Kano Pillars Ta Dakatar Da Babban Kocinta Bisa Rashin Katabus A Kakar Wasa Ta NPFL
Published: 20th, October 2025 GMT
Hukumar gudanarwa ta ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars ta sanar da dakatar da Mai Ba da Shawara a harkokin koyarwa na ƙungiyar, Ogenyi Evans, da Babban Koci, Ahmed Garba (Yaro Yaro), saboda rashin gamsasshen sakamako da ƙungiyar ke samu a farkon kakar wasa ta 2025/2026 Nigeria Premier Football League (NPFL).
A cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, ta bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne sakamakon jerin sakamakon wasanni marasa kyau da suka gaza cika tsammanin masoya da masu ruwa da tsaki a ƙungiyar.
Ya yanzu dai, kungiyar ta Sai Masu Gida ta buga wasanni takwas, inda ta samu nasara a biyu kacal, ta kuma tashi kunnen doki a wasanni 2, sannan suka sha kaye a wasanni huɗu — sakamakon da ƙungiyar ta bayyana a matsayin abin da bai dace da ƙungiya mai irin wannan matsayi ba.
A halin da ake, tsohon kyaftin ɗin ƙungiyar kuma mataimakin koci, Gambo Muhammad, zai jagoranci harkokin koyarwa tare da kocin masu tsaron raga, Suleiman Shuaibu, yayin da Coach Garzali Muhammad (Kusa) daga Junior Pillars zai shiga cikin tawagar masu koyarwa ta wucin gadi har sai an bayar da umarni na gaba.
Hukumar ta kuma jaddada aniyarta ta sake gina ƙungiyar domin samun sakamako mafi kyau da kuma ci gaba da kare martabar ta a matsayin ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa a Najeriya.
Daga Khadijah Aliyu
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Kano Pillars a ƙungiyar
এছাড়াও পড়ুন:
Tawagar Sin Ta Dindindin A Hukumar Fao Ta Fara Aiki
ShareTweetSendShare MASU ALAKA