Aminiya:
2025-12-04@20:12:35 GMT

Kano Pillars ta dakatar da Kocinta

Published: 20th, October 2025 GMT

Hukumar gudanarwar Kungiyar Kwallon kafa ta Kano Pillars ta dakatar da Babban Kocinta Ahmed Garba Yaro Yaro da bai ba da shawara ga  Kocin, Ogenyi Evans, nan take.

Ta kuma nada tsohon kyaftin kuma Mataimakin Koci, Gambo Muhammad nan take, ya jagoranci lamuran fasaha na ƙungiyar. Mai horar da masu tsaron raga, Suleiman Shuaibu, zai taimaka masa, yayin da Koci Garzali Muhammad (Kusa) daga Junior Pillars zai ba da ƙarin goyon baya har sai an fitar da sabbin umarni.

Kungiyar ta dauki wannan mataki ne bayan abin da ta kira “rashin tagomashinta” a Gasar Firimiyar Najeriya (NPFL) ta 2025/2026 da ake ci gaba da yi.

Sanarwa da kulob ɗin ta fitar, hukumar gudanarwar ta ce an ɗauki matakin ne bayan nazarin yadda ƙungiyar ta yi rashin nasara a wasannin ta na baya-bayan nan.

Ta ce “Yanzu haka, ’yan wasan sun buga wasanni takwas, amma nasara biyu kacal suka samu a ciki, sun yi canjaras biyu, sannan kuma an doke su a wasanni huɗu.”

An kama ɗan uwan Nnamdi Kanu da lauyansa —Sowore Juyin mulki: Ana zargin tsohon gwamna da ɗaukar nauyin sojojin Najeriya

Kulob ɗin, wanda yana ɗaya daga cikin ƙungiyoyin da suka fi rawar gani a tarihin ƙwallon ƙafa a Najeriya, yana fama da rashin daidaituwa a wannan kakar, abin da ke tayar da hankalin magoya baya da masu ruwa da tsaki kan jagorancin ƙungiyar.

Sanarwar ta tabbatar wa magoya baya cewa hukumar gudanarwar ta ci gaba da jajircewa wajen dawo da ƙungiyar kan turba da kuma dawo da dabi’ar ta ta samun nasara.

Kano Pillars, wadda aka fi sani da ‘Sai Masu Gida’, a halin yanzu tana can ƙasan teburin gasar ta NPFL, kuma tana fatan samun canji mai kyau yayin da kakar ke ci gaba.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: dakatar da koci Kano Pillars

এছাড়াও পড়ুন:

Tsaro: Gwamnonin Arewa na shirin dakatar da haƙar ma’adinai

Gwamnonin Arewaci, na shirin dakatar da haƙar ma’adinai a wasu yankuna da ake fama da matsalar tsaro, domin daƙile ayyukan ’yan bindiga da sauran ƙungiyoyin ta’addanci.

Wannan batu ya fito ne daga taron haɗin gwiwa na Gwamnonin Arewa da Majalisar Sarakunan Gargajiya da aka yi a Kaduna daga 1 zuwa 2 ga watan Disamba, 2025.

’Yan sanda sun kama mutum 28 kan zargin lalata mata da yara a Yobe Tsaro: Gwamnatin Kano za ta fara amfani da jirage marasa matuƙa a iyakokinta

Shugaban ƙungiyar gwamnonin, Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na Jihar Gombe, ya ce lamarin tsaro ya kai wani mataki da ke buƙatar ɗaukar matakin gaggawa.

Ya bayyana cewa wuraren haƙar ma’adinai sun zama mafakar ’yan bindiga, masu garkuwa da mutane da ƙungiyoyin ta’addanci, inda suke tara kuɗi da shirya hare-hare.

Ya ce ’yan ta’adda suna amfani da waɗannan wurare wajen ɓoye makamai da tsara kai hare-hare.

“Dkatar da haƙar ma’adinai ne zai kawo zaman lafiya, dole mu ɗauki wannan mataki.”

Gwamnan ya ce Arewa na fuskantar matsaloli da dama; garkuwa da mutane, Boko Haram, rikice-rikicen karkara da talauci, wanda ke ƙara dagula tsaron yankin.

Ya ce dole a inganta tsaro tare da magance tushen matsalolin.

Ya kuma goyi bayan tsarin ’yan sandan jihohi, inda ya bayyana cewa bai kamata siyasa ta hana ɗaukar matakan tsaro ba.

Taron ya buƙaci Sarakunan Gargajiya da malamai su ƙara ƙoƙarin wanzar da zaman lafiya da fahimtar juna.

Hakazalika, an tattauna yawan yaran da ba sa zuwa makaranta da buƙatar inganta ilimi da sauran ɓangarorin tattalin arziƙi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Kashe Shugaban ‘Yan Dabar Gaza “Abu Shabab” Da Isra’ila Ke Goyon Baya
  • NAPTIP ta daƙile yunƙurin safarar mutum 7 daga Kano zuwa Saudiyya
  • Jirgin fadar shugaban ƙasa ya ƙi sayuwa wata 5 bayan saka shi a kasuwa
  • Tsaro: Gwamnonin Arewa na shirin dakatar da haƙar ma’adinai
  • Kungiyar Guinness Ta Rigistan Ayyukan Bajinta Ta Duniya Ta Dakatar Da Karban Daga HKI
  • Tsaro: Gwamnatin Kano za ta fara amfani da jirage marasa matuƙa a iyakokinta
  • DAGA LARABA: Kalubalen Dake Gaban Janar Christopher Musa A Matsayin Ministan Tsaro
  • Shugaba Pizishkiyan:  Goyon Bayan Al’ummar Iran Ga Tsarin Musulunci Ne Ya Hana Abokan Gaba Cimma Manufar
  • Tinubu ya gana da Janar Christopher Musa bayan Ministan Tsaro ya yi murabus
  • Tinubu ya gana da Janar Christopher CG Musa bayan Ministan Tsaro ya yi murabus