Jagoran Ya Mayar Da Martani Ga Trump Cewa; Su Ci Gaba Da Mafarkinsu
Published: 20th, October 2025 GMT
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya mayar da martani ga shugaban Amurka Trump cewa: su ci gaba da mafarkinsu!
Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei a yayin da yake tsokaci kan kalaman shugaban Amurka a yayin ziyarar da ya kai yankunan da aka mamaye, ya ce Trump cikin alfahari ya ce kasarsa ta yi luguden bama-bamai tare da lalata cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran, yana mai mayar msa da martani cewa: “To, su ci gaba da yin mafarkinsu!”
A yayin ganawarsa da safiyar yau da zakaran wasanni kuma wadanda suka lashe gasar Olympics ta kasa da kasa, Jagoran ya kara da cewa: Duk abin da kuke yi ana danganta shi da Iran da kuma al’ummar kasar ne, kuma wannan tuta da zakarun Iran suka daga yana da matukar kima, kamar yadda sujjadar godiya da addu’o’in da dan wasan kasar Iran ya yi bayan samun nasara wata kyakkyawar alama ce ta al’ummar Iran.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi ishara da muhimmancin tallafawa matasa masu hazaka yana mai cewa: Wadannan matasa da suke halartar gasar Olympics ta kimiyya, taurari ne masu haskawa a yau, amma nan da shekaru goma za su haskaka rana idan suka ci gaba da aiki da kokari, y ace: Yana kuma kira ga jami’ai da kada su yi watsi da wadannan matasa, kuma kada su gamsu da abin da suka samu ya zuwa yanzu, sai dai suna shimfidar hanyar ci gaba mai bunkasa ce.
Ya kara da cewa, “Idan tauraro ya ci gaba da tafiya, nan da shekaru goma zai zama rana mai haskaka wa wasu hanya, kuma ta hanyarsu za a iya cimma manyan ayyuka.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Jaddada Aniyarta Ta Yin Riko Da Hakkokin Kasarta October 20, 2025 Sakataren Majalisar Kolin Tsaron Kasar Iran Ya Karbi Bakwancin Takwaransa Na Iraki October 20, 2025 Wakilin Amurka Na Musamman A Siriya Ya Matsa Don Ganin Kasashen Saudiyya Da Lebanon Da Kuma Siriya Sun Kulla Alaka Da Isra’ila October 20, 2025 Kungiyar Kare Hakkin Bil-Adama Ta Amnesty Ta Zargi Gwamnatin Tanzaniya Da Musgunawa ‘Yan Adawa October 20, 2025 Dakarun kare Juyin Musulunci Na Iran Sun Bayyan Shirinsu Na Karfafa Dabarun Hadin Guiwa Da yamen October 20, 2025 October 20, 2025 Kotu A Faransa Ta Yanke Hukumci Zama Gidan Yari Ga Tsohon Shugaban Kasar Nicola Sarkozi October 20, 2025 Isra’ila Ta Keta Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta Sau 80 Ta Kashe Mutane 97 Ta Jikkata 230 October 20, 2025 Arewa Ta Samu Kashi 56% Na Mukaman Gwamnatin Tinubu inji Shugaban FCC October 20, 2025 Grossi: Za a iya warware batun Shirin nukiliyar Iran ne kawai ta hanyar diflomasiyya October 20, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Arakci: Iran Da Kasashen China Da Rasha Suna Shirin Kawo Karshen Takunkuman Turai
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci ya bayyana cewa, mafi yawancin kasashen duniya sun yi Imani da ka’idoji na cin gashin kai da ‘yanci.
Abbas Arakci wanda ya gabatar da jawabi a wurin zaman majalisar zartarwa a yau Lahadi ya ce ya bayyana cewa a fagen diplomasiyya Iran ta dauki makamin dakile kokarin kasashen turai na sake dawu da takunkumi a kanta, ta hanyar aiki tare da kasashen Rasha da kuma China.
Haka nan kuma ya yi jinjina ga matakin bayan nan da kungiyar ‘yan-ba-ruwanmu ta dauka na nuna cikakken goyon bayanta ga Iran, yana mai cewa; Ana samun kafuwar sabon kawance a duniya, yayin da kasashen turai da wasu tsiraru suke a gefe daya, ita kuwa Iran da mafi yawancin kasashen duniya da su ka kunshi Rasha da China suke tare bisa aiki da ka’idojin ‘yanci da cin gashin kai.
Tun da fari Iran da hadin gwiwar Rasha da China sun aike wa da MDD wasika akan rashin halarcin matakin kasashen Farnsa, Birtaniya da Jamus na kakaba wa Iran takunkumi.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Miliyoyin Mutanen Amurka Sun Yi Zanga-zanagr Nuna Kin Jinin Donald Trump October 19, 2025 Sheikh Na’im Kassim Ya Mika Sakon Ta’aziyyar Shahadar Gumari Na Kasar Yemen Ga Sayyid Husi October 19, 2025 Sojojin HKI Sun Shiga Cikin Yankin Qunaidhara Na Kasar Syria October 19, 2025 Gaza: HKI Tana Ci Gaba Da Keta Yarjejeniyar Tsagaita Wuta October 19, 2025 Hamas ta yi Allah wadai da Isra’ila kan keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta October 19, 2025 An gudanar da zanga-zanga a sassa da dama na Amurka October 19, 2025 MDD : “Zai dauki lokaci” kafin a rage yunwa a Gaza October 19, 2025 ICC ta ki amincewa da daukaka karar Isra’ila October 19, 2025 Kissoshin rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 159 October 19, 2025 Kissoshin rayuwa: Sirar Imam Hassan(a) 158 October 19, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci