ASUU Ta Dakatar Da Yajin Gargaɗi, Ta Bai Wa Gwamnati Wa’adin Wata Guda Don Biyan Buƙatunta
Published: 22nd, October 2025 GMT
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), ta dakatar da yajin aikin gargaɗi na makonni biyu da ta fara.
Ƙungiyar ta kuma bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin wata ɗaya don biyan buƙatunta.
Rashin Abinci Mai Gina Jiki Barazana Ce Ga Lafiyar Al’umma – Gwamna Lawal Majalisa Ta Amince Da Dokar Ɗaurin Rai Da Rai Ga Masu Yi Wa Ƙananan Yara FyaɗeASUU ta yi gargaɗin cewa idan gwamnati ta gaza ɗaukar mataki cikin wa’adin da ta bayar, za ta iya komawa yajin aiki.
এছাড়াও পড়ুন:
Jihar Jigawa Za Ta Kashe Sama Da Biliyan Daya Wajen Gyaran Ajujuwa A Makarantu
Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da Naira biliyan ɗaya domin gyaran ajujuwan karatu a wasu makarantu na gwamnati.
Kwamishinan Yaɗa Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Dutse.
A cewarsa, majalisar zartarwar jihar ta amince da kashe fiye da Naira miliyan 528 domin gyaran ginin ajujuwa a wasu zababbun makarantu na gwamnati a fadin jihar.
Ya bayyana cewa, manufar aikin ita ce inganta yanayin karatu, tabbatar da tsaro, da kuma samar da iingantaccen ilimi karkashin shirin gwamnatin jihar na farfado da ilimin asali.
Sagir Musa ya kuma ce, majalisar ta amince da kashe sama da Naira miliyan 512 domin samar da kujeru da gadajen ɗalibai, domin ƙarfafa tsarin ilimi tare da tabbatar da walwala da inganci a makarantu.
Usman Mohammed Zaria