2025-10-13@13:35:11 GMT
إجمالي نتائج البحث: 36

«shawarwarin da»:

    Na farko, hada kai don samar da yanayi mai kyau ga ci gaban mata. Na biyu, a karfafa abubuwan da za su habaka ingancin ayyukan mata cikin hadin kai. Kana na uku, a gina tsarin kare hakkin mata tare. Sai na hudu, a bude sabon babin hadin gwiwa tsakanin mata a duniya.   Za a gudanar da taron kolin mata na duniya a yau da gobe Talata a birnin Beijing. Kuma tuni shugaban kasar Sin Xi Jinping da uwargidansa Peng Liyuan, suka yi musafaha da shugabannin tawagogin kasashe, da kungiyoyin duniya da suka halarci taron, tare da daukar hotuna tare da su. (Amina Xu) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Ƴan Bindiga Sun Amince Da Dakatar Da Hare-Hare A...
    “Muna kira ga majalisar kasa da ta yi la’akari da shirin gyaran tsarin kudurorin zabe cikin gaggawa. Amincewa da dokar cikin lokaci yana da muhimmanci ga shirinmu na gudanar da zabe a 2027.   “Rashin tabbas game da tsarin doka na zabe na iya kawo matsaloli masu yawa ga ayyukan hukumar INEC yayin da lokacin zabe ke karatowa,” in ji shi.   Shugaban INEC ya bayyana cewa hukumarsa ta aiwatar da shawarwarin da aka mika mata kai tsaye a rahoton EU na zaben 2023.   “An dauki mataki kan wasu bangarori na shawarwarin da ake bukatar hukumar ta aiwatar da su. Haka kuma, ana daukar mataki kan shawarwarin da suka shafi fannoni da dama wadanda ake bukatar hadin gwiwa tsakanin...
    Na farko, manufofi da ka’idojin kundin mulkin MDD su kasance tushen ka’idojin dangantakar kasa da kasa, kuma jigon tsarin shari’a na duniya. Na biyu, dole ne dokokin duniya su mutunta bambancin al’adu da tsare-tsaren shari’a na kasashen duniya, tare da tabbatar da cewa dukkannin kasashe na da matsayi iri daya, kuma ya zama dole a karfafawa kasashe masu tasowa gwiwar yin magana. Na uku, daidaiton ‘yancin kai ya kasance tushen shari’a ta zamani a duniya. Na hudu, nuna biyayya ga yarjejeniyoyin kasa da kasa, wata babbar ka’ida ce wajen aiwatar da shari’a a duniya, kuma dole ne dukkannin kasashe su cika alkawuransu bisa aminci da gaskiya. Na biyar, dole ne kasashe su gaggauta tsara dokoki a sabbin fannonin da sabbin...
     Geng Shuang ya jaddada cewa, kasar Sin kasa ce da ta’addanci ya yi wa illa. Ya ce kungiyar ETIM wadda kwamitin sulhu na MDD ya ayyana a matsayin ta ta’addanci, ta taba tada rikice-rikicen ta’addanci da dama a cikin kasar Sin, kana ta gudanar da ayyukanta a kasar Syria, da Afghanistan da sauransu. Ya jaddada cewa, kasar Sin na kira ga bangarori daban daban da su dauki matakai don yaki da kungiyoyin ta’addanci ciki har da kungiyar ETIM. (Zainab Zhang)ShareTweetSendShareMASU ALAKA Daga Birnin SinSauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi? October 7, 2025Daga Birnin SinDaukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira ga daukacin jama’ar kasar Sin da su yi aiki tukuru, tare da ingiza wanzar da zamanantarwa irin ta Sin. Xi, wanda kuma shi ne sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban hukumar zartarwar rundunar sojojin Sin, ya yi kiran ne yayin taron bikin cika shekaru 76 da kafuwar janhuriyar jama’ar kasar Sin, wanda ya gudana yau Talata a babban dakin taruwar jama’a dake birnin Beijing. Shugaba Xi, ya jaddada cewa a gabar da yanayin harkokin duniya ke saurin sauyawa cikin sama da karni guda, dole ne a yi aiki tukuru wajen yayata akidun bai daya na dukkanin bil’adama, da aiwatar da tsarin cudanyar mabanbantan sassa, da ingiza aiwatar da shawarwarin bunkasa ci gaban...
     Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya jaddada cewa; Ba dole ba ne Iran ta bi hukunce-hukuncen da ba bisa ka’ida ba Shugaban Majalisar Dokokin kasar Iran Mohammad Baqir Qalibaf ya tabbatar a cikin jawabinsa yayin zaman majalisar a yau Lahadi cewa: Iran ba ta daukar kanta a matsayin wajibcin aiwatar da kudurorin kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya da aka bayyana a matsayin haramtacciyar hanya sakamakon daukar matakin sake dawo da takunkuman da kasashen Turai uku suka yi kan Iran. Qalibaf ya yi bayanin cewa: Share fagen hanyar da za a bi wajen sake kakaba takunkuman da kasashen Turai uku suka yi da kuma mayar da takunkuman da Majalisar Dinkin Duniya ta kakabawa Iran, ba bisa ka’ida ba ne, yana...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira ga makarantun horar da ‘yan jam’iyya da su taka rawar gani wajen kyankyashe hazikai, tare da gabatar da shawarwari ga JKS.   Xi, wanda shi ne sakataren kwamitin kolin JKS, kuma shugaban hukumar zartarwar rundunar sojojin kasar Sin, ya yi kiran ne cikin wani umarni da ya gabatar ga makarantun koyar da jagoranci na ‘ya’yan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin. (Mai fassara: Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Har kullum Sin tana nacewa shawarwari, da tuntubar juna a matsayin muhimman matakan kyautata hadin gwiwa dake share fagen inganta cudanya. Tare da hakan, Sin na fatan Amurka za ta kaucewa kokarin dakile ci gabanta. Kuma duk wasu matakai na matsin lamba daga bangare guda kan kasar Sin, ba za su taba yin nasara ba, kamar dai yadda muka gani a baya. Don haka, a wannan gaba da ake ta samun karin sakamakon kyautata muamala da gudanar da shawarwari, kamata ya yi bangaren Amurka ya kauracewa kakaba shingen cinikayya, wanda ka iya gurgunta nasarorin da aka riga aka cimma. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na...
    Shawarwari biyu na Turai da na Rasha suna gaban Iran, kuma za ta amince da duk wata mafita ta gaskiya da ke kiyaye muradunta Sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani, ya bayyana ikirarin cewa; Iran ba ta amincewa da tattaunawa, a matsayin “karya” ne, yana mai tunatar da cewa, Iran na cikin wani yanayi na tattaunawa ta fuskanci farmakin soji na wuce gona da iri. Larijani ya ce: Iran za ta amince da duk wata shawara mai ma’ana da adalci da za ta kiyaye muradunta, yana mai bayyana cewa, “Iran tana nazarin shawarwarin Turai da na Rasha da suka gabatar mata.” Larijani ya tabbatar da cewa: Iran ta amince da duk shawarwarin biyu a kan wasu sharudda,...
    Daga ranar 14 zuwa 15 ga wata, an gudanar da sabon zagayen shawarwari kan harkokin tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da Amurka a birnin Madrid, babban birnin kasar Spaniya, inda bangarorin biyu suka yi musayar ra’ayoyi a kan harkokin cinikayya da ke janyo hankalinsu, tare da cimma daidaito ta fannin daidaita batutuwan da suka shafi Tiktok, da rage shingayen zuba jari, da sa kaimin hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya a tsakaninsu. Taron shawarwarin ya kasance zagaye na hudu da sassan biyu suka gudanar cikin watanni biyar da suka wuce. Kwatankwacin shawarwarin da aka gudanar a baya, a karo na farko, an sanya Tiktok cikin batutuwan da aka tattauna a shawarwarin na wannan zagaye. Yadda Sin da Amurka...
    Babban sakataren MDD António Guterres, ya bayyana a jiya Talata cewa, jerin shawarwarin da Sin ta gabatar wato shawarar raya duniya, shawarar tabbatar da tsaron duniya, shawarar raya wayewar kan al’ummun duniya, da kuma jagorantar harkokin duniya, sun dace da ka’idar kundin tsarin MDD. Guterres ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayoyin ‘yan jarida a wani taron manema labarai da aka yi a ranar. Ya ce shawarwarin da Sin ta gabatar sun mutunta manufar kasancewar bangarori da dama, kuma sun goyi bayan MDD a matsayin cibiyar hadin gwiwar kasa da kasa, tare da dukufa kan inganta hadin gwiwa tsakanin kasashe daban daban da warware rikice-rikice cikin lumana. Guterres ya kara da cewa, yanzu ana fuskantar rarrabuwar kawuna a...
