ShTinubu Ya Nemi Alkalai Su Kara Kaimi Wajen Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa
Published: 20th, October 2025 GMT
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bukaci Alkalan Najeriya su kasance masu gaskiya, rikon amana da tsoron Allah wajen yanke hukunci. Ya ce duk wata al’umma tana fara rushewa ne idan bangaren shari’a ya lalace.
Ya bayyana cewa gwamnati na kokarin inganta walwala da albashin Alkalan domin karfafa ikon cin gashin kansu.
Da yake bude taron bita na EFCC da NJI a Abuja, Shugaban wanda Mataimakinsa Kashim Shettima ya wakilta ya ce adalcin Alkalai ne ginshikin ci gaban kasa.
Ya nuna damuwa kan yadda ake jinkirta shari’o’in manyan laifukan rashawa, yana mai cewa an fi hanzarta shari’ar masu laifin yanar gizo.
Shugaba Tinubu ya jaddada cewa ba a taba kare kowa saboda siyasa a gwamnatinsa ba, inda ya bayyana cewa EFCC ta samu nasarar gurfanar da mutane sama da 7,000 tare da karbo kadarori fiye da Naira Biliyan 500 cikin shekaru biyu.
Ya bukaci Alkalan su ci gaba da koyon sabbin dabaru, musamman wajen shari’o’in yanar gizo da laifukan kuɗi, tare da tunatar da su cewa cin hanci yana shafar kowa.
A nata bayanin Babbar Alkalin Najeriya, Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun, ta bukaci Alkalan su tabbatar da yin adalci ba tare da jinkiri ko son zuciya ba.
Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya yaba da hadin kan da Alkalan je basu, yana mai cewa nasarorin da aka samu sun nuna jajircewa wajen yaki da cin hanci da rashawa.
Daga Bello Wakili
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Shari a
এছাড়াও পড়ুন:
Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Bayyana Cewa: Kuduri Mai Lamba 2231 Ya Zo Karshe
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Kuduri mai lamba 2231 ya ƙare aiki a yau
A cikin wata wasika da ya aike wa babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya da shugaban kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ministan harkokin wajen kasar Iran ya tabbatar da cewa a karshe kuduri mai lamba 2231 ya kare a yau, kuma duk wani kira na farfado da shi ko dawo da wa’adin kudirorin da ya kare, ba shi da wani tushe na shari’a, kuma ba zai iya haifar da wani tasiri na tilasta aiki da shi ba.
Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Sayyid Abbas Araqchi ya aike da wasika zuwa ga babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya da kuma shugaban kwamitin sulhu dangane da kawo karshen kuduri mai lamba 2231. Wasikar ta bayyana cewa: A ci gaba da wasikun da ya aike a baya, ciki har da na baya-bayan nan na ranar 27 ga watan Satumba 2025, daga karshe ya sanar da cewa, kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya kawo karshen kuduri mai lamba 2231, daidai da ƙayyadaddun tanadinsa.
A cikin wannan wasika na nanata matsayin Jamhuriyar Musulunci ta Iran kamar haka: Shekaru 10 da suka gabata, shirin hadin gwiwa na hadin gwiwa (JCPOA) ya fara aiki tare da amincewa da kuduri mai lamba 2231 (2015), yana mai nuni da imanin da kasashen duniya ke da shi cewa diflomasiyya da cudanya tsakanin bangarori daban-daban su ne mafi inganci hanyoyin warware rikice-rikice.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kasashen Iran, Rasha, Da China Sun Jaddada Rashin Halaccin Dawo Da Tsohon Takunkumi Kan Iran October 18, 2025 Masani Kan Harkokin Tsaro Ya Ce: Makami Mai Linzamin Iran Kirar Ghadir Ya Aike Da Sako Ga Isra’ila October 18, 2025 Jami’in Majalisar Dinkin Duniya Ya Ce: An Rusa Gaza Gaba Daya October 18, 2025 Joseph Kabila Ya Koma Kasarsa Domin Kalubalantar Hukuncin Kisa Da Aka Yanke Kansa October 18, 2025 Gaza Ta Bukaci A Binciki Isra’ila Kan Sace Sassan Jiki A Gawarwakin Falasdinawa October 18, 2025 Hamas Ta Bukaci A Kafa Kotun Kasa Da Kasa Kan Gawarwarkin Da Isra’ila Ta Dawo Mata Da Su. October 18, 2025 Madagascar : An rantsar Da Michael Randrianirina A Matsayin Shugaban Kasar October 18, 2025 Iran Ta yi Tir Da Harin da Isra’ila Ta kai Kudancin Kasar labanon. October 18, 2025 Majalisar Dattawa Za Ta Gana Da Ministan Ilimi Kan Batun Yajin Aikin Asuu. October 18, 2025 Gaza ta bukaci a binciki Isra’ila kan sace sassan jiki a gawarwakin falasdinawa October 18, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci