Nigeria: “Yan Sanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar Neman Sakin Jagoran ‘Yan Awaren Biafara
Published: 21st, October 2025 GMT
‘Yan sanda a birnin Abuja sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa Zanga-zangar masu neman a saki jagoran ‘yan awaren Biafar Nnamdi Kanu wanda ake yi wa shari’a bisa tuhumarsa da ayyukan ta’addanci.
Shi dai Kanu yana jagorantar kungiyar ‘yan asalin Biarafa ( Ipob) a takaice wacce a hukumance an haramta, saboda kiran da take yin a balle yankin kudu masu gabashin kasar da ‘yan kabilar Igbo suke da rinjaye domin kafa musu kasa mai cin gashin kanta.
Jami’an tsaro sun rika yin sintiri a tsakiyar birnin Abuja, da motoci masu silke da kuma masu watsa ruwan zafi. Haka nan kuma sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye akan masu goyon bayan kungiyar da su ka yi kokarin taruwa.
Bugu da kari, an ga wani adadi na sojoji suna taimakawa ‘yan sandan a kokarin tarwatsa masu Zanga-zangar.
Shi dai Kanu ana tsare da shi ne tun a 2021, da hakan ya sa masu goyon bayansa suke yin kira da a sake shi, da kuma yin watsi da zargin aikin ta’addanci da ake yi masa. Kanu dai ya sha kore tuhume-tuhumnen da ake yi masa a duk lokacin da aka gabatar da shi a gaban kotu.
Nigeria ta yi yakin Basasa na tsawon shekaru 3 da ya fara a 1967, wanda kuma ya ci rayukan fiye da mutane miliyan daya.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka HKI Tana Ci Gaba Da Hana Wa Falasdinawa Abinci October 21, 2025 An Yi Fashi Da Makami A Gidan Adana Kayan Tarihin ” Louvre” Na Kasar Faransa October 21, 2025 Yemen : An yi jana’izar babban hafsan sojin kasar Shahid al-Ghamari a Sana’a October 21, 2025 Iran da Iraki sun bukaci duniya da ta dakatar da kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a Gaza October 21, 2025 Equatorial Guinea ta zargi Faransa da karan-tsaye wa zaman lafiya a kasar October 21, 2025 Faransa : Sarkozy, ya fara zaman gidan yari na shekara 5 October 21, 2025 Gaza : Falasdinawa 97 sojin Isra’ila suka kashe tun bayan cimma yarjejeniya October 21, 2025 Iran Da Faransa Zasu Yi Musayar Fursinoni, Esfandiari Tana Daga Cikin Wacce Za’a Sallama October 21, 2025 Gaza: Isra’ila Ta Kashe Falasdinawa 57 A Cikin Sa’o’i 24 Da Suka Gabata October 21, 2025 Kakakin Majalisar Dokokin Kasar Lebanon Ya Ce Babu Wata Tattaunawa Da HKI October 21, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Nijar ta maka kamfanin hakar uranium na Faransa Orano kotu
Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta bayyana aniyar maka hamshakin kamfanin nan na hakar uranium na faransa (Orano) a gaban kotu bayan gano sinadarai masu guba a yankin Madaoulela, dake arewacin kasar.
Dama dai Nijar da Orano sun sun shafe watanni suna takaddama kan sinadarin uranium da ake fitwarwa a kamfanin Somaïr, wanda aka mayar da shi mallakin kasar ta Nijar a watan Yuni.
Ministan Shari’a na Nijar, Alio Daouda, ne ya sanar da hakan a lokacin wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar Talata nan.
Ministan ya ce an gano “ganguna 400 da ke dauke da samfuran sinadarai masu guba” a wani tsohon wurin hakar ma’adinan uranium a wani waje da Orano ya fice a yankin Arlit, wanda ke arewacin Nijar.
“Wannan kamfani ya cutar kuma yana ci gaba da cutar da lafiyar al’ummar Nijar ta hanyar amfani da sinadarai masu guba, da sanya rayuwar wasu cikin hadari, da kuma lalata muhalli.
Kamfanin ya ma ki bin umarnin kotu da kotunanmu suka bayar wanda ya tilasta masa na kwashe milyoyin tan na sharar tiriri mai guba na rediyoaktif da aka bari a sararin samaniya, in ji ministan na Nijar.
Ministan Shari’a na Nijar ya bayyana cewa Nijar ta dauki dukkan matakan da suka wajaba don gurfanar da Orano da kuma samun diyya kan duk barnar da aka yi wa Nijar.”
Orano, kamfani ne mallakar gwamnatin Faransa, wanda ya maye gurbin Areva, wacce ke rike da ikon mallakar hakar uranium na Nijar sama da rabin karni, saidai bayan juyin mulkin sojiji a ranar 26 ga Yuli, 2023, sabbin hukumomin Nijar sun yanke dukkan yarjejeniyoyi tsakanin Nijar da Faransa, ciki har da na hakkin hakar uranium na Orano.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Amurka ta soke bada mafaka ga ‘yan kasashen Afirka 10 December 3, 2025 Masar Ta Sanar Da Tattaunawa Da Amurka Don Shirya Sake Gina Gaza December 3, 2025 Isra’ila Ta Hana Motocin Agaji 6000 Shiga Gaza Duk Da Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta December 3, 2025 Kasar Qatar Ta Gargadi Isra’ila Game Da ci Gaba Da Keta Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta A Gaza December 3, 2025 Sharhi: HKI tana fama da karancin sojoji a dukkan rassan sojojin kasar December 2, 2025 Shugaba Pizishkiyan: Goyon Bayan Al’ummar Iran Ga Tsarin Musulunci Ne Ya Hana Abokan Gaba Cimma Manufa December 2, 2025 Shugaban Kasar Najeriya Ya Nada Janar Chiristopher Musa ( Ritaya) A Matsayin Ministan Tsaro December 2, 2025 Nigeria Ta Bai Wa Dan Takarar Shugabancin Kasar Guine Bissau Mafakar Siyasa December 2, 2025 Palasdinu: Sojojin “Isra’ila” 3 Su Ka Jikkata Sanadiyyar Taka Su Da Mota December 2, 2025 Hamas Ta Caccaki Isra’ila Game Da Hana Shigar Da Kayayyakin Agaji A Yankin Gaza December 2, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci