ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Me Aka Gano Kan Makomar Tattalin Arzikin Kasar Sin Daga Karuwar 5.2% Na Tattalin Arzikinta? October 21, 2025 Daga Birnin Sin Jirgin Kasa Mafi Saurin Gudu A Duniya Ya Fara Zirga-Zirgar Gwaji A Sin October 21, 2025 Daga Birnin Sin Jami’an Kasashen Afrika Na Koyon Dabarar Yaki Da Talauci Ta Sin A Jihar Ningxia October 21, 2025

.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

DSS ta kama likitan da ke duba ’yan bindiga a dazukan Kwara

Hukumar Tsaro ta DSS ta kama wani likita da ake zargin yana ba da magunguna tare da kula da ’yan bindiga masu garkuwa da mutane da ke wasu sassan jihar Kwara.

An kama wanda ake zargin, wanda ba a iya gano sunansa ba a lokacin rahoton, a yankin Jebba bayan rahotannin sirri sun nuna cewa wasu masu safarar kaya suna kai magunguna daga Sakkwato domin kula da ’yan fashin daji da suka samu raunuka a dazukan jihar.

Kakakin majalisar dokokin Ribas da takwarorinsa 16 sun fice daga PDP zuwa APC An kashe matashi yayin rikici a wajen raɗin suna a Bauchi

Majiyoyin tsaro sun ce da dama daga cikin waɗannan ƙungiyoyin masu laifi sun samu raunukan harbin bindiga a fafatawar da suka yi da jami’an tsaro a baya-bayan nan.

“Saboda haka muna ba da shawarar ƙara tsaurara matakan tsaro a cibiyoyin lafiya da ke cikin dazuka, domin masu garkuwa da mutane na iya kai hari a wuraren,” in ji wani jami’in tsaro.

Mai magana da yawun gwamnan jihar ta Kwara, Rafiu Ajakaye, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa kamun wata babbar nasara ce a ƙoƙarin da ake ci gaba da yi kan ’yan fashin daji.

“Wannan babban mataki ne daga DSS. Ya ƙara tabbatar da cewa hukumomin tsaro suna matsawa wa waɗannan ’yan ta’adda, suna kuma toshe hanyoyin tallafi da ke ba su damar gudanar da ayyukansu,” in ji shi.

Ajakaye ya ƙara da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da ƙarfafa haɗin gwiwa da hukumomin tsaro domin rufe dukkan hanyoyin da ke taimaka wa ayyukan garkuwa da mutane.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Shettima Ya Taya Sarkin Gumel Murna Tare da Jinjinawa Gwamna Namadi Bisa Bunkasa Bangaren Noma
  • Ina nan a PDP duk da sauya sheƙar ’yan majalisar Ribas — Wike
  • DSS ta kama likitan da ke duba ’yan bindiga a dazukan Kwara
  • Ziyarar Putin a Indiya alama ce da ke nuna cewa New Delhi na yin watsi da gargadin Trump?
  • An Ga Sojojin Ruwa Na Amurka A Kasar Puerto Rico A Shirinta Na Mamayar Venezuela
  • Shugaba Tinubu Ya Rantsar da Sabon Shugaban Hukumar Kidaya, Kwamishinoni da Manyan Sakatarori
  • CBN ya kara yawan kudin da mutum zai iya cirewa a mako zuwa N500,000
  • Gobara ta kashe mata da miji da ’ya’yansu 3 a Katsina
  • Gwamnatin Nasarawa Za Ta Gurfanar da Iyayen Yaran da Ba Sa Zuwa Makaranta
  • DAGA LARABA: Kalubalen Dake Gaban Janar Christopher Musa A Matsayin Ministan Tsaro