Wakilin Amurka Na Musamman A Siriya Ya Matsa Don Ganin Kasashen Saudiyya Da Lebanon Da Kuma Siriya Sun Kulla Alaka Da Isra’ila
Published: 20th, October 2025 GMT
Wakilin Amurka na Musamman a kasar Siriya ya matsa kaimi domin ganin kasashen Saudiyya da Lebanon da kuma Siriya sun kulla alakar jakadanci da haramtacciyar kasar Isra’ila
Wakilin Amurka na musamman a Siriya Tom Barrack, ya gabatar da manufofinsa na sake fasalin yankin Gabas taTsakiya a siyasance bayan kawo karshen yakin Gaza.
A cikin dogon hangen nesa, wanda ya wallafa a shafinsa na Twitter, Barrack ya yi ikirarin cewa abu mafi muhimmanci shi ne samar da zaman lafiya a yankin, da kwance damarar Hizbullah, da shigar da kasashen Labanon da Siriya cikin yarjejeniyoyin kyautata alaka da haramtacciyar kasar Isra’ila. Ya kara da cewa Saudiyya ma tana dab da kyautata alakarta da haramtacciyar kasar Isra’ila.
Barrak ya bayyana cewa: Taron Sharm el-Sheikh da aka gudanar a ranar 13 ga watan Oktoba tare da halartar shugaba Trump da shugabannin kasashen Larabawa da na musulmi, ya wakilci wani muhimmin lokaci a harkokin diflomasiyya na zamani na gabas ta tsakiya, la’akari da cewa abin da aka fara a matsayin sulhu a Gaza ya rikide zuwa “sabon aikin hadin gwiwa da shugaba Trump ya jagoranta na sake ginawa da bunkasa ci gaban yankin.”
Barrak ya yi imanin cewa, kasashen Larabawa da na yammacin duniya sun hade kansu a kan manufar “maye gurbin tsoro da dama da kuma keben wata kasa da bude kofa,” yana mai cewa taron na Sharm el-Sheikh “ba wai kawai bikin tsagaita bude wuta ba ne da kuma sako mutanen da aka yi garkuwa da su ba, a’a mafarin shirin zaman lafiya na dogon lokaci da ya danganci ci gaba da hadewar yankin,” in ji shi.
Amnesty International
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kungiyar Kare Hakkin Bil-Adama Ta Amnesty Ta Zargi Gwamnatin Tanzaniya Da Musgunawa ‘Yan Adawa October 20, 2025 Dakarun kare Juyin Musulunci Na Iran Sun Bayyan Shirinsu Na Karfafa Dabarun Hadin Guiwa Da yamen October 20, 2025 October 20, 2025 Kotu A Faransa Ta Yanke Hukumci Zama Gidan Yari Ga Tsohon Shugaban Kasar Nicola Sarkozi October 20, 2025 Isra’ila Ta Keta Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta Sau 80 Ta Kashe Mutane 97 Ta Jikkata 230 October 20, 2025 Arewa Ta Samu Kashi 56% Na Mukaman Gwamnatin Tinubu inji Shugaban FCC October 20, 2025 Grossi: Za a iya warware batun Shirin nukiliyar Iran ne kawai ta hanyar diflomasiyya October 20, 2025 Trump: Shugabanin Hamas ba su da hannu a kisan sojojin Isra’ila 2 a Gaza October 20, 2025 Iran Da Azerbaijan Suna Gudanar Da Atisayen Hadin Guiwa Na Sojojin Ruwa A Tekun Caspian October 20, 2025 Gwamnatin Yamen Tana Tsare Da Ma’aikatan MDD 50 Ta Kuma Kwace Kayakin Aikinsu October 20, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Lebanon: An Gudanar Da Taron Musulunci da Kiristanci a Beirut tare da halartar Paparoma
Paparoma Leo XIV ya halarci taron Musulunci da Kiristanci da tattaunawa tsakanin addinai a dandalin Shahidai da ke Beirut.
Bayan isowarsa, Paparoma ya samu tarba daga shugaban Mabiya addinin kirista na Lebanon Bechara Boutros al-Rahi, da shugaban Mabiya darikar Katolika na Syria Ignatius Joseph III Younan, da kuma Babban Mufti na Lebanon Sheikh Abdul Latif Derian, da Mataimakin Shugaban Majalisar koli ta Mabiya mazhabar Shi’a a Lebanon Sheikh Ali al-Khatib.
A lokacin taron, Mataimakin Shugaban Majalisar Shi’a a Lebanon ya yi maraba da Paparoma, yana mai cewa: “Muna farin ciki da zuwnku a Lebanon a madadin Majalisar da kuma daukacin mabiya mazhabar shi’a na Lebanon, Muna maraba da kuma godiya da ziyararku zuwa kasarmu a wannan mawuyacin lokaci da kasarmu ke ciki.”
Ya ƙara da cewa: “Muna fatan ziyararku za ta taimaka wajen ƙarfafa haɗin kan ƙasa wadda ke fama da raunukan da hare-haren Isra’ila ke ci gaba da haifarwa na zalunci.”
Ya ci gaba da cewa: “Ba ma son ɗaukar makamai, kuma muna sanya alkiblar Lebanon ta zama a hannu na gari, muna fatan duniya za ta taimaka wa ƙasarmu ta sami zaman lafiya.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Chuck Schumer: Trump Ba Shi da Ikon Kaddamar da Yaki Kan Venezuela December 2, 2025 Najeriya: Matatar Dangote Za Ta Mika Tataccen Mai Lita Biliyan 1.5 A Watan Disamba December 2, 2025 Ramaphosa ya yi watsi da barazanar Trump na ware Afirka ta Kudu daga G20 December 2, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 165 December 1, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan 164 December 1, 2025 Baqaei: Amurka Ce Babbar Barazana Ga Zaman Lafiya Da Tsaro A Duniya December 1, 2025 Paparoma Leo Na 14 Yana Ziyarar Aiki Na Kwanaki 3 A Kasar Lebanon December 1, 2025 Kamaru: Madugun Adawa Ya Rasu A Gidan Kaso December 1, 2025 Tawagar ECOWAS Ta Bar Guinea – Bissau bayan da shugaban kasar yayi barazanar korarsu Da Karfi December 1, 2025 Yawan Yahudawan Da Suke Ficewa Daga HKI Sun Nininka Har Sau 100% December 1, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci