Kasashen Iran da Iraki sun bukaci duniya da ta dakatar da kisan kiyashin da Isra’ila ke yi wa Falasdinawa a Gaza

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi da mai baiwa kasar Iraki shawara kan harkokin tsaro Qasim al-Araji sun bukaci kasashen duniya da su dakatar da kisan gillar da gwamnatin Isra’ila ke yi wa Falasdinawa a zirin Gaza.

Al-Araji, wanda ke jagorantar wata tawagar jami’an tsaro a kasar Iran, ya gana da Araghchi a yammacin jiya Litinin, inda suka yi musayar ra’ayi da su kan hanyoyin inganta hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu, da kuma tattauna halin da ake ciki a Gaza da Lebanon.

Dukkan jami’an biyu sun bayyana damuwarsu kan yadda Isra’ila ke ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza, sannan sun bukaci kasashen duniya da su dauki matakin dakatar da kisan kiyashi da laifukan da gwamnatin mamaya ke yi wa Falasdinawa, tare da tabbatar da isar da kayan agajin jin kai.

Araghchi ya bayyana kyakkyawar alakar da ke tsakanin Tehran da Bagadaza daga dukkan fannoni, inda ya jaddada bukatar ci gaba da tuntubar juna da karfafa hadin gwiwa kan harkokin tsaro, musamman a fannin kula da kan iyaka.

Al-Araji ya kuma yi wa Araghchi bayanin ci gaban da aka samu wajen aiwatar da yarjejeniyar tsaro ta tsakanin Iran da Iraki, yana mai jaddada aniyar Bagadaza na ci gaba da tabbatar da ita.

Ya yaba da hadin kai da tsayin daka da al’ummar Iran suke da shi wajen tunkarar wuce gona da iri na kasashen waje, yana mai tabbatar da cewa Iraki ba za ta taba bari a yi amfani da yankinta wajen yin barazana ga ‘yancin kai ko tsaron kasar Iran ba. Bangarorin biyu sun kara jaddada bukatar hadin kan kasashen musulmi wajen tunkarar manufofin wuce gona da iri na Isra’ila

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Equatorial Guinea ta zargi Faransa da karan-tsaye wa zaman lafiya a kasar October 21, 2025 Faransa : Sarkozy, ya fara zaman gidan yari na shekara 5 October 21, 2025 Gaza : Falasdinawa 97 sojin Isra’ila suka kashe tun bayan cimma yarjejeniya October 21, 2025 Iran Da Faransa Zasu Yi Musayar Fursinoni, Esfandiari Tana Daga Cikin Wacce Za’a Sallama October 21, 2025 Gaza: Isra’ila Ta Kashe Falasdinawa 57 A Cikin Sa’o’i 24 Da Suka Gabata October 21, 2025 Kakakin Majalisar Dokokin Kasar Lebanon Ya Ce Babu Wata Tattaunawa Da HKI October 21, 2025 Tom Barak: Saudiyya na gab da kulla alaka da Isra’ila a hukumance October 21, 2025 Kremlin: Rasha a shirye take don fadada hadin gwiwa da Iran a dukkanin fannoni October 21, 2025 Jagora Ya Mayar Da Martani Ga Trump Cewa; Su Ci Gaba Da Mafarkinsu October 20, 2025 Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Jaddada Aniyarta Ta Yin Riko Da Hakkokin Kasarta October 20, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: dakatar da kisan da Isra ila Isra ila ke

এছাড়াও পড়ুন:

Microsoft Za Ta Fuskanci Hukunci Kan Waimaka Wa Isra’ila A  Laifukan Da Take Aikatawa Kan Falasdinawa

Microsoft na fuskantar matsin lamba da kuma matakin shari’a saboda samar wa Isra’ila fasahar da ake amfani da ita wajen take hakkin Falasdinawa a Gaza da Yammacin Kogin Jordan.

A cikin wata budaddiyar wasika da aka aike wa kamfanin a ranar 2 ga wannan watan, wata kungiyar lauyoyi ta kasa da kasa ta yi gargadin cewa Microsoft da shugabanninta za su iya fuskantar hukunci na shari’a kan taimakawa da kuma tallafawa laifukan da aka aikata wa fararen hula Falasdinawa.

Eric Saib, mai kula da harkokin ci gaban kafofin watsa labarun kasa da kasa na Cibiyar Larabawa don Ci gaban Kafafen Yada Labarai, ya  jaddada cewa watannin baya-bayan nan sun nuna karara cewa ana amfani da ayyukan kamfanin wajen take hakkin dan adam a Falasdinu, yana mai kira ga masu hannun jari da su fahimci hadarin da ke tattare da ci gaba da wannan hadin gwiwa.

Wasikar ta bayyana cewa Microsoft tana bai wa sojojin Isra’ila na kasa, sama, da na ruwa bayanai masu mahimmanci duk da amincewa tsakanin kungiyoyin kare hakkin dan adam da kwararru cewa Isra’ila tana aikata kisan kare dangi a Gaza.

A cikin wani rahoto da aka fitar a ranar 30 ga Yuni, Jami’ar Majalisar Dinkin Duniya ta Musamman kan Kare Hakkin Dan Adam, Francesca Albanese, ta nuna cewa kamfanoni sama da sittin daga sassa daban-daban sun ba da gudummawa wajen rusa  Gaza, tallafawa ayyukan gina matsugunan Yahudawa a Yammacin Kogin Jordan, da kuma tilasta wa Falasdinawa yin hijira, ciki har da manyan kamfanonin Amurka kamar Amazon, Google, IBM, da Microsoft.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Amurka Tana Sake Yin Bitar Alakar Da Ke Tsakaninta Da Tanzania December 5, 2025 Fadlallah Na Hizbullah Ya Yi Kiran Hadin Kai A Tsakanin Musulmi Da Larabawa Domin Fuskantar Kalubale December 4, 2025  Jiragen Haramtacciyar Kasar Isra’ila Sun Kai Hare-hare A Kudancin Lebanon December 4, 2025  An Kira Yi Gwamnatin Canada Da Ta Kama Olmert Da Livini Na “Isra’ila December 4, 2025 An Kashe Shugaban ‘Yan Dabar Gaza “Abu Shabab” Da Isra’ila Ke Goyon Baya December 4, 2025 Iran : Jagora Ya Bayyana Ra’ayin Musulunci Kan Hakkokin Mata December 4, 2025 Taron IMO : Tehran Ta Yi Watsi Da Zarge-zargen Isra’ila Marasa Tushe December 4, 2025 MDD ta nemi a kawo karshen mamayar Isra’ila a Falasdinu da kuma Tuddan Golan December 4, 2025 Rundunar Ruwa ta IRGC na Gudanar Da Atisayen Soja a Tekun Fasha December 4, 2025 Dan wasan Taekwando Na kasar Iran Ya Samua Lambar Yabo Ta Zinariya December 4, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Iran Ta Raya Ranar Haramta Takunkuman Bangare Guda A Duniya
  • Microsoft Za Ta Fuskanci Hukunci Kan Waimaka Wa Isra’ila A  Laifukan Da Take Aikatawa Kan Falasdinawa
  • An Kashe Shugaban ‘Yan Dabar Gaza “Abu Shabab” Da Isra’ila Ke Goyon Baya
  • Iran : Jagora Ya Bayyana Ra’ayin Musulunci Kan Hakkokin Mata
  • MDD ta bukaci a kawo karshen mamayar Isra’ila a Falasdinu da kuma janyewa daga Tuddan Golan na Siriya
  • Hamas Za ta Mikawa Isra’ila Samfurin  Da Aka Samu A Karkashin Burabutsai A Yankin Gaza
  • Iran Ta ce Tsaron Yankin Tekun Fasha Jan Layi Ne Da Za’a Fuskanci Mayar Da Martani Adan Aka Taba Shi
  • Kungiyar Guinness Ta Rigistan Ayyukan Bajinta Ta Duniya Ta Dakatar Da Karban Daga HKI
  • Masar Ta Sanar Da Tattaunawa Da Amurka Don Shirya Sake Gina Gaza
  • Isra’ila Ta Hana Motocin Agaji 6000 Shiga Gaza Duk Da Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta