ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta Tsakanin Pakistan Da Afghanistan October 20, 2025 Daga Birnin Sin Gina Kasar Sin Ta Dijital Na Kara Gaba Zuwa Sabon Matakin Amfani Da Basira October 20, 2025 Daga Birnin Sin An Gudanar Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Tsakiyar JKS Na 20 A Beijing October 20, 2025

.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Wasu jiga-jigan ADC za su dawo jam’iyyarmu — Shugaban Jam’iyyar APC

Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bayyana cewa wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar ADC, za su koma APC a mako mai zuwa.

A makonnin da suka gabata, ’yan siyasa da dama daga jam’iyyun adawa suna sauya sheƙa zuwa APC, yayin da ake shirin tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.

HOTUNA: Al’ummar Jihar Neja sun yi addu’o’in neman zaman lafiya Ta’addanci: An fi kashe Musulmi a kan Kiristoci a Najeriya — Jakadan Amurka

Idan ba a manta ba, Gwamnan Jihar Enugu, Peter Mbah, ya koma APC, sannan Gwamnan Jihar Bayelsa, Douye Diri, shi ma ana sa ran zai sanar da sauya sheƙarsa a hukumance nan ba da jimawa ba.

Yilwatda, yayin ganawarsa da mambobin APC a Jos, Jihar Filato, ya ce: “A mako mai zuwa zan karɓi wasu fitattun mutane daga ADC. Wasu daga cikinsu sun bar PDP sun koma ADC, amma yanzu za su dawo APC.”

Ya ƙara da cewa, yawancin waɗanda za su koma jam’iyyar “sun riga sun kammala gwajin lafiyarsu” kuma za a tarbe su a hukumance a mako mai zuwa.

“A cikin makonni biyu masu zuwa, za mu kuma bayyana wani babban ɗan siyasa da ya kammala gwajin lafiyarsa. Za mu karɓe shi a hukumance nan gaba kaɗan,” in ji shi.

Shugaban jam’iyyar ya bayyana APC a matsayin “amaryar siyasa ta yanzu”, inda ya ce ’yan siyasa da yawa na rubibin shiga jam’iyyar.

Ya ce akwai sanatoci, gwamnoni, da ’yan majalisa da dama da ke shirin komawa APC.

“APC jam’iyya ce mai maraba da kowa,” in ji shi.

“Ba sai ka kasance daga cikin waɗanda suka kafa jam’iyyar ba kafin ka samu ci gaba a cikinta. Ni shaida ne a kan hakan. Da zarar ka shiga, kana da cikakken haƙƙi da damar da kowa yake da ita. Wannan shi ne tsarin jam’iyyarmu.”

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Matsayar Kasar Sin A Bayyane Take Dangane Da Batutuwan Cinikayya Da Tsagin Amurka
  • Gina Kasar Sin Ta Dijital Na Kara Gaba Zuwa Sabon Matakin Amfani Da Basira
  • Kano Pillars Ta Dakatar Da Babban Kocinta Bisa Rashin Katabus A Kakar Wasa Ta NPFL
  • An kama ɗan uwan Nnamdi Kanu da lauyansa —Sowore
  • Masanin Ilimin Physics Chen Ning Yang Ya Rasu Yana Da Shekaru 103
  • Kasar Sin Ta Gargadi Amurka Game Da Yunkurin Samarwa Yankin Taiwan Makamai
  • Mataimakin Firaministan Sin Ya Zanta Da Sakataren Baitul-mali Da Wakilin Cinikayyar Amurka
  • Wasu jiga-jigan ADC za su dawo jam’iyyarmu — Shugaban APC
  • Wasu jiga-jigan ADC za su dawo jam’iyyarmu — Shugaban Jam’iyyar APC