Sin Ta Kammala Ginin Cibiyar Adana Bayanai Mai Amfani Da Karfin Iska A Karkashin Ruwa
Published: 22nd, October 2025 GMT
Kasar Sin ta kammala ginin wata cibiyar adana bayanai, irinta ta farko dake karkashin teku kuma mai amfani da lantarki daga karfin iska wato (UDC), wanda aka samar a birnin Shanghai na gabashin kasar. Cibiyar ta zama wani mizanin inganci ta fuskar samar da kayayyakin sarrafa bayanai.
Cibiyar UDC wadda ke da mazauni a yankin Lingang na Shanghai, wanda yanki ne na gwajin cinikayya cikin ‘yanci, ta samu jarin yuan biliyan 1.
A cewar kwamitin gudanar da harkokin yankin Lingang, kammala aikin wata babbar nasara ce ga hadadden aikin samar da cibiyar UDC da kuma makamashi mai tsafta dake cikin teku. Ya kuma nuna yadda aka samar da wani tsarin sarrafa bayanai mai kare muhalli da kuma yadda kasar ke amfani da lantarkin da aka samar daga iska. (Mai fassara: Fa’iza)
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Ci Gaban Kasar Sin Ya Shaida Cewa Yawan Jama’a Ba Dalili Ne Na Rashin Ci Gaba Ba
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Me Aka Gano Kan Makomar Tattalin Arzikin Kasar Sin Daga Karuwar 5.2% Na Tattalin Arzikinta? October 21, 2025
Daga Birnin Sin Jirgin Kasa Mafi Saurin Gudu A Duniya Ya Fara Zirga-Zirgar Gwaji A Sin October 21, 2025
Daga Birnin Sin Jami’an Kasashen Afrika Na Koyon Dabarar Yaki Da Talauci Ta Sin A Jihar Ningxia October 21, 2025