    A bayan bayan nan, an aiwatar da jerin tattaunawa tsakanin Sin da Amurka karkashin jagorancin shugabanninsu, inda aka samu kyawawan sakamakon da ya kyautata alakarsu ta tattalin arziki da cinikayya. Wannan ya nuna shawarar da a kullum Sin ke bayarwa cewa, tattaunawa ita ce mafita ga dukkan rikice-rikice, maimakon amfani da karfi. Kasar Sin ta sha nanata cewa, babu mai samun nasara a yakin cinikayya ko haraji. Mun ga yadda aka samu hauhawar farashin kayayyaki da karuwar rashin aikin yi da faduwar darajar hannayen jari a Amurka, a lokacin da ta kaddamar da yakin haraji, wanda ya nuna cewa, maimakon cimma abun da take fata na samun fifiko, asara aka samu da lalacewar muradun kamfanoni da ’yan kasuwar kasar. Kowace...
    Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Jami’an kasar suna kiyaye shawarwarin Jagoran juyin juya halin Musulunci Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Jami’an zartaswa na kasar suna kiyaye shawarwari da umarnin Jagoran juyin juya halin Musulunci a Iran. Shugaba Pezeshkian ya rubuta a shafinsa na yanar gizo a shafin sada zumunta na X cewa: Jami’an zartaswa na kasar suna kiyaye shawarwari da umarnin Jagoran juyin juya halin Musulunci yayin ganawarsa a jiya (Lahadi) da wakilan gwamnati. Ya kara da cewa: Da yardar Allah za a shawo kan matsaloli tare da hadin kan kasa da gwiwar al’umma da taimakon al’umma da kuma saukakawa Jagoran juyin juya halin Musulunci. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new...
    Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta musanta zargin yin katsalandan a tattaunawar tsagaita bude wuta a Gaza Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Ismail Baqa’i, ya musanta zargin katsalandan din Iran a tattaunawar tsagaita bude wuta a Gaza. A yayin da yake amsa tambaya game da ikirarin da shugaban kasar Amurka ya yi na cewa Iran na tsoma baki a shawarwarin tsagaita bude wuta a zirin Gaza, ya ce: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tare da dukkan kasashen duniya tana yin kakkausar suka kan kisan gillar da ake yi a Gaza tare da goyon bayan duk wani tsari da zai kai ga dakatar da aikata laifuka da kuma rage radadin wahalhalun da al’ummar Gaza suke ciki. Baqa’i ya jaddada cewa; Masu yin shawarwarin...
    Tsoffin gwamnoni da suka fara mulki a shekarar 1999, da ake kira “Class of ’99,” sun gana da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a Fadar Gwamnati da ke Abuja a ranar Juma’a, inda suka gabatar da shawarwari na aiki domin magance matsalolin tsaro, inganta tattalin arziki da kuma samar da ayyukan yi a fadin ƙasar. Tawagar, ƙarƙashin jagorancin tsohon Gwamnan Jihar Edo, Lucky Igbinedion, ta haɗa da Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), George Akume, da wasu tsoffin gwamnoni da suka yi mulki tare da Shugaba Tinubu lokacin da yake Gwamnan Jihar Lagos. Da yake jawabi ga manema labarai bayan ganawar da ta ɗauki fiye da awa guda, Igbinedion ya bayyana cewa ziyarar tasu na da nufin yin wata ganawa da ɗan...
