2025-06-30@23:37:32 GMT
إجمالي نتائج البحث: 6199

«kasar China»:

    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana a yau cewa, a shekarun baya-baya nan, an gwada sabbin kayayyayin fasahohin zamani kamar mutum-mutumin inji mai siffar dan Adam, da gilas na zamani, da na’urorin ba da jinya dake hade da kwakwalwa da inji da sauransu, a dandalin bikin baje koli na kayayyakin shige da fice na Guangzhou wato Canton Fair, da bikin baje koli na kayayyakin sayayya na kasa da kasa, da bikin baje koli na kayayyakin da ake samarwa na kasa da kasa wato CISCE da sauransu. Wadannan bukukuwan baje koli sun shaida sabon karfin Sin na samar da hajoji da hidimomi masu karko, kana sun kasance muhimmin gadar dake hade sassan kasa da kasa kan mu’amalar...
    Wani ɗan Fashi da makami ya rasa ransa bayan da yayi yunƙurin yin fashi a unguwar Dorayi Babba, Unguwar Jakada, Kano. Rahotanni sun bayyana cewa ɓarawon, wanda aka gano sunansa Musa Nuhu, ya kutsa cikin wani gida riƙe da makami, wata wuka da nufin yin fashi a wani gida. Bayan shiga cikin gidan, ɓarawon ya kai hari kan wasu mata biyu tare da jikkata su. Sai dai wani namiji daga cikin iyalan gidan yai taho mu gama da ɓarawon a cikin wata fafatawa mai zafi da ta jawo raunika a tsakaninsu duka biyu. Gwamna Yusuf Ya Jagoranci Tawagar Kano Zuwa Jana’izar Marigayi Aminu Dantata A Madina An Sauya Sunan Makarantar Wasanni Don Girmama Ƴan Kano Da Suka Yi Hatsari Kakakin...
    A yau Litinin ne shugaban kasar Sin, kuma babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, ya jaddada bukatar yin aiki tukuru wajen aiwatar da cikakkun manufofi, na ingiza managarcin jagorancin jam’iyyar bisa kyawawan akidu. Shugaba Xi ya yi kiran ne cikin tsokacin da ya yi, lokacin da yake jagorantar taron nazari na jami’an hukumar siyasar na kwamitin kolin JKS. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumar kiwon lafiya ta kasar Sin, ta yi watsi da bangaren rahoton kwamitin SAGO, na masana kimiyya mai bayar da shawara game da asalin kwayar cutar da ta haddasa annobar COVID-19, wanda hukumar lafiya ta duniya WHO ta fitar. Wata sanarwa da hukumar ta fitar a Litinin din nan, ta ce a ranar 27 ga watan Yunin nan, kwamitin SAGO, ya wallafa wani rahoto game da tushen kwayar cutar SARS-CoV-2, wadda ta haddasa barkewar annobar COVID-19. Sanarwar ta ce, duk da yake bincike mai zaman kansa da kwamitin SAGO ya gudanar bai nuna wata sabuwar shaida game da asalin kwayar cutar ba, bai kuma bayyana wani abu da ya saba da sakamakon binciken hadin gwiwa tsakanin Sin da WHO na...
    Tsohon Gwamnan Anambra, Peter Obi ya ce zai yi takarar shugabancin Nijeriya a 2027 domin ba zai shiga duk wata yarjejeniyar haɗakar takara da kowa ba. Obi wanda ya yi takarar shugabancin Nijeriya a Zaben 2023 a karkashin inuwar jam’iyyar Labour (LP), ya tabbatar wa magoya bayansa cewa babu gudu babu ja da baya dangane da takararsa a babban zaɓen kasar na gaba. An sanya dokar hana fita a Kaduna An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata zuwa Talata Sai dai ya ce idan har akwai wata yarjejeniya da zai kulla, ba za ta wuce wacce za ta ba shi damar zama shugaban ƙasa na wa’adi daya ba, sannan ya miƙa wa shugaba na gaba mulki a ranar 28 ga watan Mayun...
    Shugaban kasar Iran ya soki lamirin hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA A wata tattaunawa ta hanyar wayar tarho da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron a yammacin jiya Lahadi, shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi Allah wadai da dabi’ar nuna fuska biyu daga Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya, yana mai cewa irin wannan dabi’a ta nuna fuska biyu za ta janyo rugujewa da haifar da matsaloli da dama ga tsaron yankin da ma duniya baki daya. A yayin wannan tattaunawa, shugaba Pezeshkian ya ce, wadannan ayyuka na nuna fuska biyu sun haifar da matsaloli da dama ga harkokin tsaro na yanki da na duniya, kuma ana sa ran hukumar kula da makamashin nukiliya ta IAEA za ta...
    A wata tattaunawa ta hanyar wayar tarho da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron a yammacin jiya Lahadi, shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi Allah wadai da dabi’ar nuna fuska biyu daga Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya, yana mai cewa irin wannan dabi’a ta nuna fuska biyu za ta janyo rugujewa da haifar da matsaloli da dama ga tsaron yankin da ma duniya baki daya. A yayin wannan tattaunawa, shugaba Pezeshkian ya ce, wadannan ayyuka na nuna fuska biyu sun haifar da matsaloli da dama ga harkokin tsaro na yanki da na duniya, kuma ana sa ran hukumar kula da makamashin nukiliya ta IAEA za ta mutunta haƙƙin kasashe da guje wa ɗabi’a nuna fuska biyu a fagen ayyukanta da...
    Dakatar da ayyukan wuce gona da iri kan Iran wani sharadi ne na ci gaba da tattaunawar makamashin nukiliya Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin siyasa Majid Takht-e Ravanchi ya bayyana cewa: Sharadin ci gaba da gudanar da zaman shawarwarin makamashin nukiliyar Iran shi ne dakatar da duk wani matakin wuce gona da iri kan Iran, kuma har yanzu Amurka ba ta dauki wani mataki ba kan wannan batu. A wata hira da tashar BBC game da batun tattaunawar makamashin nukiliyar Iran da Amurka: Takht-e Ravanchi ya ce: “Sun ji daga Amurka cewa a shirye take ta ci gaba da tattaunawar, amma har yanzu ba a tsayar da ranar ba, kuma Iran ba ta amince da...
    Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta bayyana cewa: Dokar Majalisar Shawarar Musulunci ta kasar ta dakatar da hadin gwiwa da hukumar IAEA dole ne aiki da ita Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, Ismail Baqa’i ya bayyana a wani taron manema labarai cewa: Dole ne hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ta yi aiki nesa da batun siyasa, yana mai nuni da cewa: Dokar Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran kan dakatar da hadin gwiwa tsakanin Iran da hukumar ta IAEA, dole ne yin aiki da ita. Ya ce wannan doka ta tana nuna damuwa da fushin al’ummar Iran ne dangane da hare-haren wuce gona da iri da aka kaiwa cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran da kuma kisan gillar da aka yi...
    A bisa jagorancin Alhaji Mustapha Junaid, iyalan mamacin, da suka haɗa da matan sa da ‘ya’ya da jikokin sa, sun tarbi tawagar, kuma sun yi masu godiya. Minista Badaru ya miƙa saƙon ta’aziyya daga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana cewa, “Rasuwar Baba Aminu ta taɓa Shugaba Tinubu matuƙa. Yana addu’ar Allah ya yi masa sakayya da gidan Aljannar Firdausi, kuma yana ba dukkan iyalan sa haƙurin su yi jimirin jure wannan babban rashi.” Jakaden Nijeriya a Saudi Arebiya, Ambasada Ibrahim Modibbo, da Babban Jagoran Aikin Jakadanci, Ambasada Mu’azam Ibrahim Nayaya, da Jami’in Kula da Tsaro a Ofishin Jakadanci, Manjo Janar Adamu Hassan, duk suna cikin tawagar. Malaman da aka je da su kuma duk sun yi addu’o’i ga marigayi...
    Cibiyar nazarin harkokin jigilar kayayyaki da sayayya da bayar da hidimomi ta hukumar kididdiga ta kasar Sin ta sanar a yau cewa, alkaluman yawan kayayyakin da masana’antu ke sayarwa (PMI) na kasar a watan Yuni, sun kai kaso 49.7, karuwar maki kaso 0.2 kan na watan da ya gabata. Duk da cewa akwai sauye-sauye a yanyin tafiyar tattalin arzikin kasar Sin a rabin farko na bana, daga alkaluman na PMI za a iya ganin yadda tattalin arzikin ke ingantuwa da samun tagomashi yadda ya kamata, tare da nuna juriya mai karfi. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp...
    Iran ta bukaci gudanar da binciken gaggawa na Majalisar Dinkin Duniya kan harin da yahudawan sahayoniyya suka kai gidan kurkukun Evin A cikin wata wasika da ya aike wa babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya da shugaban kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniyar, jakada kuma zaunannen wakilin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya, Amir Sa’ed Irawani, ya yi kira da a gaggauta gudanar da bincike mai tsanani kan harin da ‘yan sahayoniyya suka kai gidan yarin Evin da ke birnin Tehran. A cikin wasikar, Irawani ya rubuta cewa: Wannan harin da aka kai a ranar Litinin, 23 ga watan Yunin wannan shekara ta 2025, an nufi wani gidan yarin farar hula da gangan, wanda hakan ya sabawa dokokin kare hakkin...
    Dalibai 29 ne suka rasa rayukansu sakamakon turmutsitsin a Jamhuriyar Afrika ta tsakiya yayin tserewa fashewar taransifoma Akalla dalibai 29 ne suka mutu a birnin Bangui na kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a wani turmutsutsu sakamakon fashewar tiranfomar lantarki a lokacin jarrabawar sakandare, a cewar ma’aikatar lafiya ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Wata takarda daga ma’aikatar lafiya ta ce: “Mutane 29 ne suka rasa rayukansu bayan an kai su asibitocin birnin Bangui.” Ba a samu ingantattun bayanan yawan wadanda suka mutu ba har zuwa yammacin ranar Larabar da ta gabata, a lokacin da fashewar ta faru, sama da dalibai 5,300 ne ke zana jarrabawar kwana na biyu na jarabawar sakandare.
    Gabanin fara wasannin ƙasashen Afrika na ƙwallon ƙafa ta mata da hukumar ƙwallon ƙafa ta nahiyar Afirka (CAF) ta shirya a ƙasar Morocco da za a fara a ranar Asabar, Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afrika (CAF) za ta ƙaddamar da sabon kofin gasar a wani ɓangare na ƙoƙarin ɗaukaka wasan ƙwallon ƙafa na mata a nahiyar Afrika. A ranar Laraba, 02 ga watan Yuli na shekarar 2025 za a ƙaddamar da sabon kofin gasar cin kofin Afrika ta mata a ƙasar Morocco, ƙasar da za ta karɓi baƙuncin gasar ta bana, sabon kofin wani ɓangaren ne na burin shugaban CAF Dr Patrice Motsepe na bunƙasa ƙwallon ƙafa na mata a Afrika. NDLEA Ta Kai Samame Fitattun Wuraren Shaye-shaye, Ta Cafke...
    Kasar Sin ta kawo karshen aikin bayar da agajin gaggawa mafi girma a gundumar Rongjiang da ke lardin Guizhou, a yankin kudu maso yammacin kasar da misalin karfe 10 na safiyar ranar Lahadi, yayin da aka kammala ruwan saman da aka tafka kamar da bakin kwarya kamar yadda mahukuntan yankin suka bayyana. Lardin Guizhou da wasu larduna masu iyaka da shi da ke kudu maso yammacin kasar Sin sun fuskanci mamakon ruwan sama tun daga ranar 18 ga watan Yuni, lamarin da ya haifar da mummunar ambaliyar ruwa, inda lamarin ya fi muni a yankin Rongjiang. Mahukuntan yankin sun raba yankin zuwa kashi bakwai a matsayin wadanda ambaliyar ta fi shafa tare da kwashe mazauna zuwa wasu manyan wurare masu...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnatin Kaduna ta sanya dokar taƙaita zirga-zirga ta tsawon kwana guda a wasu sassan jihar. Wannan na zuwa ne bayan wani hargitsi tsakanin jami’an tsaro da wasu ɓata-gari a yankin Kakuri. Wuraren da dokar ta shafa sun haɗa da Kakuri Bus Stop, Kurmi Gwari, Monday Market, Afaka Road, da Kakuri GRA. Wata sanarwa da Gwamnatin Kaduna ta fitar ta buƙaci mazauna da su kiyaye umarnin wannan doka.
    Adadin mambobin JKS na ci gaba da karuwa, inda rassanta ke ci gaba da ingantuwa. Baya ga haka, sassanta a matakin farko na kara karfi. Wannan na kunshe ne cikin rahoton kididdiga da sashen shirye-shirye na kwamitin kolin jam’iyyar ya fitar yau Litinin, gabanin bikin cika shekaru 104 da kafuwar jam’iyyar. Zuwa karshen 2024, jam’iyyar na da mambobi sama da miliyan 100.27, karuwar kusan miliyan 1.09 kan na shekarar 2023. Zuwa karshen 2024 kuma, JKS na da sassa miliyan 5.25 a matakin farko, karuwar 74,000 idan aka kwatanta da shekarar 2023. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu...
    Rahotanni na cewa an ɗage jana’izar fitaccen ɗan kasuwar nan, Alhaji Aminu Dantata da ya rasu ranar Asabar a ƙasar Hadaɗɗiyar Daular Larabawa. Gwamnatin Nijeriya ce ta sanar da hakan ta bakin Ministan Labarai, Mohammed Idris yayin ganawa da da BBC. APC ta sa ranar taron Majalisar Zartarwa bayan murabus ɗin Ganduje An kashe ubangidan Turji, Kacalla Ɗanbokolo a Zamfara Ministan ya ce an ɗage jana’izar sakamakon rashin isar gawar marigayin a kan lokaci zuwa birnin Madina. A cewarsa, “akwai ƙa’idoji da Gwamnatin Saudiyya ta shimfiɗa kan yadda za a shigar da gawa domin yi mata jana’iza a ƙasar. “Saboda haka yanzu ana nan ana ta cike-ciken takardu tsakanin Gwamnatin Saudiyya da iyalan mamacin,” in ji Ministan. Mohammed Idris ya...
    Gwamnatin Zamfara ta bayyana cewa jami’an sa-kai sun kashe wani riƙaƙƙen ɗan bindiga da ya addabi wasu yankunan jihar mai suna Kacalla Ɗanbokolo. Mai bai wa gwamnan jihar shawara kan harkokin tsaro, Ahmad Manga wanda ya tabbatar da hakan ya bayyana kisan Ɗanbokolo a matsayin gagarumin nasara a yaƙi da matsalar tsaro. “Ɗanbokolo mutum ne da ya fi Bello Turji fitina, ya fi Turji aikata miyagun laifuka, illa kawai shi Turji sunansa da ya karaɗe kafofin yaɗa labarai,” in ji Ahmad Manga. “Mutanensa da aka kashe sun haura 100, saboda haka wannan gagarumar nasara ce a gare mu,” in ji Manga. Ya bayyana cewa Kacalla Ɗanbokolo ya rasa ransa a wata arangama a ƙauyen Kurya, tsakanin jami’an sa-kai na Gwamnatin...
    Jam’iyyar APC mai mulki a Nijeriya ta tsayar da 24 ga watan Yulin bana a matsayin ranar da za ta gudanar da taronta na Majalisar Zartarwa. Mataimakin Sakataren jam’iyyar, Barista Fetus Fuanter ne ya tabbatar wa manema labarai hakan a yau Litinin a Abuja. Magidanci ya kashe matarsa da adda a Yobe Jami’an tsaro sun hana taron kwamitin amintattun PDP Fuanter ya ce kusoshin jam’iyyar za su gana kafin gudanar da taron Majalisar Zartarwar. Taron da za a gudanar shi ne na biyu ta fuskar girma a cikin jerin tarukan da jam’iyya ke zaman yanke shawara da daukar wasu muhimman matakai bayan babban taronta na kasa. Wannan dai na zuwa ne yayin da ake ci gaba cece-kuce tun bayan murabus...
    Hukumomin Iran sun bayyana cewa aƙalla mutum 935 ne suka rasa rayukansu a hare-haren Isra’ila yayin yaƙin kwanaki 12 da ya gudana tsakaninsu da ƙasar. Cikin waɗanda suka mutu sun haɗa har da mata 132 da yara 38, kamar yadda mai magana da yawun Hukumar Shari’a, Asghar Jahangir, ya bayyana a wata sanarwa a ranar Litinin, wacce kamfanin dillancin labarai na Tasnim ya ruwaito. Magidanci ya kashe matarsa da adda a Yobe HOTUNA: Sabon shugaban rikon APC APC ya jagoranci taron Majalisar Gudanarwa A baya, Ma’aikatar Lafiya ta ce adadin wadanda suka mutu sakamakon hare-haren Isra’ila ya kai 606, sannan mutane 5,332 da suka jikkata. Jahangir ya ce hare-haren Isra’ila kan gidan yari na Evin da ke Arewa maso Yammacin...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Yobe ta ƙaddamar da farautar wani mutum mai shekara 55, wanda ake zargin ya kashe matarsa ​​da adda a garin Babbangida da ke Karamar Hukumar Tarmuwa. Jami’in hulda da jama’a na rundunar, Dungus Abdulkarim, a cikin wata sanarwa ya ce wanda wanda ake zargin ya yi wannan aika-aika ne da misalin karfe 11 na safiyar ranar Juma’a, 28 ga watan Yuni a kauyen Koriyel. “Ya aikata hakan ga matarsa ’yar shekaru 40 ta hayar amfani da adda, inda ya kashe ta ya kuma tsere saboda wasu dalilai da har yanzu ba a tantance ba,” in ji sanarwar. Tuni dai ’yan sanda suka fara kokarin cafke wanda ake zargin do ya fuskanci shari’a. A wani labarin kuma,...
    Ya ce a tare da shi a cikin tawagar, akwai Ministan shari’a, Antoni-janar na tarayya, Yarima Lateef Fagbemi, SAN; Ministan yaɗa labarai, Alhaji Mohammed Idris, da ƙaramin Minista a ma’aikatar gidaje, Hon. Yusuf Abdullahi Ata. Tawagar ta kuma haɗa da wasu manyan Malamai, waɗanda suka ƙunshi, Dr Bashir Aliyu Umar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa da Limamin masallacin Ɗantata da ke Abuja, Khalifa Abdullahi Muhammad.   Daga nan ma’aikatan ofishin Jakadancin Nijeriya da ke Jidda, ƙarƙashin Jakada Mu’azzim Ibrahim Nayaya, wanda da ma shi ke kai-kawo wajen shirya yadda jana’iazar za ta gudana, duk sun haɗu da tawagar don gudanar da ita a yau Litini.   Alhaji Ɗantata dai ya rasu ne a Abu Dhabi ta Haɗaɗɗiyar Ɗaular Larabawa...
