Gwamnonin Arewa sun yi ta’aziyyar mutanen da suka rasu a fashewar tanka a Neja
Published: 22nd, October 2025 GMT
Ƙungiyar Gwamnonin Arewa (NSGF), ta bayyana hatsarin fashewar tankar mai da ya auku a ƙauyen Essa a Ƙaramar Hukumar Katcha a Jihar Neja, a matsayin abin baƙin ciki da tausayi.
Shugaban ƙungiyar kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ne, ya yi alhinin lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.
Ya miƙa saƙon ta’aziyyae ga gwamnatin Jihar Neja da al’ummarta da kuma iyalan da abin ya shafa.
“Wannan lamari abin baƙin ciki ne ƙwarai da gaske. Addu’o’inmu suna tare da iyalan mamatan da kuma jama’ar Jihar Neja a wannan lokaci na jimami,” in ji Yahaya.
Ya kuma gargaɗi jama’a da su guji ɗibar man da ya zube a kan hanya saboda guje wa hatsari.
“Wannan mummunan lamari ya sake tunatar da mu buƙatar tabbatar da ingantattun matakan tsaro da kuma ƙara wayar da kan jama’a game da hatsarin dakon mai.
“Gwamnati, hukumomi da jama’a dole su haɗa kai don hana aukuwar irin waɗannan abubuwan da za a iya gujewa,” in ji shi.
Gwamnan, ya yaba da ƙoƙarin ma’aikatan ceto, jami’an tsaro, da ‘yan sa-kai waɗanda suka yi aiki tuƙuru wajen ceto waɗanda abin ya rutsa da su.
Ya yi addu’ar Allah Ya jiƙan waɗanda suka rasu, Ya kuma bai wa waɗanda suka jikkata lafiya.
Gwamnan, ya kuma tabbatar da cewa ƙungiyar za ta ci gaba da aiki tare da hukumomin gwamnati na tarayya da na jihohi domin ƙarfafa tsarin kare rayuka da dukiyoyin al’umma a yankin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Fashewar tankar mai Gwamnonin Arewa rasuwa ta aziyya
এছাড়াও পড়ুন:
Jirgin sojin sama ya yi hatsari a Neja
Rahotanni na nuna cewar wani jirgin yaƙi na rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF), ya yi hatsari a Jihar Neja.
Jirgin ya faɗi a sansanin NAF da ke Kainji jim kaɗan bayan tashinsa.
Nakiya ta hallaka yara 4 a Borno Kwastam ta kama jirgin ruwan Brazil ɗauke da hodar iblis a LegasMajiyoyi sun ce jirgin ya samu matsala ne, lamarin da ya sa matuƙan jirgin suka ɗauki matakin gaggawa.
Mai magana da yawun NAF, Ehimen Ejodame, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ƙarin bayani na tafe…