    2. Gyaran zaɓe da shari’o’in zaɓe 3. Ƙirƙirar sabbin jihohi 4. Samar da Ƴansandan jihohi 5. Haɗa kai don gudanar da mulki Daga cikin muhimman shawarwari, akwai na kafa hukumar zaɓen ƙananan hukumomi (NALGEC), ƙara kujeru ga mata a majalisu, da ba wa ‘yan Nijeriya dake ƙasashen waje damar yin zaɓe. Hakanan, akwai shawarwarin sauya wasu abubuwa daga jerin abubuwan da majalisar tarayya ke da ikon yi zuwa na majalisun jihohi, da kuma ƙirƙirar Majalisar Sarakuna ta ƙasa. Kwamitin ya yi kira ga duk ‘yan ƙasa da su halarci tarurrukan sauraron ra’ayin jama’a da za a gudanar a: – Lagos (Kudu maso Yamma) – Enugu (Kudu maso Gabas) – Ikot Ekpene (Kudu maso Kudu) – Jos (Arewa Tsakiya) – Maiduguri...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Sabbin masu sana’oi na tafka kurarai da suka hada da rashin kyakkyawar tsari, karancin jari, rashin shawarwarin kwararru da wasu kalubalen na daban.   Sai dai masana suna ganin idan sabbin masu sana’oi za su yi amfani da shawarwarin da suke badawa zai taimaka wajen dorewar sabbin sana’oin su. NAJERIYA A YAU: Rashin Aikin Yi Da Hanyoyin Magance Su A Najeriya DAGA LARABA: Dalilan Rashin Jituwa Tsakanin Marasa Lafiya Da Jami’an Kiwon Lafiya Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan irin wadannan kura-kurai da kuma shawarwarin da masana suka bada don dorewar sabbin sana’oi. Domin sauke shirin, latsa nan
    Iran ta ce za a gudanar da zagaye na gaba na tattaunawa da Amurka a ranar Lahadi mai zuwa a Muscat, babban birnin kasar Oman. Kakakin ma’aikatar Esmail Baghai a wata sanarwa da ya fitar ya ce “An shirya zagaye na gaba na tattaunawa tsakanin Iran da Amurka a ranar Lahadi mai zuwa a birnin Muscat.” Tun a watan Afrilu, Tehran da Washington ke gudanar da shawarwarin kan shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya. An yi shawarwari guda uku a tsakanin kasashen biyu a birnin Muscat, yayin da sauran biyun suka gudana a Rome, babban birnin kasar Italiya. Tehran da Washington sun gudanar da wadannan zagaye biyar na shawarwarin a shiga tsakanin kasar Oman, kan batun maye gurbin yarjejeniyar nukiliyar...
    Ministan harkokin wajen Iran Seyed Abbas Araghchi ya tabbatar da cewa Iran ba za ta amince da duk wata tattaunawa kan dakatar da shirinta na inganta makamashin Uranium gaba daya ba. Ya bayyana hakan ne a gefen ziyarar da shugaban kasar ya kai kasar Oman, inda ya jaddada cewa, bai kamata tattaunawa da Amurka za ta hada da batun ba wanda Tehran ba za a amince da shi ba. Araghchi ya ce, ana ci gaba da tattaunawa da Amurka, amma batun tace uranium shi ne ya kasance babban abin da ake samun sabani. Ya kuma kara da cewa, an yi shawarwari da ministan harkokin wajen Oman game da shirya wani sabon zagaye na shawarwari tsakanin Iran da Amurka. Ministan ya...
    Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta bayyana sabbin ci gaban da aka samu a tattaunawar da aka yi a birnin Roma Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya jaddada cewa: Ana gudanar da zagaye na biyar na tattaunawa ba na kai tsaye ba tsakanin tawagar Amurka da na Iran a cikin yanayi na kwarewa. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya bayyana a yau Juma’a cewa: Tattaunawar tana gudana cikin kwarewa da kwanciyar hankali, yana mai cewa abin da ake yadawa a kafafen yada labarai hasashe ne da baya da tushe ko inganci kuma baya da bambanci da shaci fadi. A yau Juma’a da yamma ne aka fara shawarwarin da ba na kai tsaye ba karo na biyar...
    Iran ta sanar da lokaci da kuma wurin da za a yi sabon shawarwari tsakanin Iran da Amurka Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya sanar da cewa: A gobe Juma’a ne za a gudanar da zagaye na biyar na shawarwari tsakanin Iran da Amurka a birnin Roma. A lokacin da ya isa birnin Shiraz don halartar taron yankin kan harkokin diflomasiyya na cikin gida, Araghchi ya bayyana cewa, gudanar da wannan taro da ya fi mayar da hankali kan diflomasiyyar tattalin arzikin yankin, ya shiga cikin tsarin manufofin makwabtaka na Iran, yana mai jaddada cewa, ko shakka babu za ta yi tasiri. Araqchi ya kara da cewa “Za a gudanar da tattaunawar zagaye na biyar ranar Juma’a a Roma...
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Sun yi imani da tattaunawa da zaman lafiya ba tare da mika wuya ga barazana ba A yayin ganawarsa da masu fafutukar siyasa da zamantakewa a lardin Kermanshah da ke yammacin kasar Iran a jiya Alhamis, shugaban na Iran Masoud Perzeshkiyon ya ce za a gudanar da shawarwari kan shirin makamashin nukiliyar Iran cikin karfin gwiwa da mutunta juna, yana mai jaddada wajabcin rashin mika wuya ko mika kai ga duk wata barazana. Shugaba Pezeshkiyon ya jaddada cewa yin shawarwari ɗaya ne daga cikin ka’idodin hankali da zurfin tunani, amma ba a kan kowane farashi ba. Dole ne a gudanar da shawarwari cikin aminci da mutuntawa tare da bin ka’idojin kasa da kare kima....
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Iran ta bayyana cewa tattauanwa ta hudu data wakana tsakaninta da Amurka tana da wahala amma kuma tana da amfani. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmaeil Baghaei ya ce zagaye na hudu na tattaunawar da Amurka abu ne mai wahala amma mai amfani ce. M. Baghaei ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a karshen zagaye na hudu na shawarwarin Tehran da Washington a babban birnin Muscat na kasar Omani yau Lahadi. Ya kara da cewa Oman ne za ta sanar da lokaci da wurin da za a gudanar da shawarwarin na gaba. A nata bangare Amurka ta bakin wani babban jami’inta da ya bukaci a sakaya sunansa ya bayyana cewa, sakamakon zagaye...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa; Ana nazarin lokacin gudanar da zagaye na huɗu na shawarwari tsakanin Iran da Amurka Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya sanar da cewa: Ana nazari kan lokacin gudanar da zagaye na gaba na tattaunawar Iran da Amurka wand aba na kai tsaye ba, kuma mai shiga tsakani na Oman zai sanar da karin bayani da zarar an tantance lokaci da wurin da za a yi. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya shaidawa kamfanin dillancin labaran kasar Iran cewa: Ana duban lokacin da za’a gudanar da zagaye na gaba na tattaunawa tsakanin Iran da Amurka. Baqa’i ya kara da cewa: Mai shiga tsakani na Oman zai sanar da bayanai...
    Ya kara da cewa, “Za mu gwabza yaki, idan yakin ya zama dole, amma kofofinmu a bude suke idan Amurka tana son a tattauna,” kana ya ce, Sin na neman hawa teburin tattaunawa da yin shawarwari ne kawai bisa daidaito, da mutuntawa da kuma samun moriyar juna. (Abdulrazaq Yahuza Jere). Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Mai ba da shawara ga Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Masu sasantawa Iran a birnin Roma suna da cikakken ikon gabatar da shawara kan matsayin kasarsu Ali Shamkhani mai ba da shawara ga Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi nuni da cewa: Masu gudanar da shawarwari na Iran sun tafi birnin Roma ne domin yin shawarwari karo na biyu da Amurka kan batun makamashin nukiliyar kasar Iran. Ya ce masu yin shawarwari na Iran suna da cikakken ikon gabatar da shawara kan matsayin kasarsu. Shamkhani ya yi nuni da cewa: Masu shiga tsakani na Iran suna neman cimma cikakkiyar yarjejeniya bisa ka’idoji guda tara: tsanani, samar da lamuni, dage takunkumi, yin watsi da tsarin Libya/UAE, kaucewa...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya soki abunda ya danganta da barazanar Amurka ga Teheran, yana mai cewa kasarsa a shirye take ta shiga tattaunawa ta hakika ba tare da barazana ba. “Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana neman tattaunawa ta gaskia, a yayin da suke barazana ga Iran a daya bangaren kuma suna neman yin shawarwari,” in ji Pezeshkian a ranar Asabar. “Idan kuna neman shawarwari, to me yasa kuke yin barazana? A yau, Amurka ba wai kawai ta wulakanta Iran ba har ma da duniya, kuma wannan hali ya saba wa bukatar tattaunawa,” in ji shi. Kalaman na Pezeshkian sun zo ne bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya yi kira ga Tehran da ta shioga shawarwari kai tsaye...
    Saboda haka ne, hukumar ta shawarci manoman da ke da ra’ayin noma a kakar noman ta bana da su tabbatar sun tuntube ta, ko kuma tuntubar sauran hukumomin da ke hasashen yanayi, domin sanin lokacin da ya ya fi dacewa su yi shuka. Hukumar ta yi hasashen cewa, jihohin Zamfara, Katsina, Kano, Kaduna, Jigawa, Filato, Bauchi, Borno, Yobe, Adamawa, Taraba, Neja, Kwara, Kogi, Abuja, Ekiti da kuma Ondo, za su fuskanci daukewar ruwan sama da wuri, inda aka kwatanta da na dogon zango da aka samu a daminar bara. Haka zalika, hukumar ta yi hasashen cewa; za a samu jinkirin ruwan sama a wasu sasssan jihohin Kaduna, Nasarawa, Benuwe, Legas, Kwara, Taraba, Oyo, Ogun, Kuros Riba, Delta, Akwa Ibom, Ebonyi,...
    Na hudu, kudurin Sin shi ne inganta hadin gwiwa ta hanyar tattaunawa, tare da adawa da neman kwamitin sulhu na MDD ya shiga tsakani. Bugu da kari, ministan ya ce Sin za ta tsaya kan dabarar daukar matakai daya bayan daya da saka alheri da alheri, da neman cimma matsaya ta hanyar tattaunawa. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    An yi cikakken zama na uku na taron shekara shekara na majalisar bada shawarwari kan harkokin siyasar kasar Sin da safiyar yau Lahadi a babban dakin taron al’umma dake birnin Beijing, inda zaunannen memban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar, wanda kuma shi ne shugaban majalisar bada shawarwari kan harkokin siyasar kasar Sin, Wang Huning ya halarci taron, kana, membobin majalisar guda 14 ne suka gabatar da jawabai. A jawabinta, mambar majalisar Ge Huijun ta ce, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da wani muhimmin jawabi a wajen babban taron murnar cika shekaru 75 da kafa majalisar bada shawarwari kan harkokin siyasar kasar, jawabin da ya kafa alkabila da samar da babban tushe ga ci gaban...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce dagewar da wasu kasashe masu cin zarafi suka yi na yin shawarwari da Iran na yi ne don neman amfanin kansu. Ayatullah Khamenei ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ya yi da manyan jami’ai na bangarori uku na gwamnati a ranar Asabar. Jagoran ya ce “Dagewar da wasu gwamnatoci suka yi kan yin shawarwari ba wai don warware al’amura ba ne, a’a yana nufin aiwatar da abin da suke so.” Ayatullah Khamenei ya kara da cewa: ” Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta amince da abin da suke tsammani ba.” Wadannan gwamnatocin da suke cin zalin ba sa neman yin shawarwari kan batun nukiliya...
    3- Rubewar hakora 4- Barazanar kiba 5- Barazanar ciwon zuciya da jijiyoyin jini 6. Barazanar ciwon siga (nau’i na biyu) 7- Haddasa kumburin jiki 8- Barazanar ciwon kashi da gabbai (rheumatoid arthritis) 9- Ciwon daji ko kansa da dai sauran makamantansu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Majalisar bayar da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin (CPPCC), ta kaddamar da taronta na shekara-shekara yau Talata, a nan birnin Beijing. Shugaban kasar Sin Xi Jinping da sauran shugabannin kasar ne suka halarci taron bude zaman na 3 na kwamitin CPPCC karo na 14 da ya gudana a babban dakin taron jama’a. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Da yammacin yau Litinin ne aka gudanar da taron manema labarai na taro na uku, na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin ko CPPCC karo na 14, inda mai magana da yawun taron Liu Jieyi, ya gabatar da yanayin taron ga kafofin watsa labarai na kasar Sin da na waje, tare da amsa tambayoyin manema labarai. A fannin gudanar da ayyuka da ba da shawarwari, Liu Jieyi ya gabatar da cewa, CPPCC ta mai da hankali kan batutuwa masu muhimmanci da wahala, da suka hada da inganta zamanantarwa irin ta Sin, da kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali na zamantakewar al’umma, kuma ta gudanar da ayyuka da suka shafi tattauna batutuwan siyasa guda 85, da aiwatar...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, ta sanar da fara shawarwarin tsagaita wuta a mataki na biyu tsakaninta da Isra’ila. Kakakin Abdul Latif al-Qanou ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a kafar sadarwar zamani. A cikin wata sanarwa da ta fitar a tashar ta Telegram mai magana da yawun kungiyar Abdel Latif al-Qanoua ya zargi Isra’ila da “jinkirta aiwatar da ka’idojin jinƙai a yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma dakatar da aiwatar da hukuncin kisa.” Ya ce har yanzu kungiyar Falasdinu ta damu da batutuwa da dama da suka hada da matsuguni ga mutanen Gaza, da kuma kayan agaji da kuma kokarin sake gina yankin. Al-Qanou ya kuma zargi Isra’ila da “katse” ka’idojin jin kai da ke...
۱