Majalisar Najeriya Ta Amince Da Dokar Daurin Rai Da Rai Ga Masu Yi Wa Kananan Yara Fyade
Published: 22nd, October 2025 GMT
Majalisar Dattawa ta amince da sabuwar doka da ta tanadi daurin rai da rai ga duk wanda aka samu da laifin lalata da yaro ko yarinya karama.
Dokar na son kare hakkokin kananan yara ne, kuma ta shafi maza da mata baki daya, ba tare da wani zabi na biyan tara ba. Sanata Adams Oshiomhole (Edo ta Arewa), ya ce yara ba su da iko ko yardar wajen amincewa da yin jima’i kuma irin wannan abu na jefa su cikin tashin hankali har abada.
Da farko ya ba da shawarar a daure mai laifi na tsawon shekaru 20, amma yawancin sanatoci sun nemi hukunci mafi tsauri.
Sanata Muhammad Adamu Aliero (Kebbi ta Tsakiya) ya bayar da shawarar daurin rai da rai, kuma majalisar ta amince da wannan gyara baki daya.
Zaa tura Dokar zuwa Majalisar Wakilai don amincewa da ita kafin a aike wa Shugaban kasa sanya hannu.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Birtaniya Ta Cire Kungiyar Tahrirush -Sham Daga Jerin Yan Ta’adda October 22, 2025 China Ta Kammala Gina Cibiyar Adana Bayanai Masu Amfani Da Karfin Iska October 22, 2025 Iran Ta Godewa Rasha Game Da Goyon Bayan Da Ta Bata A Kwamitin Sulhu Na M D D October 22, 2025 Sudan: Jirgin ‘Drone’ Ya Fada Kan Tashar Jiragen Sama Na Khurtum Kafin A Sake Bude Ta October 22, 2025 Sheikh Qasim: Natanyahu Ya Zubar Da Jini Mai Yawa Amma Babu Lamuni Ga Amincin Isra’ila Nan Gaba October 22, 2025 Aragchi Da Guterres Sun Tattauna Kan Gaza Da Rikicin Yemen Ta Wayar Tarho October 22, 2025 Rasha da Habasha sun tattauna kan karfafa hadin gwiwa a tsakaninsu a fannin nukiliya October 22, 2025 Sayyed al-Houthi: Mun shirya dawowa fagen daga idan Isra’ila ta ci gaba da kisan kiyashi a Gaza October 22, 2025 Nigeria: “Yan Sanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar Neman Sakin Jagoran ‘Yan Awaren Biafara October 21, 2025 HKI Tana Ci Gaba Da Hana Wa Falasdinawa Abinci October 21, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Mayar Da Martani Kan Sanarwar Bayan Taron Majalisar Kasashen Yankin Tekun Fasha
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Esmail Baghaei ya yi Allah wadai da kakkausar murya da sanarwar bayan taron shugabannin Kasashen Yankin Tekun Farisa (GCC) wanda suka fitar game da tsibiran Iran guda uku.
Baghhaei ya nuna takaici kan dagewar da kungiyar GCC ta yi kan maimaita ikirari maras tushe na Hadaddiyar Daular Larabawa game da tsibiran Abu Musa, Greater Tunb, da Lesser Tunb na Iran.
Ya yi Allah wadai da ikirarin da ke cikin sanarwar karshe ta taron kolin GCC karo na 46 game da wadannan tsibirai na kasar Iran, yana mai jaddada cewa Abu Musa, Greater Tunb, da Lesser Tunb muhimmin bangare ne na yankin Iran kuma duk wani ikirari sabanin hakan ba shi da inganci, kuma a bayyane yake ya saba wa ka’idar girmama mutuncin yankin kasashe da kyakkyawar makwabtaka.
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Waje ya jaddada manufar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kyakkyawar maƙwabtaka da haɗin gwiwa da ƙasashen da ke makwabtaka da ita don ƙarfafa dangantaka da kuma kiyaye tsaro da kwanciyar hankali a yankin.
Ya yi kira ga Hadaddiyar Daular Larabawa da Majalisar Haɗin Kan Kasashen Gulf da su guji ɗaukar matakai masu tayar da hankali waɗanda suka saɓa wa kyakkyawar alaƙar maƙwabta da Iran.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Afirka ta Kudu Za Ta Dauki Hutu Daga Halartar Tarukan G20 A Karkashin Shugabancin Trump December 5, 2025 Microsoft Za Ta Fuskanci Hukunci Kan Taimaka Wa Laifukan Isra’ila A Kan Falasdinawa December 5, 2025 Amurka Tana Sake Yin Bitar Alakar Da Ke Tsakaninta Da Tanzania December 5, 2025 Fadlallah Na Hizbullah Ya Yi Kiran Hadin Kai A Tsakanin Musulmi Da Larabawa Domin Fuskantar Kalubale December 4, 2025 Jiragen Haramtacciyar Kasar Isra’ila Sun Kai Hare-hare A Kudancin Lebanon December 4, 2025 An Kira Yi Gwamnatin Canada Da Ta Kama Olmert Da Livini Na “Isra’ila December 4, 2025 An Kashe Shugaban ‘Yan Dabar Gaza “Abu Shabab” Da Isra’ila Ke Goyon Baya December 4, 2025 Iran : Jagora Ya Bayyana Ra’ayin Musulunci Kan Hakkokin Mata December 4, 2025 Taron IMO : Tehran Ta Yi Watsi Da Zarge-zargen Isra’ila Marasa Tushe December 4, 2025 MDD ta nemi a kawo karshen mamayar Isra’ila a Falasdinu da kuma Tuddan Golan December 4, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci