HOTUNA: NDLEA ta kama hodar iblis da aka ɓoye a cikin carbi da takalma
Published: 16th, March 2025 GMT
Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta NDLEA sun cafke wasu mutane da hodar iblis da suka ɓoye a cikin carbi da kuma takalma.
A cewar hukumar, an cafke ababen zargin ne yayin da suke ƙoƙarin safarar hodar iblis ɗin zuwa ƙasa mai tsarki.
Femi Babafemi, darektan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na NDLEA ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa tare da hotunan hodar iblis ɗin da aka kama.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: hodar iblis hodar iblis
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan sanda sun kama wani mutum da jabun kuɗi a Gombe
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta kama wani mutum, mai shekaru 35 daga ƙauyen Kunji da ke Kwadon, bisa zargin mallakar jabun kuɗi.
Kakakin ’yan sandan jihar, DSP Buhari Abdullahi, ya ce an kama Kawu ne a ranar 28 ga watan Yuni, 2025, a ofishin ’yan sanda na Lawanti, sannan aka kai shi ofishin Amada domin ci gaba da bincike.
Ambaliya: Zulum ya bada umarnin tallafa wa mutanen Damboa da Askira-Uba Majalisar Dokokin Filato ta zaɓi sabon shugabaYa ce an samu dalar Amurka 1,000 da ake zargin na bogi ne (kimanin Naira miliyan 1.5), da kuma Naira 10,000 a cikin kayansa.
A yayin bincike, Kawu ya amsa cewa kuɗin na wani mutum ne.
’Yan sanda sun ce suna ci gaba da bincike domin gano wanda ya ba shi kuɗin.
Rundunar ta kuma ce za ta ci gaba da yaƙar masu ta’ammali da jabun kuɗi tare da tabbatar da cewa za ta sanar da jama’a yadda binciken ke tafiya.