Sayyed al-Houthi: Mun shirya dawowa fagen daga idan Isra’ila ta ci gaba da kisan kiyashi a Gaza
Published: 22nd, October 2025 GMT
A cikin jawabin da ya gabatar a wannan Talata da aka nuna kai tsaye a taron jana’izar babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Yemen Laftanar Janar Mohammed al-Ghamari, Sayyed Abdulmalik al-Houthi ya jaddada cewa, kasar Yemen za ta ci gaba da kasancewa cikin shirin komowa ga ayyukan soji idan Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta koma kisan kare dangi, da kuma ci gaba da killace yankin zirin Gaza.
Sayyed al-Houthi ya yi ishara da irin babban gangami na dubban daruruwan mutane da suka taru a wurin jana’izar shahid al-Ghamari a matsayin abin da ke nuni da tsayin daka na al’ummar Yemen a kan manufofinsu.
Sayyed al-Houthi ya kuma yi nuni da cewa al’ummar Yemen sun gamsu da matsayi mai Daraja da suke a kansa, na yin sadaukarwa domin taimakon ‘yan uwansu musulmi da ake zalunta a Gaza, inda ya bayyana arangamar da Yemen ta yi da yahudawan sahyuniya a cikin shekaru biyu da cewa sadaukarwa saboda Allah da kuma ‘yan adamtaka, da kuma kin mika wuya ga zaluncin masu grman kai na duniya.
Ya ce wadanda suka mika wuya ga mnufofin yahudawa a yankin, ba su daukar komai face kaskanci da kunya a idon duniya, sabanin matsayar al’ummar Yemen da sauran bangarori masu gwagwarmaya domin taimakon al’ummar Falastinu a yankin, wadanda suka Fifita rayuwa a cikin karama da ‘yanci, ko da kuwa hakan zai kaisu ga matsayi na shahada a kan tafarkin gaskiya.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Nigeria: “Yan Sanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar Neman Sakin Jagoran ‘Yan Awaren Biafara October 21, 2025 HKI Tana Ci Gaba Da Hana Wa Falasdinawa Abinci October 21, 2025 An Yi Fashi Da Makami A Gidan Adana Kayan Tarihin ” Louvre” Na Kasar Faransa October 21, 2025 Yemen : An yi jana’izar babban hafsan sojin kasar Shahid al-Ghamari a Sana’a October 21, 2025 Iran da Iraki sun bukaci duniya da ta dakatar da kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a Gaza October 21, 2025 Equatorial Guinea ta zargi Faransa da karan-tsaye wa zaman lafiya a kasar October 21, 2025 Faransa : Sarkozy, ya fara zaman gidan yari na shekara 5 October 21, 2025 Gaza : Falasdinawa 97 sojin Isra’ila suka kashe tun bayan cimma yarjejeniya October 21, 2025 Iran Da Faransa Zasu Yi Musayar Fursinoni, Esfandiari Tana Daga Cikin Wacce Za’a Sallama October 21, 2025 Gaza: Isra’ila Ta Kashe Falasdinawa 57 A Cikin Sa’o’i 24 Da Suka Gabata October 21, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Jiragen Haramtacciyar Kasar Isra’ila Sun Kai Hare-hare A Kudancin Lebanon
Rahotanni daga kasar Lebanon sun ambaci cewa da marecen yau jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai hare-hare a garuruwan Mahruna,jibaa, Bar-ishit da Majadil dake kudancin Lebanon. Hare-haren sun rusa gidaje da dama na garuruwan da su ka kai wa harin.
Wannan harin dai yana faruwa ne kwana daya bayan da Lebanon ta aike da wakili a cikin kwamitin ttataunawa da ‘yan sahayoniyar da tsohon jakadan kasar Simon Karam yake wakiltarta.
Tashar talabijin din almanar ta ambato ofishin karamar hukumar garin Mahrunah tana yin tir da wannan harin wanda ya rusa wani gida na fararen hula a tsakiyar unguwa.
Bayanin ya ci gaba da cewa; Kai hari a tsakiyar unguwar fararen hula keta dokokin ‘yan adamtaka na duniya. Kuma abinda ‘yan sahayoniyar suke yi jefa tsoro ne a cikin zukatan mutanen yankin.
Haka nan kuma ya ce; Abokan gaba ba za su iya yin nasarar kashe gwiwar mutanen garin ba,ko kuma su yi tasiri akan jajurcewarsu.
A can Nakura ma, wani karamin jirgin sama maras matuki ya jefa bom a kusa da masu kiwon kifi a gabar ruwa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka An Kira Yi Gwamnatin Canada Da Ta Kama Olmert Da Livini Na “Isra’ila December 4, 2025 An Kashe Shugaban ‘Yan Dabar Gaza “Abu Shabab” Da Isra’ila Ke Goyon Baya December 4, 2025 Iran : Jagora Ya Bayyana Ra’ayin Musulunci Kan Hakkokin Mata December 4, 2025 Taron IMO : Tehran Ta Yi Watsi Da Zarge-zargen Isra’ila Marasa Tushe December 4, 2025 MDD ta nemi a kawo karshen mamayar Isra’ila a Falasdinu da kuma Tuddan Golan December 4, 2025 Rundunar Ruwa ta IRGC na Gudanar Da Atisayen Soja a Tekun Fasha December 4, 2025 Dan wasan Taekwando Na kasar Iran Ya Samua Lambar Yabo Ta Zinariya December 4, 2025 Hamas Za ta Mikawa Isra’ila Samfurin Da Aka Samu A Karkashin Burabutsai A Gaza December 4, 2025 Iran: Tsaron Yankin Tekun Fasha Jan Layi Ne Da Za’a Fuskanci Mayar Da Martani Adan Aka Taba Shi December 4, 2025 Kungiyoyin Kare Hakkin Dan Adam Sun Kira Ga Kasar Kanada Ta Kama Olmert Da Livni December 4, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci