ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin Ta Bayar Da Tallafin Dala Miliyan 3.5 Ga Shirin Samar Da Abinci A Zambia October 21, 2025 Daga Birnin Sin Matsayar Kasar Sin A Bayyane Take Dangane Da Batutuwan Cinikayya Da Tsagin Amurka October 20, 2025 Daga Birnin Sin Sin Ta Kara Wasu Wurare 22 Cikin Yankunan Dausayi Masu Matukar Muhimmanci A Kasar October 20, 2025

.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Gurfanar da Iyayen Yaran da Ba Sa Zuwa Makaranta

Daga Aliyu Muraki

Hukumar Ilimi Matakin Farko ta Jihar Nasarawa (NSUBEB) ta yi barazanar kamawa tare da gurfanar da iyayen da  ‘ya’yansu ba sa zuwa makaranta a jihar.

Shugaban Hukumar, Dr. Kasim Mohammed Kasim ne ya bayyana haka yayin ganawa da manema labarai a matsayin wani bangare na ayyukan babban  taron inganta ilimi da hukumar ta shirya.

Dr. Kasim Mohammed Kasim ya ce, ilimin boko matakin farko haƙƙin kowanne yaro ne, ba gata ba, kuma ya sha alwashin tabbatar da cewa ba a bar wani yaro a baya ba.

Shugaban Hukumar ya bayyana cewa hukumar ta yanke shawarar gudanar da gagarumin wayar da kan jama’a ta hanyar tarurrukan jin ra’ayoyin jama’a, da kafofin watsa labarai domin jaddada muhimmancin ilimin boko na a matakin farko ga kowane yaro a jihar.

Dr. Kasim Mohammed Kasim ya ce sun sayi motocin bas guda bakwai da za a gudanar da wayar da kan jama’a a dukkan sassan kananan hukumomi 13 na jihar, domin fadakar da iyaye  muhimmancin kai ‘ya’yansu makaranta.

Game da babban taron, Dr. Kasim Mohammed Kasim ya ce wannan taro zai hada manyan masu ruwa da tsaki ciki har da masana ilimi, jami’an gwamnati, sarakunan gargajiya, masu tsara manufofi, iyaye, malamai da sauransu.

Ya ce, mahalarta taron za su tattauna hanyoyin magance matsalolin ilimi, musayar kwarewa da sabbin dabaru domin kara inganta koyarwa da koyo a jihar.

Ya lissafo wasu daga cikin matsalolin da suka hada da ginin makarantu marasa inganci, karancin kujeru, karancin malamai, yawan rashin zuwa aiki daga ma’aikata, da rashin daidaitaccen tsarin tura malamai, da sauransu.

Ya ce hukumar ta maida malamai 1,900 wadanda a da ke aiki a ofis-ofis zuwa azuzuwa domin koyarwa, kuma nan ba da jimawa ba za a dauki sabbin malamai 1,000 domin cike gibi a makarantun jihar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ’Yan sanda sun kama tsohon shugaban PCACC, Muhuyi Rimin Gado a Kano
  • Jami’an tsaro sun kama masu garkuwa da mutane 7 a Gombe
  • DSS ta kama likitan da ke duba ’yan bindiga a dazukan Kwara
  • Iran Ta Mayar Da Martani Kan Sanarwar Bayan Taron  Majalisar Kasashen Yankin Tekun Fasha
  • NAPTIP ta daƙile yunƙurin safarar mutum 7 daga Kano zuwa Saudiyya
  • Mutum 6 sun rasu, 13 sun jikkata a hatsarin mota a Kogi
  • An Ga Sojojin Ruwa Na Amurka A Kasar Puerto Rico A Shirinta Na Mamayar Venezuela
  • Kamfanonin jiragen Sama Na Kasashen Yamma Na Neman Izinin Amurka Don Komawa Iran
  • Amurka ta soke bada mafaka ga ‘yan kasashen Afirka 10
  • Gwamnatin Nasarawa Za Ta Gurfanar da Iyayen Yaran da Ba Sa Zuwa Makaranta