    Jami’an tsaro sun hana mambobin Kwamitin Amintattu na Jam’iyyar Adwa ta PDP gudanar da taron da suka tsara gudanarwa. A safiyar Litinin din nan ne jami’ai da yawa ne suka kutsa cikin zauren da aka tsara gudanar da taron inda suka bukaci wadanda suka hallara da su watse. Jami’an tsaro da aka jibge a hedikwatar babbar jam’iyyar adawar sun hana mambobin kwamitin amintattu gudanar da taronsu a hedikwatar jam’iyyar. Har zuwa lokacin hada da wannan rahoto, wasu daga cikin ’yan kwamitin amintattun na PDP suna tattaunawa a kan halin da ake ciki. Mun samu rahotannin cewa jami’an sun umurci mambohin su bar ofishin jam’iyar domin ganin ba a gudanar da wani taro a ofishin jam’iyar ba.
    Sabon Mukaddashin Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Ali Bukar Dalori, ya shiga ofis, inda a halin yanzu yake jagorantar taron Kwamitin Gudanarwa na jam’iyyar.
    Tawagar Sarki Muhammadu Sanui II da  Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da Gwamnan Jigawa Umar Namadi sun sauka a Madina domin halartar jana’izar Alhaji Aminu Dantata.
    Tawagar Sarki Muhammadu Sanui II da  Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da Gwamnan Jigawa Umar Namadi sun sauka a Madina domin halartar jana’izar Alhaji Aminu Dantata.
    Gwamnatin kasar Iran ta gargadi kasashen yammacin Asiya kan cewa mai yuwa yaki ya sake barkewa tsakaninta da HKI, akwai tababa kan cewa HKI zata kiyaye budewa juna wuta da ta cimma da kasar Iran. Shafin yanar gizo na labarai ArabNews na kasar Saudiya ya nakalto Manjo Janar Abdulrahman Musawi babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran  yana fadar haka a lokacinda yake zantawa ta wayar tarho da ministan tsaro na kasar Saudiya Yerima Khalid bin Salman, ya kuma kara da cewa HKI ba kasashe abin amincewa ba. Musawi ya ce sojojin JMI a shirye suka su dakile dukkan hare-haren da HKI zata kawo nan gaba. A wani bangare kuma shugaban hukumar makamashin nukliya ta kasa da kasa ta kuma MDD...
    Bayan hare-haren da kungiyoyin yan ta’adda masu iko da kasar Siriya suka kai kan wani Cuci a kasar Siriya jami’an gwamnatin kasar Siriya sun nuna damuwarsu da yiyuwar wadannan kungiyoyi su kawo hare-hare a cikin kasar ta Lebanon musamman a cikin wadan nan kwanaki na makokin Imam Hussain (a). Wani Jami’in gwamnati a kasar ta Lebanon ya fadawa Jaridar da The National ta kasar Amurka kan cewa a makon da ya gabata an kama wani shugaban yan kungiyar yan ta’adda ta ISIS a cikin kasar, tare da zarginsa da shiri hare-hare masu yawa a kasar Lebanon. Kafin haka dai a cikin watan da ya gabata wani dan ta’ada ya tarwatsa kansa a cikin wani coci a birnin Damascus babban birnin...
      Wani matashi a yankin wanda ya bayyana sunansa da Kaase, ya ce ‘yan bindigar a yunkurinsu na farko sun yi kokarin afkawa garin Daudu amma jami’an tsaro suka dakile su, sai suka tafi Tse Asongu da Asha amma al’ummar garuruwan duk sun gudu kafin isowar su. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    JMI ta bawa kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen makamai masu linzami wadanda ake iya cillasu daga cikin tekuna mai suna Ghadr. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya ce makamai mai linzami samfurin Ghadir wanda ake iya cilla shi daga cikin teku ya shiga hannun sojojin kasar Yemen sannan bisa bayanan wasu kasashen yamma hakan wani hatsari ne ga kasashen Amurka da kawayenta a yankin, musamman HKI. Makamin wanda ake iya cillashi daga tekun red sea yana yin barna mai yawa ga makaman makiya.  Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran bata yi wani karin bayani dangane da wannan labarin ba, majiyar ofishin daraktan tsaron kasa na Amurka ta bayyana cewa, JMI tana ta fi ko wace kasa a yankin mallakan...
    Muna sane da wuraren da ake yaki masu taba zuciya: Gaza, Sudan, Ukraine da sauran wurare. Rikicin baya-bayan nan tsakanin Iran da Isra’ila, wani abin tunatarwa ne ga raunin zaman lafiya musamman a yankin Gabas ta Tsakiya mai fama da tashe-tashen hankula.   Duk da haka, a cikin wannan tashin hankali, mun yi nasarar dakile yakin duniya na uku. A wannan zamani na nukiliya, wannan nasara ce da ba za mu taba dauka da wasa ba. Ita ce wacce ta kamata mu kiyaye da karfin kokarinmu.   A cikin shekaru 80 da suka gabata, yawancin ci gaban dan’Adam shi ma yana da tasiri a MDD kai tsaye. Yi la’akari da nasarar da aka samu ta ci gaban karni, wanda kasashe...
      Magoya bayan Kwankwaso, wadanda aka fi sani da Kwankwasiyya, sun yi ikirarin cewa Ganduje ya bai wa mutanen Kano kunya, shi ya sa ya yi murabus.   Shugaban jam’iyyar NNPP na Kano, Hashimu Dungurawa, wanda ya yi magana a madadin magoya bayan Kwankwaso, ya bayyana murabus din Ganduje a matsayin kwaso abin kunya ga Kano.   Ya bayyana cewa, an sami Ganduje ne da son yin almundahana, musamman a lokacin zaben shugabannin jam’iyyar da aka kammala kwanan nan.   Dungurawa ya yi wannan ikirarin ne a ranar Lahadin da ta gabata yayin da yake amsa tambayoyi daga LEADERSHIP game da matakin da jam’iyyar za ta dauka na gaba bayan faruwar wannan lamari.   Ya ce, kafafen yada labarai sun...
    A ranar Litinin din nan za a gudanar da Sallar Jana’izar hamshakin attajiri, Alhaji Aminu Dantata, wanda ya rasu a birnin Dubai na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa. Alhaji Aminu Dantata, wanda ke matsayin kaka ga attajirin Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ya rasu ne bayan rashin lafiya yana da shekaru 94. Aminiya ta ruwaito cewa Majalisar Malaman Jihar Kano, ta gudanar da sallar jana’izar marigayin ba tare da gawar ba a ranar Asabar, a Masallacin Dangi da ke Kundila Kano. Sallar ta samu halartar dubban jama’a da shugabanni daga ciki da wajen Kano. Hakan kuwa ta faru ne bayan iyalan marigayin sun sanar bayan rasuwarsa cewa ya bar wasiyya cewa a idan Allah Ya dauki rayuwarsa, binne shi a birnin Madina...
    Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf, tare da Gwamnan Jigawa, Umar Namadi da kuma Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, sun tafi ƙasar Saudiyya domin halartar jana’izar Alhaji Aminu Ɗantata. Gwamnan ya jagoranci tafiyar ce domin halarta Sallar Jana’izar a Madina ne, bayan rasuwar hamshaƙin attajirin a birnin Dubai da ke ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa a ƙarshen mako. Kakakin Gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawaki tofa ne ya sanar da haka a safiyar Litinin. A ranar Lahadi Aminiya ta ruwaito cewa hukumomin Saudiyya sun amince da yin jana’iza da binne Alhaji Aminu,  Ɗantata a Madina, kamar yadda ya bar wasiyya.
     Majiyar ‘yan sahayoniya ta ce, sai zuwa watan Oktoba ne za a iya kawo karshen lalacewar da matatar man fetur din Haifa ta yi sanadiyyar harin makami mai linzami na Iran. Jaridar “Time Of Isra’il” ta bayyana cewa a tsawon yakin kwanaki 12, Iran ta yi wa Isra’ila mummunan harin mai ciwo da sai yanzu ne sannu a hankali zurfinsa yake bayyana. A jiya Lahadi ne matatar man fetur ta Haifa ta sanar da cewa; Wani karamin sashe nata ne zai fara aiki, saboda hare-haren makamai masu linzami na Iran.  Matatar man fetur din wacce ake kira da sunan : “BAZAN” ta ce sai zuwa wata Oktoba ne ake sa ran cewa za ta koma aiki baki daya. A ranar...
    Janar Abdurrahim Musawi wanda ya tattauna ta wayar tarho ta kwamandan sojojin jamhuriyar  musulunci ta Pakistan, Asim Munir, ya yi jinjina akan mataki na jarunta da Pakistan din ta dauka akan harin da HKI ta kawo wa Iran, haka nan kuma yadda ta nuna goyon bayanta ga Iran. Janar Musawi ya  kuma yi ishara da matsayar gwamnati da al’ummar Pakistan akan ta’addanci na HKI, kamar kuma yadda ya bayyawa kwamandan sojojin kasar ta Pakistan yadda Amurka ta taimakawa HKI a tsawon kwanaki 12 na yakin.  Har ila yau, janar Musawi ya ce; Tare da cewa mun rasa kwamandoji masu girma a farkon harin ta’addancin, sai dai kuma duk da haka, mun hana ‘yan sahayoniyar cimma manufofinsu. A farkon yakin dai,...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Kisa ta hanyar daukar doka a hannu na kara ta’azzara da saka damuwa a zukatan ‘yan Najeriya.   Yayin da wasu ke ganin daukar doka a hannu daidai ne, wasu kuwa na ganin hakan zai cigaba da haifar da rashin doka da oda a kasa. Shin ko me doka ta ce a kan daukar doka a hannu da wasu ‘yan Najeriya su’ke yi? NAJERIYA A YAU: Ko Wadanne Dalilai Ne Ke Hana Mata A Arewa Koyon Ilimin Kimiyya? DAGA LARABA: Ko Najeriya Na Da Kudin Renon Sabbin Jihohi? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan hanyoyin da za a bi don kawo karshen daukar doka a hannu a...
      Da yake jawabi jim kadan kafin tashinsa a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, Gwamna Yusuf ya bayyana marigayi Dantata a matsayin uba ga mutane da yawa, wanda karamcinsa da sadaukarwarsa ya wuce iyaka.   Gwamnan ya jaddada cewa, zuwan tawagar a Madina shaida ce ta matukar mutuntawa da jama’a da gwamnatin jihar Kano suke yi masa na gadon alkairai da ya bari kuma a matsayinsa na dattijon jihar.   Ana sa ran jana’izar da za a yi a birnin Madina, za ta samu halartar wakilan jiha da na tarayya, da ‘yan uwa, ‘yan kasuwa, malaman addinin Islama, da masoya daga sassan duniya baki daya, tare da yin addu’ar Allah ya jikansa. Daga kanmu, magana ta ƙare....
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi Uwargida Oluremi Tinubu wacce ta ba da Naira miliyan 110 ga iyalan marigaya. An kuma yi alƙawarin cewa gwamnati za ta ɗauki nauyin ilimin yaran waɗanda suka rasu da kuma taimaka wa matansu da iyayensu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A ranar 28 ga watan Yuni, 2025, Najeriya ta yi rashin ɗaya daga cikin fitattun ’ya’yanta, Alhaji Aminu Alhassan Dantata bayan ya shafe shekaru 94 a duniya.  Ya rasu a birnin Abu Dhabi na ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) wanda rasuwarsa ta kasance wani babban giɓi a tarihin ci gaban Najeriya, musamman a fannin tattalin arziƙi da tallafa wa marasa ƙarfi. Kebbi: PDP za ta yi haɗaka don ƙalubalantar APC a zaɓen 2027 Mutanen Sakkwato na neman ɗaukin gwamnati game da Bello Turji Wannan rashi na Dantata babban al’amari ne da ya shafi Najeriya da ma Yammacin Afirka baki ɗaya. Aminu Dantata ya kasance mutum mai tasiri a fannonin kasuwanci, hidimar jama’a, addini da ayyukan jin-ƙai. A wannan zamani da...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Fitaccen ɗan kasuwar nan, Alhaji Dahiru Bara’u Mangal, ya bayar da tallafin Naira miliyan 80 don taimaka wa mutane masu fama da cutar mafitsara da matsalar gwaiwa domin yi musu tiyata kyauta. An gudanar da tantance marasa lafiyar a Asibitin Ƙashi na Amadi Rimi kafin a fara aikin tiyatar a ranar Asabar da ta gabata. Kebbi: PDP za ta yi haɗaka don ƙalubalantar APC a zaɓen 2027 Mutanen Sakkwato na neman ɗaukin gwamnati game da Bello Turji Alhaji Kabir Husaini, wanda ke jagorantar aikin, ya bayyana cewa wannan shi ne karo na uku da Mangal ke bayar da irin wannan taimako ga marasa lafiya masu ƙaramin ƙarfi. Ya ce a baya, Mangal ya taimaka wajen yi wa masu lalurar gwaiwa...
    Fitaccen ɗan kasuwar nan, Alhaji Dahiru Bara’u Mangal, ya bayar da tallafin Naira miliyan 80 don taimaka wa mutane masu fama da cutar mafitsara da matsalar gwaiwa domin yi musu tiyata kyauta. An gudanar da tantance marasa lafiyar a Asibitin Ƙashi na Amadi Rimi kafin a fara aikin tiyatar a ranar Asabar da ta gabata. Kebbi: PDP za ta yi haɗaka don ƙalubalantar APC a zaɓen 2027 Mutanen Sakkwato na neman ɗaukin gwamnati game da Bello Turji Alhaji Kabir Husaini, wanda ke jagorantar aikin, ya bayyana cewa wannan shi ne karo na uku da Mangal ke bayar da irin wannan taimako ga marasa lafiya masu ƙaramin ƙarfi. Ya ce a baya, Mangal ya taimaka wajen yi wa masu lalurar gwaiwa...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Al’ummar Iran masu juriya za su tsaya tsayin daka har zuwa digon jini na karshe Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Al’ummar Iran masu juriya za su tsaya tsayin daka har zuwa digon jini na karshe a kan duk wanda ya nemi juya akalarsu. Araqchi ya rubuta a cikin shafinsa na yanar gizo a dandalin sada zumunta na X cewa: “Har yanzu, al’ummar Iran masu girma sun nuna wa duniya karfinsu da juriyarsu.” Ya kara da cewa: Karfin kadawar guguwar masu kishin kasa da suka fito kan tituna domin karrama shuwagabannin soji da suka yi shahada, malamai, masu bincike, da ‘yan kasa, ciki har da mata da kananan yara...
    Shugaban majalisar dokokin jama’ar kasar Mexico Sergio Carlos Gutiérrez, ya bayyana yayin da wakilin babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG ya zanta da shi a kwanakin baya cewa, tunanin raya al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil’adama da shugaba Xi Jinping ya gabatar ya burge shi matuka. Ya ce, an gabatar da tunanin don tattauna yadda sassan kasa da kasa za su zauna tare, da taimakawa juna, da amincewa da bambance-bambance a fannonin tattalin arziki, da yawan mutane, da yankunan kasa a tsakanin kasashen duniya, da sa kaimi ga maida bambance-bambance su zama hanyar dinkewa da juna, da kuma samar da kyakkyawan yanayin zaman rayuwar al’ummun kasa da kasa. Kana yana fatan jama’ar kasashen duniya ciki...
    Manjo Janar Mousawi ya bayyana cewa: Suna shakka da kokwanto kan gaskiyar tsagaita bude wuta shin za ta dore kuwa tsakaninsu da ‘yan sahayoniyya Babban hafsan hafsoshin sojin kasar Iran ya yi gargadin gazawar yarjejeniyar tsagaita bude wuta, yana mai nuni da rashin kwarin gwiwa kan kudurin makiya na cika alkawuran da suka dauka. A wata tattaunawa ta wayar tarho da ministan tsaron kasar Saudiyya Yarima Khalid bin Salman, babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran Manjo Janar Seyyed Abdurrahim Mousawi ya bayyana cewa: Harin da yahudawan sahayoniyya da Amurka suka kaddamar kan kasar Iran ya zo ne duk da kamewa da kai zuciya nesa da Iran take yi, kuma a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa ba na...
    Hasarar da gwamnatin mamayar Isra’ila ta yi a hare-haren da ta kai wa kasar Iran ya kai dala biliyan uku Kafar watsa labaran Bloomberg ta Amurka ta yi kiyasin cewa: Hasarar da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi a yakin da ta yi da Iran ya kai kusan dala biliyan 3, saboda gyaran gine-gine da suka lalace da kuma biyan diyya ga kamfanoni. Kafar ta Bloomberg ta bayyana a cikin wani rahoto cewa: Hasarar da gwamnatin mamayar Isra’ila ta yi na nuni da irin yadda Iran ta kutsa kai cikin tsaron Isra’ila a cikin kimanin makonni biyu da harba makaman masu linzami kan yankunan kasar. Jaridar Amurka ta rawaito wani jami’in gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila yana cewa: “Wannan shi ne...
    Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila sun sake yi wasu sabbin kutse a yankunan Quneitra na kasar Siriya Rahotonni sun bayyana cewa:  Da sanyin safiya ne sojojin mamayar Isra’ila suka kutsa cikin yankunan garin Saida da kuma kauyen Abu Mathra da ke yankin kudancin Quneitra na kasar Siriya.  Wannan ya zo daidai da wani sintiri da sojojin mamayar Isra’ila da ke ci gaba da yi a kauyen Kodna da ke cikin karkarar Quneitra, ba tare da wata arangama ko gargadi daga mahukuntan Siriya ba. Ana ci gaba da yin shiru a hukumance dangane da irin wadannan tsauraran matakan da gwamnatin mamayar Isra’ila ke yi a kan iyakar kasar da tuddan Golan na Siriya da ta mamaye, lamarin da ya sanya ayar...
    Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo da Rwanda sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya bayan shafe shekaru 30 suna rikici Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo da Rwanda sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya, shekaru talatin bayan rikicin da ya barke a shekara ta 1994 da ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane daga bangarorin biyu. An rattaba hannu kan takardar ne a gaban sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio, ministar harkokin wajen Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, Teresa Kayumba, da na Rwanda Olivier Nduhungirehe. Yarjejeniyar da Amurka da Qatar suka wakilci shiga Tsakani ta hada da tanade-tanade kan mutunta yankunan kasa, haramta ayyukan soji, kwance damarar makamai da hadewar kungiyoyin da ba na gwamnati ba, da kuma samar da wani tsari na hadin gwiwa don daidaita...
    Kakakin ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin, ya ce kasarsa na adawa da duk wata yarjejeniyar yafe haraji da Amurka za ta kulla da wata kasa, wadda ka iya illata moriyar Sin, tare da baiwa kasar da aka kulla yarjejeniyar damar samun yafiyar haraji daga Amurka. Kakakin wanda ya bayyana hakan a jiya Asabar, lokacin da yake amsa tambayar da manema labarai suka yi masa, dangane da tattaunawar cinikayya da Amurka ta yi tare da wasu kasashe, ya ce, idan an samu aukuwar irin wannan yanayi, kasar Sin ba za nade hannu ba, za ta dauki matakai na martani domin kare halastattun hakkoki da moriyarta. Jami’in ya kara da cewa, tun watan Afrilun da ya gabata, Amurka ke ta ingiza matakan...
    Wannan ne ma dalilin da yasa wasu ke ganin hadakar za ta iya yin karfi kwarai da gaske, kasancewar ta samu wakilci a sassa daban-daban na wannan kasa. Dalili kuwa shi ne, ‘yansiyasa ne da a baya suka samu damar rike manya-mnyan mukamai, sannan kuma har zuwa yanzu yana da tasiri a fagen siyasar kasar yadda ya kamata. Manya-manyan jiga-jigan da ake gani a cikin wannan sabuwar tafiya ta hadakar jam’iyyar sun hada da: Jagoran adawa a kasar, wanda a baya ya sha yin takarar shugabancin kasa, sannan kuma ko a shekarar 2023 shi ne ya zo na biyu bayan da ya samu kuri’a kusan miliyan bakwai. Alhaji Atiku Abubakar, wanda a yanzu dan jam’iyyar PDP ne; ya kasance guda...
    Jam’iyyar PDP a Jihar Kebbi, ta bayyana shirinta na haɗa kai da sauran jam’iyyu da ƙungiyoyi domin karɓe mulki daga hannun APC a zaɓen 2027, a matakin jiha da kuma tarayya. An bayyana wannan matsaya ne a garin Birnin Kebbi ranar Asabar, yayin wani taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar, inda aka jaddada buƙatar yin sulhu da warware rikicin cikin gida da ke damun PDP. Mutanen Sakkwato na neman ɗaukin gwamnati game da Bello Turji An samu amincewar yi wa Dantata jana’iza a Madina Jigo a jam’iyyar, Ibrahim Mera, ya ce sun amince su haɗa kai da kowa domin a samu nasarar kawar da APC a jihar. “Za mu yi aiki tuƙuru don ganin haɗakar ta yi tasiri. Mun...
    Tashin farashin man fetur a kasuwannin duniya ci-gaban mai hakar rijiya ne ga Nijeriya wadda ke kan gaba wajen fitar da mai ta yadda za ta samu makuddan kudin shiga sai dai gagarumar matsala ce ga ‘yan kasa wadanda za su fuskanci karin mai a cikin gida wanda zai zama silar karin kunci a dalilin farashin abubuwa da dama da zai hau sama.  A cewar masana, Gabas ta Tsakiya da ke samar da akalla kashi 34 na mai a duniya da kashi 18 na gas, gumurzun kasashen biyu ya haddasa farashin danyen mai tashi da kashi 10, yayin da gas ya kara da kashi 7. Haka ma akwai fargabar Isra’ila na iya illata harkokin mai da jigilarsa a mashigar Hormuz...
    Al’ummar Ƙaramar Hukumar Isa da ke Jihar Sakkwato, sun roƙi gwamnatin jihar da ta Tarayya da jami’an tsaro da su kai musu ɗauki kan barazanar da ƙasurgumin ɗan bindiga Bello Turji ke musu. A farkon makon nan ne aka samu labarin cewa Bello Turji ya bai wa mazauna wasu yankuna a Isa wa’adin gina masa ƙaramin dam ko kuma su fuskanci hukunci mai tsanani. Babu wanda zai manta da gudunmawar da Wike ya ba ni — Fubara An samu amincewar yi wa Dantata jana’iza a Madina Har ila yau, ya umarce su da su bar garuruwansu, domin ba ya buƙatar ganinsu a wajen. Wani mazaunin yankin, Wanzami Abubakar Isa, ya bayyana damuwarsa cewa suna zaune garuruwansu kamar baƙi. “Abin takaici...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira ga mazauna wani kauyen dake yankin Nyingchi na jihar Xizang mai cin gashin kai, da su rungumi akidar ‘yan uwantakar kabilarsu, da samar da yanayin gudanar da rayuwa mai kyau. Shugaba Xi ya yi kiran ne cikin wasikar da ya mayar ga mazauna kauyen, wadda a ciki ya bayyana fatansa gare su, bayan da ya ziyarci kauyen cikin watan Yulin shekarar 2021. Ya ce, bayan fahimtar cewa kauyen ya samu sabbin sauye-sauye a shekarun baya-bayan nan, kuma mazaunansa sun samu karin kudaden shiga, ya yi matukar farin ciki. Shugaba Xi ya kara da cewa, yana fatan karkashin manufofin JKS, mazauna kauyen za su gina yankunan kan iyakoki, tare da kyautata rayuwar al’ummunsu...
    Bisa ga sanarwar, wannan wani sashe ne na sabon yunkuri na ba da cikakken ‘yanci ga majalisar kananan hukumomi 774 na kasar nan. Haka kuma a kan gyaran kananan hukumomi, wata kudirin doka da ke neman kirkiro wata hukumar zabe mai zaman kanta ta kananan hukumomi (NALGEC), wanda za ta dunga shiryawa, gudanar da kuma kula da zaben kananan hukumomin, za a kuma gabatar da ita ga ‘yan Nijeriya don yin nazari a taron sauraron jin ra’ayoyin. Wadansu batutuwa da aka fitar a cikin sanarwar da suka hada da kudirin dokoki guda biyu kan tsaro da manufar samar da ‘yansandan jihohi da majalisar tsaro na jihohi don tsara manufofin tsaro na cikin gida a matakin yankuna. “A bangaren gyaran manufifin...
    Masanan sun kuma bayyana cewa, kashi 25 cikin 100 na manya a Nijeriya na dauke da kwayar cutar Sikila. Ana bikin ranar Sikilar ne a kowace shekara, ranar 19 ga Yuni, domin wayar da kan jama’a game da cutar da kuma yadda ake sarrafa ta. Wasu iyayen da suka bayyana irin abubuwa na renon yara masu fama da cutar, sun bayyana cewa; ba don an yaudare su da kuskuren sakamakon gwajin da aka yi musu kafin aure ba, da sun kaucewa matsalolin da suke fuskanta a halin yanzu. Wata uwa mai ‘ya’ya uku daga unguwar Dagbana da ke babban birnin tarayya Abuja, ta bayyana wa LEADERSHIP yadda aka ba ta takardar shaidar cewa; ita da maigidanta za su iya yin...
    Alhazan da suka hada da wakilan hukumar alhazai, jami’an hukumar jin dadin alhazai ta jiha, malamai, da sauran alhazai, sun bayyana jin dadinsu ga gwamnati da hukumar alhazai bisa irin kulawar da suka samu a lokacin aikin hajjin.   Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan isowar mahajjatan, babban daraktan hukumar jin dadin alhazai ta jihar Jigawa, Ahmed Labbo ya bayyana jin dadinsa bisa nasarar da aka samu na dawo da alhazan jihar Jigawa Nijeriya cikin koshin lafiya.   “Mun gode wa Allah da ya dawo mana da alhazan mu lafiya,” in ji Labbo. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga...
    Gwamnatin Saudiyya ta amince a yi jana’iza tare da binne gawar attajirin ɗan kasuwar nan na Kano, Alhaji Aminu Alhassan Dantata. Babban sakataren marigayin, Mustapha Abdullahi Junaid ya ce shirye-shirye sun kammala domin gudanar da jana’iza tare da binne gawar marigayin a garin Madina. A wani saƙo da Mustapha ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya bayyana cewa, “AlhamdulilLah an samu amincewar (hukumomi). “Za a ɗauki Aminu Alhassan Ɗantata daga Abu Dhabi zuwa Madina. Za a yi jana’iza gobe da safe in sha Allah.” Aminiya ta ruwaito cewa a safiyar jiya Asabar ce dai attajirin ɗan kasuwar ya rasu a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa. Amma iyalansa suka jinkirta binne shi domin a cewarsu, suna so ne su cika masa burinsa na...
    Tsohon tauraron ƙungiyoyin Manchester United da Real Madrid, Ruud van Nistelrooy ya ajiye aikinsa na horas da Leicester City bisa fahimtar juna. Wannan na zuwa ne bayan da a ƙarƙashin jagorancinsa ƙungiyar ta yi wasanni 27 da ta gaza taɓuka abin a zo a gani a cikinsu, lamarin da ya kai ta ga faɗawa gasa mai daraja ta biyu a Ingila wato Championship. Wata sanarwa da kungiyar ta fitar, ta ce an cimma matsaya tsakaninta da Van Nistelroy ne bayan tattaunawar da suka yi. A ƙarshen watan Nuwamban da ya gabata, bayan da ta kori Steve Cooper a lokacin da suke matsayi na 16 a gasar Firimiyar bara, Liecester City ta ƙulla yarjejeniya da Van Nistelrooy, kwangilar da ba za...
    “Abin da muke son cimma shi ne, a duk shekara mu tabbatar da ganin mun rubanya yawan madarar da ake samarwa kasar a kasar daga tan miliyan 700,000 zuwa tan miliyan 1.4 daga nan zuwa shekara biyar masu zuwa”, a cewar Ministan. “A Nijeriya akwai sama da Shanu miliyan 20.9, Tumaki sama da miliyan 60, Awakai sama da miliyan 1.4”, in ji shi. Kazalika, Minstan ya kara da cewa; burin shi ne ganin an kara bunkasa tattalin arzikin kasar tare da kuma kara samar da ayyukan yi ga ‘yan kasar. “Ina son fayyace cewa, ba wai batu ne kawai na yawan Shanun da ake da su a kasar nan ba, batu ne na jama’a da samar da ayyukan yi, habaka...
    Masu bincike sun gano cewa sojojin HKI sun kashe Falasdinawa akalla 100,000 tun bayan fara yakin tufanul Aksa a ranar 7 ga watan Octoban shekara 2023. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kan cewa farfesa Michael Spagat da kuma Khalil Shikaki  Bafalasdine masanin masanin fasahar siyasa a Jami’ar London na kasar Burtania suka jagoranci bincike wanda ya kai ga fitar da wannan sakamakon. Labarin ya kara da cewa masu binciken sun kiyasta mutane a gidaje 2000 a birnin  Gaza kadai wanda falasdinawa kimani 10,000 suke rayuwa, sannan suka yi lissafi suka kaim ga wannan sakamakon. Bincike ya kara da cewa daga watan jenerun shekara ta 2025 falasdinawa 75,200 sojojin yahudawan suka kashe da makamai, sannan wasu kimani...
    Majalisar dokokin tsibirin Corsica a yankin Mediterranean, wacce ta kasance jiha ce a kasar Faransa, ta amince da kasar Falasdinunu a matsayin cikakken kasa mai zaman kanta a MDD. Tsirin dai tana neman samun yanci daga kasar faransa, ta amince da samuwar kasar Falasdinu da kuma yin watsi da HKI a matsayin yar mamaya. Kissan kiyashi mai ban tsoro wanda HKI take yi a zirin Gaza ya tada hankalin mutane da dama a duniya kuma ya shara fagen amincwa da kasar Falasdinu mai zaman kanta. Labarin ya kara da cewa Marie-Antoinette Maupertuis shugaban majalisar dokokin kasar ta Corsican ne ya gabatar da bukatar amincewa da kasar Falasdini a majalisar. Ya ce bisa wasu dokokin MDD kasar Falasdinu kasace mai zaman...
    Shugaban majalisar dokokin kasar Iran Muhammad Bakir Qalibof ya bayya shugaban kasar Amurka Donal Trump a matsayin mutum wanda baya iya yin magana guda ya tsaya kanta, mutumtum ne wanda yake tupka da warwara a lokaci guda. Tashar talabijin ta Presstva a nan Tehran ta nakalto kakakin  majalisar dokokin yana fadar haka a zaman majalisar dokokin kasar a jiya Talata. Qalibof ya kara da da cewa kalaman da Trump yake fada na kaskanta shugabannin JMI yana daga cikin yakin kwakwale ne da mutanen kasar Iran. Kuma yakamata ya sani, kuma wadanda suke tare da shi su sani mutanen Iran zasu ci gaba da kare kansu su kuma yaki da wadanda suke shishigi a kan kasarsu. Daga karshen yan siyasan makiya...
    Gwamnatin kasar Faransa ta nawa JMI barazana kan cewa idan bata amince da yarjeniyan da Amurka take so ba to za’a sake dawo da takunkuman MDD a kanta. Kamfanin dillancin labaran tasnim na kasar Iran ya nakalto ministan harkokin wajen kasar Faransa Jean-Noel Barrot yana fadar haka, ya kuma kara da cewa idan Iran ta ki ta rattaba hannu kan yarjeniyar da gwamnatin shugaba Trump yake so kan shirinta na makamashin Nukliya ba, abinda muke buklata kawai shi ne mu aika da wasika kan a dawoda takunkuman tattalin arziki kan kasar Iran, wadanda suka hada da na makamai, kudade, da kuma fasaha wadanda aka dagesu shekaru 10 da suka gabata. Bayanda Amurka ta fice daga yarjeniyar JCPOA a shekara 2018...
    Har ila yau, Maishaddar ya ci gaba da bayyana cewa; dangane da batun da mutane ke yi na cewa, alaka tsakaninsa da jarumi kuma mawaki Umar M. Sharif ta yi tsami, duba da cewa; an daina ganinsa a ci gaban shirin ‘Gidan Sarauta’ da Maishadda ke daukar nauyi, Bashir ya bayyana cewa; wannan magana ko kusa babu kamshin gaskiya a ciki, don ba a ga Umar a shirin ‘Gidan Sarauta’ zango na 4 ba, wannan ba dalili ne da zai sa a yi tunanin ko akwai wata matsala a tsakanina da shi ba, domin kuwa; a duk wani shiri mai dogon zango, akwai lokacin da za a daina ganin jarumi, amma kuma daga baya ya sake bayyana. Bashir ya kara...
    Alhaji Ahmad Manga ya ce, “an ɗauki matakin ne da haɗin gwiwar gwamnatin jiha da gwamnatin tarayya”.   Jami’an CPG na Zamfara sun kuma samu goyon bayan dakarun Civilian JTF na jihar Borno, inda suka ƙaddamar da harin a-yi-ta-ta-ƙare na bazata ga maɓoyar ta Bello Turji.   Gwamnatin jihar Zamfara ta ce artabun na ranar Litinin da haɗin gwiwar jami’an tsaro suka fara da ɗan fashin dajin tamkar buɗe sabuwar ƙofar ci gaba da yaƙarsa ne.   “Alhamdulillahi an tarar da shi har gida nai inda ba a taɓa zuwa ba, kuma ya ga cewa ana iyawa, kuma an isko shi,” inji Ahmad Manga.   Ya ƙara da cewa “an kuma buga wuta, an yi nasarori da dama inda aka...
    Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce za ta yi duk mai yiwuwa domin bankaɗo tushen ɓullar cutar coronavirus da kuma dalilin fantsamarta a sassan duniya. Shugaban hukumar, Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana hakan yana cewa duk da faɗi-tashin ƙwararru, har yanzu ba su da wani cikakken bayani kan abin da ya hana su cimma buri kan binciken da suke gudanarwa. Cutar Coronavirus na cikin cutukan da suka fi gigitar da duniya, wadda ba za’a taɓa mantawa da ita a duniya ba, la’akari da yadda ta yi sanadin mutuwar miliyoyin mutane, da kuma tilasta sanya dokar hana shige da fice, matakin da ya tsayar da duniya cak. An dai fara samun ɓullar cutar a yankin Wuhan na ƙasar China a ƙarshen...
    Sojojin mamayar HKI suna ci gaba da kai hare-hare a yammacin kogin Jordan, inda a safiyar yau lahadi su ka kutsa cikin wani gida a garin Jenin,kamar kuma yadda ‘yan share wuri zauna su ka kutsa gidan wani bafalasdine a kudancin Nablus. Rahotanni da suke fitowa daga Falasdinu suna cewa; an yi taho mu gama a tsakanin Falasdinawa da ‘yan mamaya a garin Tal a kudancin Nablus. A sansanin ‘yan hijira na Jenin sojojin na mamaya sun tarwatsa wani gida na Bafalasdine wanda ya haddasa tashin hayaki da kuma jin kara mai tsanani a sassa mabanbanta na garin Jenin. Haka nan kuma ‘yan mamayar sun yi amfani da motar Buldoza wajen rusa wasu gidaje a sansanin na Jenin. A makon...
    Babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sheikh Na’im Kassim ya bayyana cewa; Babu yadda za a yi Hizbullah ta mika makamanta a cikin wannan lokacin da yaki bai kare ba, kuma HKI  tana cigaba da keta tsagaita wutar yaki. Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya bayyana masu tunani irin wannan da rashin Sanya hankali a cikinsa. A jawabinsa na dararen Muharram a jiya Asabar, babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya kuma ce;  Nauyi ne da ya rataya a wuya gwamantin kasar ta takawa HKI birki akan keta tsagaita da take yi wanda take kai wa fararen hula hare-hare.” Sheikh Na’im Kassim ya kuma ce; Babu yadda za a yi Hizbullah ta ci gaba da Sanya idanu ba tare da iyaka ba, domin...
    Kwamandan rundunar Kudus dake karkashin IRGC Birgediya janar Isma’ila Ka’a’ni ya bayyana cewa; Iran ta samu nasara, kuma nasara ce wacce za ta dore da yardar Allah. Birgediya janar Isma’ila Ka’a’ni wanda ya halarci jana’izar shahidan ta’addancin HKI ya bayyana cewa; Daga yanzu zuwa gaba abinda yake gabanmu shi ne ci gaba da samun nasarori. Haka nan kuma ya ce; Idan har aka samu hadin kai, aka yi aiki tare a tsakanin al’ummar kasa, to komai zai tafi daidai.” Birgediya janar Ka’a’ni ya kuma jinjina wa shahidai, yana mai kara da cewa; tafarkinsu zai cigaba da wanzuwa. A lokacin yakin kwanaki 12 HKI ta rika watsa  cewa ta kashe kwamandan na rundunar Kudus, lamarin da ya tabbata fargaganda ce.
     Kwamitin koli na  tsaron kasa a cikin majalisar shawawar musulunci ta Iran ya bayyana cewa; Saboda yadda hukumar makamashin Nukiliya ta kasa da kasa ( IAEA) take ci gaba da siyasarta na nuna wariya, ci gaba da aiki da ita ba shi da wani alfanu a wurin Iran.  Shugaban kwamitin tsaron kasar a majalisar shawarar musulunci ta Iran Ibrahim Azizi ya bayyana cewa; Karkataccen rahoton da hukumar makamashin Nukiliyar ta kasa da kasa ya gabatar ne ya zama abinda HKI ta fake da shi wajen kawo wa Iran hari na ta’addanci. Azizi ya kara da cewa; Iran ta sha nanata cewa, shirinta na Nukiliya na zaman lafiya ne, kuma yana gudana ne a karkashin yarjejeniyar hana yaduwar makaman Nukiliya. Ibrahim...
    Wani sabon rahoto da Asusun Bayar da Lamuni IMF ya fitar ya ce Nijeriya na mataki na 12 a cikin jerin kasashe mafiya talauci a fadin duniya. IMF ya ce talauci na kara karuwa a cikin kasar da ta dauki shekaru biyu tana kokarin sauya fuskar tattalin arziki, amma kuma take dada fadawa cikin duhu na tattalin arziki. Yadda na hannun daman ’Yar’Adua ya yi tuggun hana ni zama shugaban ƙasa — Jonathan  HOTUNA: Yadda aka yi jana’izar Aminu Ɗantata a Kano Jaridar Cable ta ruwaito cewa, Nijeriya tana mataki na 12 a cikin kasashe mafiya talauci bisa la’akari da karfin tattalin arziki a ma’aunin GDP na Dalar Amurka 807 a bana. Kawo yanzu dai shekaru biyu bayan kaddamar da...
    Yau Asabar, kwamitin kula da raya kasa da aiwatar da gyare-gyare ta kasar Sin (NDRC), ta ce ta ware yuan miliyan 100, kwatankwacin dala miliyan 13.95, kari kan yuan miliyan 100 da ta ware a ranar Larabar da ta gabata, domin taimaka wa ayyukan agaji a kudu maso yammacin Sin. Mummunar ambaliyar ruwa ta sake dawowa a gundumar Rongjiang ta lardin Guizhou dake kudu maso yammacin kasar Sin, lamarin da ya sanya hukumomin wurin sake ayyana matakin koli na tunkarar ambaliya, daga karfe 12:30 na rana a yau. Hukumomi a yankin na kwashe mazauna daga wuraren da lamarin ya shafa. Zuwa karfe 6 na yamma, gundumar ta tsara aikin gaggawa na kwashewa tare da tsugunar da iyalai 11,992 da daidaikun...
    Jiya Jumma’a 27 ga watan Yuni ne, aka kaddamar da wani aikin hadin-gwiwar kafafen yada labaran kasar Sin da kasashen waje daban-daban, mai taken “Ziyara a jihar Xizang don tunkarar zamanantarwa” dake karkashin jagorancin cibiyar watsa labarai ta harsunan Asiya da Afirka ta babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, da ofishin fadakar da al’umma na kwamitin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin reshen jihar Xizang mai cin gashin kai ta kasar, da gidan rediyo da talabijin na jihar, da kamfanin zirga-zirgar jiragen kasa na Qinghai-Xizang na kasar Sin, inda aka gayyaci manyan ’yan jaridu gami da shahararrun masu amfani da shafukan sada zumunta na intanet guda 20, don watsa labarai game da jihar ta Xizang. A...
    Iran ta yi kira da a gudanar da bincike mai zaman kansa kuma a hukumance kan zaluncin ‘yan sahayoniyya da Amurka Mataimakin babban jami’in kula da harkokin kasa da kasa na ma’aikatar shari’a kuma sakataren hukumar kare hakkin bil’adama ta Iran ya yi la’akari da matakin wuce gona da iri na baya-bayan nan da yahudawan sahayoniyya da Amurka suka yi kan cibiyoyin makamashin nukiliya, da kafofin yada labarai, da cibiyoyin kiwon lafiya na Iran, da kuma wuraren zama, gidajen yari da birane da kauyuka, a matsayin misali karara na keta dokokin kasa da kasa da hakkokin bil’adama. A cikin wata wasika da ya aike wa kwamishinan kare hakkin bil-Adama na Majalisar Dinkin Duniya Volker Türk Nasser Seraj mataimakin shugaban hukumar...
    Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Iran ba ta san mika wuya ba, kuma tana rubuta tarihin mutunci da jinin shahidanta A jawabin da ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya yi bayan halartar jana’izar shahidan Quds ya jaddada cewa: Iran ba ta san ma’anar mika wuya ba, yana mai fayyace cewa tarihi zai shaida cewa Iraniyawa sun zubar da jininsu tare da kin ba da kasarsu da mutuncinsu. Araqchi ya bayyana a shafinsa na Instagram cewa: “Duk da zafi da rashi na shahidansu kwatsam, amma tunaninsu yana nan a cikin zukatan masu hankali, da kuma zukatan al’ummomi masu zuwa, kuma suna sane da yin riko da Imani da hanyarsu, kuma za su ci gaba da bin tafarkinsu.”...
    Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya jaddada cewa: Iran za ta ci gaba da tace sinadarin Uranium a cikin kasarta Jakada kuma zaunannen wakilin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya Amir Sa’ed Irawani ya bayyana cewa: Iran tana jaddada matsayinta na cewa dole ne ta gudanar da ayyukan tace sinadarin Uranium a cikin kasarta, yana mai cewa: “Kungiyar masu sa-ido zata iya kasance a Iran, amma ba za ta maye gurbin Shirin Iran na cikin gida ba.” Jakadan Iran na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya Irawani a wata hira da ya yi da tashar talabijin ta Al-Monitor, ya kara da cewa: “Iran ta kasance tana neman mafita ta hanyar lumana don tunkarar matsalolin da ake iya fuskanta...
    Darakta Janar na hukumar kula da makamashin nukiliya ta IAEA ya bayyana cewa: Ba zai iya tabbatar da cewa Iran na kera makamin nukiliya ba! A wata hira da tashar talabijin ta Faransa LCI, Darakta Janar na hukumar kula da makamashin nukiliya ta IAEA Rafael Grossi ya bayyana cewa: Ba zai iya tabbatar da cewa Iran tana kera makamin nukiliya ba. Grossi dai ya fuskanci tambayoyi da kalubale da dama daga mai gabatar da Shirin, kan ko Iran na daf da kera makamin nukiliya? Ya amsa a cikin halin shakku, yana mai cewa a cikin rahoton ya nisanci zargin Iran da kokwarin kera makamin nukiliya domin babu tabbas kan zargin. Da aka tambaye shi ko Iran na kera makamin nukiliya?...
    Wani mummunan hatsari ya afku a Masar inda ‘yan mata 18 suka mutu sakamakon fashewar wata motar dakon mai Wani mummunan hatsarin mota ya afku a kasar Masar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar wasu mata 18 da direban bas a kan hanyarsu ta zuwa gonar inabin domin girbin inabin. Hatsarin ya afku ne a ranar Juma’a a kan hanyar yankin da ke gundumar Menoufia, bayan wata babbar mota ta yi karo da motar bas din da ke dauke da ‘yan matan 18. Dukkansu sun fito ne daga kauye daya, Kafr El-Sanabseh, a gundumar Menoufia, kuma dukkansu ‘yan kasa da shekara 21 ne. Hotunan wannan mummunan hatsarin da aka yi ta yawo da su a shafukan sada zumunta, sun nuna...
    A nata bangare hukumar CAEA ta ce za ta hada hannu da hukumar kula da makamashin nukuliya ta duniya IAEA da sauran abokan hulda daga kasashe masu tasowa, wajen inganta kirkire-kirkire da raya makamashin nukiliya. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Masana da jami’ai a Nijeriya, sun yaba wa ci gaba na a-zo-a-gani da karin kuzarin da ake samu a hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Nijeriya, suna masu bayyana kokarin da aka yi zuwa yanzu a hadin gwiwar bangarorin biyu a tafarkin zamanantar da kansu. Masanan sun bayyana haka ne yayin taro na biyu na bayan taron FOCAC da aka yi ranar Alhamis a Abuja, babban birnin kasar. Cibiyar nazarin dangantakar Sin da Afrika dake Nijeriya ce ta shirya taron mai taken “Hada Hannu Wajen Zamanantar da Sin da Afrika da cimma shirye-shirye 10 na Hadin Gwiwa a Cikin Al’ummar Sin da Afrika mai Makoma ta Bai Daya a Ko da Yaushe.” Da yake jawabi, daraktan cibiyar nazarin Sheriff Ghali...
    Ya ce yana matuƙar daraja lokutan da suka gudanar tare. Ya roƙi Allah ya bai wa iyalan Dantata da Dangote, Masarautar Kano, da al’ummar jihar da ƙasar baki ɗaya haƙuri da juriyar rashin wannan babban mutum. “Allah Ya jikan shi Ya sa Aljannatul Firdaus makomarsa,” in ji Buhari. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Mustapha ya ce idan lokaci ya ƙure kuma ba a samu amincewa daga Madina ba, za su dawo da gawar zuwa Kano domin a yi masa sutura. Don haka, har yanzu ba su yanke shawarar ainihin inda za a binne shi ba. Alhaji Aminu Alhassan Ɗantata ya rasu yana da shekaru 94, kuma mutane da dama sun aike da saƙon ta’aziyyarsu, ciki har da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Alhaji Atiku Abubakar, Rabiu Musa Kwankwaso da wasu shugabanni da dama. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...
    Ya ci gaba da cewa, Hukumar ta NPA, ta yi kasafin da dara haka, na wannan adadin, musaman ganin cewa, ta na burin, kara inganta ayyukanta, yadda za su yi dai-dai, da yadda ake gudanar da ayyukan, a sauran Tashoshin Jiragen Ruwa na duniya. Shugaban Hukumar ya kuma sanar da cewa, a shekarar 2024, Hukumar ta NPA, kudin shigar da ta yi hasashen Tarawa daga na Naira biliyan 865.39, sun karu zuwa Naira biliyan 894.86. “ Wannan ya nuna yadda Hukumar ta NPA, ta mayar da hankali da kuma kara zage Damtse wajen ganin ta Tarawa Gwamnatin Tarayya kudaden shiga, masu yawa,”  A cewar Dantsoho. Shugaban ya kuma bayyana cewa, kudaden shigar da Hukumar ke hasashen Tarawa a shekarar ta...
    Mai magana da yawun hukumar raya hadin-gwiwa da sassan kasa da kasa ta kasar Sin, Li Ming, ya bayyana a jiya Jumma’a cewa, Sin ta riga ta kaddamar da ayyuka kimanin dubu 15 na inganta kwarewar ma’aikata karkashin hadin-gwiwarta da kasashe da kungiyoyin kasa da kasa sama da 180, inda aka horas da kwararrun ma’aikata fiye da dubu 500 a bangarori daban-daban, al’amarin da ya taimaka wa kasa da kasa samun ci gaba. Kana kuma, akwai ’yan kasashen Afirka da dama wadanda suka yi amfani da manufofi da dabarun kawar da talauci da suka koya a kasar Sin, don taimaka wa ayyukan yaki da fatara a kasashensu.   Kakakin ya kara da cewa, tun daga shekaru sama da 70 da...
    Duk ana dora alhakin yadda lamarin cinikin Bayi ya bunkasa kan wani mutum dan asalin kasar Birtaniyya da ake kira da suna,John Hawkins. Hawkins  shi ne mutumin da ya kara daukaka, bunkasa,da zamanan har da lamarin cinikin Bayi”manufa anan yayi  gyare- gyare daga yadda Turawan kasar Fotugal suka fara da barinsa,ya yi masa kwaskwarima,zuwa lamarin kasuwanci mai daraja”. Jiragen ruwa suna tasowa daga Kasar Birtaniya ko kuma Ingila  da Bindigogi, Madubi,da kuma Giya,Jiragen na zuwa wani wurin da ake kira da suna inda ake daukar Bayi a kai su  kasar ko kasashen da suka saye su, yanzu wurin ana kiransa da suna yankin Neja Delta inda daga can ne kuma za ‘a fara tafiya, har sai sun kai inda zasu...
    An yi wa marigayi Alhaji Aminu Ɗantata jana’izar Salatul ‘Ga’ib’ a garin Kano. An yi sallar ne a masallacin Umar bn Khattab da ke kan titin Gyadi-Gyadi. Za a binne Aminu Ɗantata a Madina — Iyalansa Mangu: Gwamnatin Filato ba ta aiko da wakilai don yin ta’aziyya ba — Sarkin Zazzau  Sheikh Ibrahim Khalil, Shugaban Majalisar Malamai na Jihar Kano, tare da Sheikh Ibrahim Aminu Daurawa, ne suka jagoranci sallar. Manyan baƙi da dama sun halarci jana’izar, ciki har da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, mambobin majalisar zartarwa na Jihar Kano, manyan ‘yan kasuwa da wasu mutane. Aminiya ta ruwaito marigayi Alhaji Aminu Dantata, ya rasu a birnin Abu Dhabi, kuma za a birne shi a Madina...
    Albarkacin ranar yaki da miyagun kwayoyi ta kasa da kasa, ofishin dakile miyagun kwayoyi na kasar Sin ya gabatar da rahoton halin da kasar take ciki a wannan bangare, inda alkaluma suka nuna cewa, a shekarar 2024, hukumomi masu alaka sun binciki laifuka masu nasaba da miyagun kwayoyi fiye da dubu 37, da cafke masu aikata laifukan dubu 62, baya ga kama miyagun kwayoyi ton 26.7. Adadin laifuka masu nasaba da miyagun kwayoyi da aka bincika ya ragu da kashi 12.9%, yayin da yawan masu aikata laifukan da aka cafke ya ragu da kashi 5.6% bisa na makamancin lokacin a shekarar 2023. Ban da wannan kuma, Sin ta yi kokarin sauke nauyin dake wuyanta, inda ta shiga a dama da...
    Iyalan marigayi Alhaji Aminu Ɗantata, wanda ya rasu, sun bayyana cewa ya bar wasiyyar cewa a birne shi a Birnin Madina na ƙasar Saudiyya. Majiyoyi daga cikin iyalansa sun bayyana cewa marigayin ya buƙaci a birne shi kusa da uwargidansa a Madina a duk lokacin da ya rasu. Mangu: Gwamnatin Filato ba ta aiko da wakilai don yin ta’aziyya ba — Sarkin Zazzau  ‘An kashe ’ya’yana da mijina da ’yan uwana a hanyar ɗaurin auren ɗana’ A gefe guda kuma, Majalisar Malamai ta Jihar Kano ta yi wa marigayin sallar Ga’ib a Masallacin Aliyu bin Abu Talib da ke unguwar Dangi. Cikin wata sanarwa da ta fitar, majalisar ta bayyana cewa za a yi masa sallar ne duk d gawarsa...
    Mai Martaba Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, ya bayyana cewa Gwamnatin Jihar Filato ba ta aiko da wani wakili zuwa Zariya domin yi wa iyalan waɗanda aka kashe a Ƙaramar Hukumar Mangu a Jihar Filato, ta’aziyya ba. Aminiya ta ruwaito, yadda wasu matasa suka farmaki motar wasu ’yan ɗaurin aure su 31, inda suka kashe 13 daga cikinsu. Aminu Ɗantata: Na roƙi Allah kada Ya ba ni abin da mutane ba za su amfana ba Za a yi wa Aminu Ɗantata Salatul Ga’ib a Kano Sarkin ya bayyana hakan ne lokacin da jagoran shugabannin addinai, Tsohon Ministan Matasa da Wasanni Solomon Dalung, ya jagoranci wata tawaga zuwa fadarsa domin yin ta’aziyya. Sarkin ya gode wa tawagar bisa wannan ziyara,...
    Rundunar sojin Isra’ila ta tabbatar da wani hari da fararen hula’yan ’yan ƙasar suka kai wa sojojinta. An kai wa dakarun rundunar sojojin ko-ta-kwana na Isra’ila hari ne a yankin Gaɓar Yammacin Kogin Jordan. Yahudawa ’yan share wuri zauna suka kai wa sojojin na Isra’ila harin ne a yayin da sojojin ke aiwatar da wani samamen tare da yin kame a yankin, mai suna Kafr Malek. Sanarwar da rundunar ta fitar ta ce, “fararen hula ’yan Isra’ila sun yi wa jami’an ruwan duwatsu tare da cin zarafin sojojin ta jiki da ta baki, ciki har da kwamandan rundunar.” Yunwa ta kashe yara 66 a Gaza ‘An kashe ’ya’yana da mijina da ’yan uwana a hanyar ɗaurin auren ɗana’ Yadda aka...
    Nasarar da kungiya ta samu a matakin rukuni za a ba ta Dala miliyan biyu, canjaras kuma miliyan daya, wadda ta cinye kofin kuma za ta samu ladan Dala miliyan 40. Ganin yadda kungiyoyin Turai suka mamaye gasar, Afirka na fatan samun karin dama a nan gaba, ma’ana a Karara nahiyar Afirka yawan kungiyoyin da za su dinga wakiltar ta. Wasu na fatan kungiyoyin Afirka da ke cikin gasar za su ja hankalin duniya zuwa nahiyar ko da kuwa gasarta ta zakaru ba ta iya yin hakan ba, da kuma kawo musu kudi idan aka kwatanta da takwarorinsu. Sabuwar gasar African Footbal League da hukumar CAF ta kaddamar a 2023 ba a sake yin ta ba, duk da irin rigingimun...
    – Lokacin: Asabar 2:00 na rana. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Har yanzu dai gwamnatin Syriya ba ta komai ba game da barna da hasarar rayuka da makamai da kuma jiragen da ake amfani da su da ta sararin samaniyarta ke haifarwa ba. Shafin Intanet na kafar Enab na kasar Syria ya wallafa wani labari a ranar 15 ga watan Yuni game da shirun da gwamnatin Syriya ta yi kan karakainar da jiragen yaki da makamai masu linzami ke yi a sararin samaniyar kasar. Wani mai sharhi ya fada wa Enab cewa gwamnatin Syriya ta yanke shawarar tsayawa tsakiya kan lamarin ne kasancewar tana daukar Isra’ila da Iran a matsayin abokan gabarta. Ya ce: “Babu daya daga cikinsu da za ka bayyana shi a matsayin abokin al’ummar Syriya, kuma dukkaninsu sun...
    Mahaifin angon da ’yan uwan angon na jini da danginsa na daga cikin mutane 13 da aka yi wa kisan gilla a hanyar ɗaurin auren ango, inda aka ƙona gawarwarkin wasunsu a cikin motar da ta ɗauko su, a yankin Mangun da ke ƙaramar Hukumar Mangu ta Jihar Filato. Mahaifiyar angon, Malama Faji Sani da ke zaune a ƙauyen ɗan Bami Anguwar Rimi a ƙaramar Hukumar Kudan ta Jihar Kaduna, ta shaida wa Aminiya cewa mijinta da ’ya’yanta biyu da ƙannenta biyu da kuma kishiyarta, na cikin mutanen da aka kashe su a harin na ranar Juma’a da dare. Ta ce mijin nata, Alhaji Sani, wanda da shi suka dogara, ya rasu ya bar ’ya’ya 13 da jikoki da dama....
    Iran ta gudanar da gagarumin jana’izar tare da karramawq ga kwamandojinta da masana kimiyyar nukiliya da wasu ’yan kasar da Isra’ila ta kashe a yankin kwana 12 da aka gwabza a tsakanin ƙasashen. Iran ta shirya gagarumin jana’izar a ƙwaryar birnin Tehran kwana huɗu bayan Isra’ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a yaƙin da ɓangarorin biyu ke iƙirarin nasara a yaƙin da aka fara ranar 13 ga Yuni, 2025. A safiyar Asabar daruruwan dubban mutane ne suka fito ɗauke da tutocin ƙasar suna wake-waken jinjina domin karrama kwamandojin da suka kwanta dama a wurin jana’izar. Mutanen sun kuma riƙa daga hotunan mamatan a matsayin waɗanda suka yi mutuwar shahada, a yayin da suke la’antar Isra’ila da Amurka. Daga cikin...