraba albarkatun ƙasa bisa adalci daga gwamnatin tarayya.“Wannan tsarin yana daidai da yadda ake yi a wasu jihohi, inda ake amfani da bayanan masarautu, yankuna da ƙauyuka wajen tsara ci gaba da rarraba kuɗaɗe,” in ji shi.Gwamnan ya jaddada muhimmancin sarakunan gargajiya wajen haɗa kan jama’a da tallafa wa ayyukan ci gaba, tare da tabbatar da cewa za a aiwatar da sabon tsarin cikin gaskiya.Ya yaba wa kwamitin bisa jajircewarsu da yadda suka gudanar da aikin cikin gaskiya da tsari.Tun da farko, shugaban kwamitin, Hamza Koshe Akuyam, ya bayyana cewa sun karɓi buƙatu 196, wanda 17 don kafa sabbin masarautu, 166 don sabbin yankuna, da...
    Irabor ya ƙara da cewa dole ne gwamnati ta bi hanyoyi daban-daban wajen magance matsalar tsaro, ba ta hanyar amfani da sojoji kaɗai ba.Ya ce ya kamata a samar da manufofi masu inganci da za su rage talauci, rashin aiki da yawan yara marasa zuwa makaranta.“Idan muka rage yara marasa zuwa makaranta da kuma marasa aikin yi, za mu rage yawan mutanen da ‘yan ta’adda ke iya ɗauka aiki,” in ji shi.Ya kuma gargaɗi ‘yan siyasa da su daina sa siyasa a batun harkar tsaro.A ranar bikin cikar Nijeriya shekara 65 da samun ‘yancin kai, Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa dakarun Nijeriya suna samun nasara a yaƙi da ta’addanci da garkuwa da mutane, amma jam’iyyun adawa sun ce matsalar...
    Shugaban Kamaru Paul Biya, ya bayyana cewa zai tsaya takara a wa’adi na takwas a watan Yuli, yana mai kafa hujja da cewa hakan  amsa kiraye-kirayen jama’a ne da ke neman ya ci gaba da mulkin kasar. Duk da sukar da ake yi, da kuma dimbin kalubalen tsaro da tattalin arziki, shugaban kasar da ya fi dadewa kan karagar mulki a duniya na da  damar samun nasara a zaben da za a gudanar a ranar 12 ga watan Oktoba a kasar da ke da tsakiyar nahiyar Afirka,  mai arzikin koko da man fetur. Sai dai watakila babban abin da ke fuskantar Biya a wannan karon shi ne lafiyarsa, wadda aka dade ana ta cece-kuce a kai, musamman yadda ya shafe...
    Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta sake rage kuɗin aikin Hajjin shekarar 2026 nan take, kuma ta fitar da sabon farashin cikin kwana biyu. Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan hukumar ta sanar da rafin kimanin N200,000 a kan farashin da maniyyata suka biya a bara. Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ne ya isar da umarnin shugaban kasa yayin wani taro da ya yi da shugabanni da mambobin hukumar NAHCON a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, a ranar Litinin. Shettima ya buƙaci a samu hadin kai tsakanin jami’an jihohi da na tarayya, ciki har da gwamnoni, wajen fitar sabon farashin da ya dace da yanayin tattalin arzikin ƙasar. An fara...
    A gobe Talata ce 7 ga watan Otoba, yakin tufanul-Aksa ya ke cika shekaru 2 tsakanin HKI da kungiyar Hamas wacce take iko da zirin gaza na kasar Falasdinu da aka mamaye. Jaridar ‘The National’ na kasar Amurka ta nakalto firay ministan HKI Benyamin Natanyahu yana cewa gwamnatinsa tana samun nasara a yakin, duk da cewa abinda yake kasa yana nuna akasin haka. Musamman idan an dubi manufofin HKI na fara shiga yakin. Wasu masana a HKI basu amince da da cewa Natanyahu yana samun nasara a wannan yakin ba. Wanda shi ne yaki mafi tsawo wanda HKI ta shiga tun bayan kafata shekaru kimani 80 da suka gabaya. Jaridar ‘The Nation’ ta yi hira da Nimrod Novik daya daga...
    Ya kuma tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya tana aiki don ƙirƙirar yanayi mai sauƙin zuba jari, da zaman lafiya don masana’antu, da haɓaka tattalin arziki mai dorewa. A ƙarshe, ya kira masu ruwa da tsaki da su fifita tattaunawa a wajen neman mafita maimakon rikici, yana cewa, “Nijeriya ƙasa ce mai girma da ke neman mafita a abubuwa da yawa, ya zama dole ne mu haɗa kai wajen kare abin da ke amfanar ƙasa baki ɗaya.” Tags: Aliko DangoteShettima ShareTweetSendShare Abubakar Sulaiman Related Manyan Labarai Talaucin Da Ya Ninku Fiye Da Sau Biyu A Gwamnatin Tinubu, An Ƙuduri Aniyar Kawar Da Shi Nan Da Shekaru 5 4 hours ago Manyan Labarai Uba Sani Ya Amince...
    A zaman da aka yi a yau, lauyan Ministan ya shaidawa kotu cewa an isar da takardun shari’ar ga dukkan waɗanda ake ƙara, yana mai zargin Shugaban Jami’ar UNN da saɓa umarnin kotu ta hanyar rubuta wasika ga jaridar yanar gizo Premium Times, inda ya ƙalubalanci ikirarin Nnaji na cewa tsohon ɗalibin jami’ar ne. A cewar lauyan, wannan wallafa ta karya umarnin kotu na barin komai a yadda yake har sai an saurari shari’ar. Sai dai lauyan jami’ar ya musanta yin wani kuskure, amma ya ce za su ja hankalin jami’an su don bin umarnin kotu yadda doka ta tanada. Tags: MinistaNnajiUNN ShareTweetSendShare Naziru Adam Ibrahim Related Ilimi Uwargidan Shugaban Ƙasa, Remi Tinubu, Ta Nuna Damuwa...
      Ya kara da cewa yan shekarun da suka gabata, an yi shakku kan dorewar wasan Hockey a Nijeriya, amma yanzu tawagarmu ta mata ita ce ta zo matsayi na 3 a Afirka, yayin da tawagar maza ke matsayi na 4, wadannan nasarorin sun nuna irin yadda muka himmatu wajen ganin mun kara inganta wannan wasa a Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Firaministan ƙasar Faransa, Sebastien Lecornu, ya yi murabus daga muƙaminsa kwana guda bayan ya kafa gwamnatinsa. Fira Minista Sebastien Lecournu ya sanar da ajiye mukaminsa ne a safiyar Litinin ɗin nan bayan ya yi wata da Shugaba Emmanuel Macron. Ya yi murabus ne washegarin da ya kafa majalisar ministocinsa domin tafiyar da gwamnati, kuma ƙasa da wata guda bayan Shugaba Macron ya naɗa shi a kujerar. A jiya  Lahadi ne ya sanar da sunayen mambobin sabuwar majalisar ministocinsa inda ya naɗa sabbin muƙamai, amma ya bar wasu da dama a kan kujerunsu, lamarin da bai yi wa ’yan adawa daɗi ba. Zargin takardun bogi: Jami’ar Nsukka ba ta taɓa ba ni takardar digiri ba — Minista ’Yan bindiga sun kashe...
    Kwamitin da Gwamnatin Jihar Bauchi ta kafa domin nazarin buƙatun ƙirƙirar sababbin masarautu da yankunan hakimai da dagattai, ya ba da shawarar ƙirƙirar masarautu 13, da hakimai 2 da dagattai 113 a fadin jihar. Wannan shawara na kunshe ne a cikin rahoton da shugaban kwamitin, Hamza Koshe Akuyam, ya miƙa wa Gwamna Bala Mohammed a ofishinsa da ke Bauchi. Da yake miƙa rahoton, Akuyam ya bayyana cewa masarautu 13 da yankunan hakimai biyu da aka bayar da shawarar kafa su su ne suka cancanta daga cikin sama da buƙatu 100 da aka karɓa daga sassan jihar daban-daban. Kwamitin, an kaddamar da shi ne a ranar 4 ga Yuli 2025, da umarnin ya duba buƙatun al’ummomi, ya tantance dalilan tarihi, al’ada da...
    Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC), ta fara binciken Tsohon Gwamnna Jihar, Abdullahi Umar Ganduje, kan zargin karkatar da sama da Naira biliyan huɗu zuwa aikin Dala Inland Dry Port. Ana zargin kuɗin an kashe su wajen bayar da kwangila don samar da wasu abubuwan more rayuwa a wajen aikin. Mata da yara 95,000 ke mutuwa a sanadin shaƙar hayaƙin girki — Uwargidan Fubara Fitaccen ɗan jarida a Kano, Aliyu Abubakar Getso ya rasu An gano yadda aka mayar da kashi 20 na kuɗin wanda mallakar jihar ne zuwa ga iyalan Ganduje a shekarar 2020. Wannan ya janyo an cire Jihar Kano daga cikin masu mamallaka kamfanin, inda ’ya’yan Ganduje ke riƙe...
    Uwargidan Gwamnan Jihar Ribas, Eyoanwan Bassey Otu, ta ce aƙalla mata da ƙananan yara 95,000 ne ke mutuwa a kowace shekara a Najeriya sakamakon shaƙar hayaƙin girki. Ta bayyana haka ne yayin wani taron wayar da kai da aka gudanar a ofishinta da ke Kalaba, inda ta jaddada buƙatar amfani da hanyoyin girki masu tsafta da aminci a Najeriya. Wike ya gana da Fubara da dattawan Ribas kafin kafa sabuwar majalisar zartarwa Rundunar Sojin Nijeriya ta cafke jami’anta 16 kan saɓa ƙa’idar aiki Uwargidan gwamnan, wacce Asi Akiba, matar ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Kalaba, Kalaba ta Kudu da Odukpani ta wakilta, ta ce hayaƙin itacen girki da sauran hanyoyin da ba su da inganci sun zama hanyar mutuwa ta...
    Uwargidan Gwamnan Jihar Ribas, Eyoanwan Bassey Otu, ta ce aƙalla mata da ƙananan yara 95,000 ne ke mutuwa a kowace shekara a Najeriya sakamakon shaƙar hayaƙin girki. Ta bayyana haka ne yayin wani taron wayar da kai da aka gudanar a ofishinta da ke Kalaba, inda ta jaddada buƙatar amfani da hanyoyin girki masu tsafta da aminci a Najeriya. Wike ya gana da Fubara da dattawan Ribas kafin kafa sabuwar majalisar zartarwa Rundunar Sojin Nijeriya ta cafke jami’anta 16 kan saɓa ƙa’idar aiki Uwargidan gwamnan, wacce Asi Akiba, matar ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Kalaba, Kalaba ta Kudu da Odukpani ta wakilta, ta ce hayaƙin itacen girki da sauran hanyoyin da ba su da inganci sun zama hanyar mutuwa ta...
    Uwargidan Gwamnan Jihar Ribas, Eyoanwan Bassey Otu, ta ce aƙalla mata da ƙananan yara 95,000 ne ke mutuwa a kowace shekara a Najeriya sakamakon shaƙar hayaƙin girki. Ta bayyana haka ne yayin wani taron wayar da kai da aka gudanar a ofishinta da ke Kalaba, inda ta jaddada buƙatar amfani da hanyoyin girki masu tsafta da aminci a Najeriya. Wike ya gana da Fubara da dattawan Ribas kafin kafa sabuwar majalisar zartarwa Rundunar Sojin Nijeriya ta cafke jami’anta 16 kan saɓa ƙa’idar aiki Uwargidan gwamnan, wacce Asi Akiba, matar ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Kalaba, Kalaba ta Kudu da Odukpani ta wakilta, ta ce hayaƙin itacen girki da sauran hanyoyin da ba su da inganci sun zama hanyar mutuwa ta...
    Sanata Mohammed Ali Ndume, mai wakiltar Borno ta Kudu, ya yaba wa Gwamna Babagana Zulum da Sojojin Operation Hadin Kai bisa gaggawar da suka nuna wajen ziyartar garin Kirawa bayan hare-haren da Boko Haram ta kai, wanda ya yi sanadin mutuwa da ƙone gidaje da fadar dagaci. Sanatan ya bayyana cewa harin ya tilasta wa mazauna da dama guduwa zuwa ƙasar Kamaru. A wata sanarwa da ya fitar a Maiduguri ranar Lahadi, Ndume ya gode wa gwamnan bisa alƙawarin tura Sojoji domin kare garin da kuma amincewa da gina asibiti, da rijiyoyi, da wasu muhimman ayyukan raya ƙasa a yankin. Ya ce irin waɗannan matakai za su taimaka wajen dawo da ƙwarin gwuiwar jama’a. Zulum Ya Rabawa Talakawan Dikwa  Tallafin...
    Sanarwar ta ƙara da cewa: “A cikin baƙin ciki muke alhinin rasuwar Ambasada Muhammad Jabbi Maradun, fitaccen dattijon jiha kuma ɗan jiharmu ta Zamfara na gaskiya.   “An haifi Jakada Jabbi ne a ranar 12 ga Nuwamba a shakrar 1943, a Ƙaramar Hukumar Maradun.   “Ambasada Maradun ya taba zama jakadan Nijeriya a ƙasar Tunisia daga 1999 zuwa 2003.   “Ya yi fice a yunƙurin samar da jihar Zamfara.   “Bayan kafuwar jihar Zamfara, Ambasada Jabbi ya shiga gwamnatin soja ta farko a ƙarƙashin Kanar Jibril Bala Yakubu, inda ya riƙe muƙamin kwamishinan Kasuwanci, Masana’antu da Yawon Buɗe Ido.   “Ayyukan sa na siyasa sun haɗa da jam’iyyun GNPP, NPN, da NRC, kuma ya kasance mai ruwa da tsaki a...
    Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya gana da Gwamna Siminalayi Fubara da wasu Dattawan Jihar Ribas. Mai taimaka wa Wike kan yaɗa labarai, Lere Olayinka ne, ya wallafa hoton ganawar a shafukan sada zumunta, inda ya ce kakakin Majalisar Dokokin jihar, Martin Amaewhule, ya halarci taron. An yi wata gagarumar zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa a Turai Ban taɓa cewa Buhari yana da alaƙa da Boko Haram ba — Jonathan Ko da yake Olayinka bai bayyana abin da aka tattauna a taron ba, amma wannan ce ganawa ta farko da aka yi tsakanin Wike da Fubara tun bayan da gwamnan ya kori wasu daga cikin muƙarrabansa yayin da yake shirin kafa sabuwar majalisar zartarwa a jihar. Rahotanni sun nuna cewa...
    Ya kara da cewa, “Ba a bar mu mun yi noma ba, kuma ana kwace mana kayanmu, Haƙurin mutane ya fara kaiwa bango.”   “Mutane suna rayuwa cikin tsoro, waɗannan miyagu suna barazanar hana mu girbin amfanin gonakinmu.   “Akwai wata ƙungiya da ake kira Lakurawa da kowa ke tsoro – karfinsu a yankin yana ƙaruwa.” Haruna ya ƙara da cewa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Iran ta yi kira ga kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC da ta dauki matakin haramtawa Isra’ila shiga harkokin wasanni na kasa da kasa. A cikin wata wasika da ya aike zuwa ga ministocin harkokin wasanni na kasashe 57 na kungiyar ta OIC, ministan wasanni da matasa na kasar Iran Ahmad Donyamali ya bukaci takwarorinsa da su hada karfi da karfe wajen ganin an kawar da Isra’ila daga wasannin kasa da kasa. Mista Donyamali ya yi kira da a kafa kungiyar wasanni ta kasashen musulmi domin neman kwamitin Olympics na kasa da kasa (IOC) ya dakatar da gwamnatin Isra’ila a gasar wasannin duniya. A cikin wasikar tasa, ya jaddada cewa gwamnatin Isra’ila ta keta yarjejeniya wassanin Olympics da duk...
    Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, ya musanta maganganun da ake yaɗawa cewar ya ce tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, yana da alaƙa da Boko Haram. Jonathan, ya yi wannan bayani ne kan cewar an fahimci bayaninsa a baibai, a taron ƙaddamar da littafin tsohon Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Lucky Irabor. ’Yan sanda sun kama wanda ake zargi da sace hakimi a 2023 a Kano Isra’ila ta kai hare-hare a Gaza duk da kiran Trump na tsagaita wuta A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ikechukwu Eze, ya fitar, Jonathan ya ce ba a fahimci ainihin kalamansa ba. “Ofishin Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan, ya lura da rahotannin karya da ke yawo a wasu kafafen labarai wai Jonathan...
    Sojojin HKI sun bada sanarwan cewa zasu fara shirin aiwatar da shirin shugaban Trump na tsagaita buduewa juna wuta a Gaza. Da kuma batun musayar fursinoni gaba daya da kungiyar Hamas. Shafin yanar gizo na labarai Arab News na kasar Saudia ya bayyana cewa a jiya da yamma ne kungiyar Hamas ta bayyana cewa ta amince da tsagaita wuta tsakaninta da HKI wanda shugaban kasar Amurka Donal Trump ya gabatar. Kungiyar ta bayyana cewa ta amince da wasu sassa na yarjeniyar amma sai an tattauna kan wasu. Wata majiyar sojojin yahudawan ta bayyana cewa shuwagabannin kasar sun basu umrnin dakatar da kai hare- hare kan falasdinawa a Gaza. Wannan sanarwan ta zo sa’o’ii kadan bayan da shugaban Amurka ya umurci...
    Burgediya JanarEsma’il Qa’ani babban kwamnadan dakarun “Qudus'” IRGC a nan Iran ya bayyana cewa kungiyar Hamas ta boye ranar fara yakin tufanul Aksa har shugaban kungiyar Shahid Isma’il Haniyya da shahida Nasarallah duk basu san da lokaci fara yakin ba, sai suka ji an fara. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Janar Qa’ani yana fadar haka, a jiya jumm’a a hirar da aka yi da shi a tashar talabijin ta cikin gida a nan Iran. Ya kumakara da cewa a lokacinda aka fara yakin shugaban kungiyar ta Hamas yana kan hanyarsa ta zuwa kasar Iraki, yana dawowa ne ya ji labarin fara shi. Janar Qa’ani ya kara da cewa, amma  duk da haka, shahida Nasarallah ya zauna...
    A ranar 3 ga watan ne hukumar ciniki ta duniya (WTO) ta gudanar da taron shekara-shekara na majalisar kula da harkokin cinikayya karo na uku a birnin Geneva na kasar Switzerland. Kasar Sin ta yi amfani da wannan dama domin daidaita wannan batu, inda ta fallasa tare da sukar matakin “harajin ramuwa” na Amurka daga bangare guda da gitta kariyar cinikayya, inda ta yi nuni da cewa, matakan kakaba harajin da Amurka ta dauka sun haifar da illa ga harkokin cinikayyar duniya, kana ta bukaci Amurka ta mutunta ka’idojin WTO, tare da yin aiki da dukkan bangarori don karfafa gudanar da harkokin kasuwancin duniya cikin kwanciyar hankali ba tare da tangarda ba. Membobi irinsu Indiya, Brazil, Masar da Pakistan sun...
    Shugaban cibiyar fasaha da kere-kere ta Pardis a nan Tehran ya bada sanarwan cewa, wakilai daga kasashe 65 ne suka bayyana anniyarsu ta halattan gasar fasahar kere-kere ta shekara ta 2025 a cibiyarsa. Kamfanin dilancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Mehdi Saffaari –Nio yana fadar haka a jiya Jumma’a ya kuma kara da cewa gasar ta dai-dai kun mutane, wadanda zasu gwada korewarsu da kuma fasahar da suke da ita a gasar wacce za’a gudanar daga ranar 27-30 ga watan Octoba damukeciki a nan Tehran. A taron yan jaridun da ya kira don bada wannan sanarwan Mehdi Safaari-nio ya ce mafi yawan mahallata gasar matasa ne musamman daliban makarantu wadanda suke son gwada korewarsu da kumailminsu.  Kuma a...
      Me Hakan Ke Nufi Ga Tawagar Nijeriya? Ga Yadda Tsayuwar Rukunin C Yake A ranar 9 ga watan Satumba ne tawagar Super Eagles ta Nijeriya ta tashi da kunnen doki a wasan da ta buga da tawagar ta Afirka ta Kudu a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya. Bayan wasan ne kasar Afirka ta Kudu ta kara zama a saman teburi da maki 17 cikin wasa takwas da ta buga a Rukunin C. Tawagar Jamhuriyar Benin ke biye mata da maki 14, sai kuma Nijeriya da ke mataki na 3 da maki 11. Sai dai kuma Nijeriya ta kasance tana da maki daya ne da na Rwanda da ke mataki na 4, sai kuma kasar Lesotho da...
    Ana ta rade-radin an baki sarauta, shin mene ne gaskiyar maganar? Alhamdulillah, maganar an bawa Zahra’u sarauta ba karya ba ne, hakkun haka ne an ba ni sarauta.   Mutane za su so su ji, shin daman Haj. Zahra’u ‘yar Ghana ce, tana da sarauta a Ghana? A’a! Ni ba ‘yar Ghana ba ce, ba abin da na hada da Ghana, sai dai so da yarda, saboda ma’abota kallon finafinan hausa ne. Ni kuma ina cikin wannan masana’anta ta finafinan hausa, musamman Dadin Kowa na Arewa24. Alhamdulillah Arewa24 ta sa sunanmu ya tafi a duniya. Ta yi mana riga ta yi mana wando babu abin da ba ta yi mana ba, domin dalilin fuskanmu da ta tafi ake kaunar mu...
    Dagacin garin Kirawa a Ƙaramar Hukumar Gwoza, a Jihar Borno, Abdulrahman Abubakar, ya bayyana dalilin da ya sa ya tsere daga Najeriya zuwa Kamaru bayan harin Boko Haram. A farkon makon nan, mayaƙan Boko Haram sun kai hari garin Kirawa, inda suka kashe mutum biyu sannan suka ƙone fadarsa. ’Yan bindiga sun sace uwa da ’ya’yanta a Kogi Isra’ila ta kai hare-hare a Gaza duk da kiran Trump na tsagaita wuta A hirar da aka yi da shi, Abubakar ya ce babu wani zaɓi da ya rage masa face ya tsere. “Babu abin da ya rage sai na tsere zuwa Kamaru. Mazauna garin sun hau manyan motoci sun tsallaka iyaka, wasu kuma sun gudu zuwa Maiduguri.” Boko Haram ta saki...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    “Rushewar wannan gada na haifar mana da matsala sosai. Gwamnati ta taimaka ta gyara,” in ji Wayu Bamga, mazaunin yankin. Nanlong Nyas ya ƙara da cewa, “Gyaran da aka yi bai daɗe ba kafin ruwa ya sake lalata gadar.” Wasu direbobi kamar Umar Sa’adu da Abubakar Haruna sun ce duk lokacin da suka isa wurin gadar, sai sun biya ma’aikata su tura motarsu kafin su iya tsallaka rafi kana su ci gaba da tafiya. Rushewar Gadar Namne Ta Taraba Ta Tsayar Da Zirga-Zirga A Jihar Taraba kuwa, Gadar Namne dake kan hanyar Jalingo–Wukari  ta rushe a watan Agustan 2024 bayan ruwan sama mai yawa, kuma har yanzu shekara guda bayan haka, babu wani gyara da gwamnatin tarayya ko ta jiha...
    ’Yan bindigar da ke addabar yankunan karkara sun kaƙaba sun ƙaƙaba musu haraji da ke kaiwa Naira miliyan 10 a Ƙaramar Hukumar Mashegu Jihar Neja. Rahotanni sun nuna cewa an umarci al’ummomin yankunan Babban Rami da Kaboji su su biya Naira miliyan biyu-biyu. Yankin Sabon Rijiya da Sabon Rami an umarce su da su Naira dubu 500, yayin da aka umarci ƙauyukan da ke kusa da Dajin Keji su tara Naira miliyan 10 gaba ɗaya. Haka nan, ana ƙaƙaba wa al’ummar Khizi an kaƙaba musu harajin Naira miliyan shida, da wa’adin ranar Juma’a, 3 ga Oktoba, 2025. Wata mata ta banka wa kanta wuta a Bauchi Sharri Jonathan ke wa Buhari don lashe zaɓen 2027 —Garba Shehu Wani mazaunin yankin...
    Tsohon mai magana da yawun marigayi Shugaba Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu, ya mayar da martani kan maganar tsohon Shugaba Goodluck Jonathan da ya ce ƙungiyar Boko Haram ta taɓa naɗa Buhari a matsayin wanda zai shiga tsakanin a tattaunawarsu da Gwamnatin tarayya. A yayin taron ƙaddamar da littafin “Scars: Nigeria’s Journey and the Boko Haram Conundrum” wanda tsohon Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Lucky Irabor (mai ritaya) ya rubuta, Jonathan ya bayyana cewa mayaƙan Boko Haram sun taɓa zaɓar Buhari a matsayin mai shiga tsakani domin tattaunawarsu da gwamnati. Jonathan ya ce a lokacin mulkinsa, gwamnatinsa ta kafa kwamitoci daban-daban don tattaunawa da mayaƙan Boko Haram domin samun zaman lafiya. Sai dai a martaninsa bayan labarin ya karaɗe kafofi...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya yi gargadin cewa amincewa da takunkuman da kasashen yamma suka kakaba wa Iran ba bisa ka’ida ba ya sabawa dokokin kasa da kasa, inda ya yi kira ga kasashen duniya da su bijirewa haramtattun takunkuman. Jakadan Iran a Colombo Alireza Delkhosh ya bayyana cewa, gargadin na ministan harkokin wajen kasar na kunshe ne a cikin wasikun da ya aike wa takwarorinsa na Sri Lanka da Maldives. Araghchi ya yi kira ga takwarorinsa na kasashen da su dau mataki mai tsanani kan takunkumin da Amurka da kasashen yammacin Turai suka kakaba iran, bayan da Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar a ranar 28 ga watan Satumba sake dawo da takunkuman da aka kakaba wa Iran,...
    Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, zai tashi daga Legas zuwa Jos, Babban Birnin Jihar Filato, a ranar Asabar domin halartar jana’izar mahaifiyar Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Farfesa Nantewe Yilwatda Goshwe. Zai halarci jana’izar Nana Lydia Yilwatda Goshwe, mahaifiyar Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa. Ana fargabar mutuwar mutane a gobarar tankar mai Boko Haram ta wuce yadda mutane ke tsammani — Jonathan Bayo Onanuga, Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Tsare-tsare, ya ce Shugaban Ƙasa zai kuma gana da shugabannin coci daga Arewacin Najeriya a Jos. Ana sa ran Tinubu zai koma Legas a ranar bayan kammala ziyarar. A gefe guda kuma, Ma’aikatar Yaɗa Labarai ta Jihar Filato ta sanar da taƙaita zirga-zirgar ababen hawa a...
    Anyanwu a cikin wasikarsa ya bayyana cewa an kammala dukkan shirye-shirye wasu tsare-tsare don gudanar da taron, kuma za a gudana da shi kamar yadda aka tsara. “Muna tabbatar wa hukumar zabe cewa za mu gudanar da taron kamar yadda aka tsara tun farko ba tare da dagawa ba. “Ya kamata hukumar zabe ta yi watsi da wasikar da shugaban jam’iyyar ya tura mata tun da farko na dage toron,” ya aika wa INEC wasikar ne a ranar 26 ga Satumba ba tare da sa hannunna ba. A cewar sakataren, bai kamata INEC ta yi aiki kan wata wasikar da ba sanya hannunsa hade da na Damagum ba. Wata majiyar ta bayyana cewa abin da ke faruwa yanzu ya nuna...
    Ana fargabar mutuwar wasu mutane masu ababen hawa da wasu da ke hanya  sakamakon faɗuwar wata tankar mai da ke ɗauke da mai a ranar Juma’a ta kuma tada gobara a hanyar Abeokuta zuwa Sagamu a Jihar Ogun. An samu rahoton cewa tankar ta faɗi ne ta gefenta sannan man da ke ciki ya  zube a kan titin Abeokuta zuwa Kobape-Siun-Sagamu a  daidai  wurin musayar hanyar. Boko Haram ta wuce yadda mutane ke tsammani — Jonathan NAFDAC ta lalata magungunan jabu na N15bn a Oyo Kakakin Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa na Jihar Ogun, Babatunde Akinbiyi a cikin sanarwar da ya fitar, ya ce lamarin ya janyo tashin gobara. Ya kuma ɗaura laifin haɗarin a kan gudun wuce ƙima...
    Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, ya ce Boko Haram sun fi sojojin Najeriya makamai, lamarin da ya sa yaƙin ya zama ɗaya daga cikin manyan matsalolin tsaron ƙasar nan. Ya bayyana haka ne a Abuja lokacin ƙaddamar da littafin Scars: Nigeria’s Journey and the Boko Haram Conundrum da tsohon Babban Hafsan Tsaro, Janar Lucky Irabor (mai ritaya), ya rubuta. 2027: Dalilin da ya sa Atiku bai ayyana takararsa ba — Hadimi Fashewar tukunyar gas ya haddasa gobara a jami’ar Gombe Jonathan, ya ce rikicin Boko Haram ya bambanta da sauran matsalolin da Najeriya ta fuskanta kamar na ’yan tawayen yankin Neja Delta da rikicin addini ko ƙabilanci. Ya bayyana cewa Boko Haram sun samu goyon baya daga ƙasashen waje, suna...
    Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, ya ce Boko Haram sun fi sojojin Najeriya makamai, lamarin da ya sa yaƙin ya zama ɗaya daga cikin manyan matsalolin tsaron ƙasar nan. Ya bayyana haka ne a Abuja lokacin ƙaddamar da littafin Scars: Nigeria’s Journey and the Boko Haram Conundrum da tsohon Babban Hafsan Tsaro, Janar Lucky Irabor (mai ritaya), ya rubuta. 2027: Dalilin da ya sa Atiku bai ayyana takararsa ba — Hadimi Fashewar tukunyar gas ya haddasa gobara a jami’ar Gombe Jonathan, ya ce rikicin Boko Haram ya bambanta da sauran matsalolin da Najeriya ta fuskanta kamar na ’yan tawayen yankin Neja Delta da rikicin addini ko ƙabilanci. Ya bayyana cewa Boko Haram sun samu goyon baya daga ƙasashen waje, suna...
    Bayanan sun bayyana cewa; “Jimillar makarantu 228 suka ci gajiyar shirin, inda kimanin dalibai 829,423 suka nema. Ya zuwa yanzu kuma, dalibai 510,378 ne suka samu wannan tallafi na bayar da rance. “Zuwa 10 ga watan Satumba, an biya kimanin Naira 53,801,717,293.00 a matsayin kudaden makaranta na daliban, yayin kuma da aka biya Naira 45,751,360,000.00 a matsayin alawus-alawus na daliban. Idan aka tattara kudaden baki-daya, jimillarsu ta kama Naira 99,553,077,293.00,” a cewar rahoton. Duk da nasarar da aka samu a fadin kasar, shirin ya fuskanci kalubale wajen ganin an yi adalci a rabon a dukkanin shiyoyin fadin kasar guda shida da ake da su. Alkaluman da LEADERSHIP ta tattara a watan Mayun 2025, sun nuna dimbin gibin da ke tsakanin...
    Sarah Mullally ta zama sabuwar Shugabar Cocin Ingila, wato Archbishop ta Canterbury, inda ta kasance mace ta farko da za ta jagoranci Cocin Ingila inda wannan muƙamin ya samo asali tun zamanin Daular Romawa da kuma al’ummar Anglican na duniya. Sarki Charles III ya amince da naɗin Mullaly bayan kwamitin da aka dora wa alhakin nemo wanda zai maye gurbin Justin Welby, wanda ya yi murabus a farkon wannan shekarar saboda wani zargi na cin zarafi, kamar yadda gwamnatin Birtaniya ta sanar a ranar Jumma’a. Cocin Ingila ita ce ta haifi ɗarikar Anglican a duniya. Mullally, mai shekaru 63, ta zama Archbishop ta Canterbury ta 106. A cikin wata sanarwa, tsohuwar ma’aikaciyar jinya ta bayyana cewa ta fahimci “babban nauyi”...
    Hukumar da ke Kula da Ingancin Abinci da Magunguna a Najeriya (NAFDAC) a ranar Alhamis ta lalata magunguna da kayayyakin jabu, da wa’adin aikinsu ya ƙare da marasa inganci, da jabun magunguna da darajarsu ta kai Naira biliyan 15 a garin Ibadan na Jihar Oyo. Darakta-Janar ta Hukumar NAFDAC Farfesa Mojisola Adeyeye ce ta sanar da hakan a lokacin da aka lalata magungunan a Ibadan, babban birnin jihar. 2027: Dalilin da ya sa Atiku bai ayyana takararsa ba — Hadimi An naɗa Remi Tinubu Sarauniyar Yaƙin Akko Adeyeye wanda Daraktan bincike da tabbatar da doka na NAFDAC, Martins Iluyomade ya wakilta, ya ce hukumar ta ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da cewa abinci, magunguna, kayan kwalliya, na’urorin likitanci, sinadarai...
    Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, har yanzu bai ayyana cewa ko zai tsaya takarar shugaban ƙasa a 2027 ba. Yayin da wasu ’yan siyasa kamar Peter Obi da Rotimi Amaechi suka nuna sha’awar tsayawa takara, Atiku ya ce “lokaci bai yi ba” domin yanke hukunci. Isra’ila ta kame dukkan jiragen ruwan da ke koƙarin kai kayan agaji Gaza An naɗa Remi Tinubu Sarauniyar Yaƙin Akko Kwanan nan, wasu rahotanni sun bayyana cewa Atiku ya faɗa wa BBC Hausa cewa zai bai wa matashi damar tsayawa takara. Wannan ya haifar da cece-kuce a kafafen sada zumunta. Amma hadiminsa, Paul Ibe, ya ce ba a yi wa maganganun Atiku kallo na tsanaki ba, an fahimce su ba daidai ba. Ibe, ya...
    Wata gobara da ta tashi a daren Alhamis ta lalata wani ɓangare na ɗakin kwanan dalibai mata a Jami’ar Jihar Gombe, tare da jikkata dalibai uku. Ana zargin gobarar ta tashi ne sakamakon fashewar gas ɗin girki a wani ɓangare na ɗakin kwanan da ke cikin harabar jami’ar. Da yake tabbatar da faruwar lamarin a wata hira ta wayar tarho da wakilinmu a ranar Juma’a, Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar Kashe Gobara ta Kasa, reshen jihar, Bashir Mu’azu, ya bayyana lamarin da cewa abin takaici ne. “Lamarin ya faru ne sakamakon fashewar gas ɗin girki. Binciken farko ya nuna cewa daliba ce ta bar girki ba tare da kulawa ba,” in ji Muazu. Sai dai ya bayyana cewa babu...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp