Assalamu alaikum masu sauraro sharhin bayan labarammu zai yi magana dangane da ‘Atisayen sojojin ruwa mai taken (“damarar tsaro na shekara ta 2025”) wandake ke gudana a nan Iran. Wanda ni tahir amin zan karanta.

////.. A ranar litinin da ta gabata ce sojojin ruwa na kasashen China, Rasha da kuma Iran suka fara atisayen sojojin ruwa na hadin giwan kasashen uku, wanda suka sanya masa suna :damarar tsaro na shekara ta 2025″ wanda kuma ke gudana a halin yanzu a arewacin tekun Indiya da ke kudu maso gabacin kasar Iran da tekun farisa da kuma tekun Omman.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa atisayen wanda zai dauki kwanaki uku cur ana gudanar da shi, zai maida hankali wajen al-amuran da suka shafi tsaron ruwa na yankuna daban-daban a inda wadanda kasashe suke kula da su.

Labarin ya kara da cewa a yau talata sojojin kasashen uku sun gudanar da wani bangare na atisayen. Rear admiral Mostafa Tajeddine mataimakin kwamandan gudanarwa na sojojin Ruwa na kasar Iran ne ya bayyana haka. Ya kuma kara da cewa wannan bangaren daukar hotuna na atisayen ya kammala kamar yadda aka tsara.

Tajuddine ya kara da cewa ana daukar hotunan yadda atisayen ke gudana daga jirgin ruwa wanda yake kula da hakan daga cikin jiragen ruwan yaki sojojin ruwa na rundunar IRGC. Ya kuma ce JMI tana da shirin kula da zaman lafiya a yankunan ruwa daban –daban a kasashe yankin da kuma na sauran kasashen duniya.

Shi ma a jawabinsa Rear admiral Shahram Irani, babban kwamandan sojojin Ruwa na JMI ya bayyana cewa, yayi watsi da zancen shugaban kasar Amurka Donal Trump dangane da wannan atisayen na cewa, Amurka tafi taron kasashen Iran Rasha da kuma China, ya kuma bayyana cewa wannan kalaman ‘rudu ne’ kawai wanda shugaban ya shiga.

Kafin haka dai shugaban  kasar na Amurka yace bai damu da atisayen kasashen uku suka yi a tekun faraisa, don ya san Amurka ta fi su karfi gaba daya. Irani ya ce manufar kasashen uku a wannan atisayen, mai suna ‘damarar tsaro na shekara ta 2025″ ita ce tabbatar da tsaro a yankin da kuma duniya, sabanin abinda Amurka take yi na samar da tashe-tashen hankula a cikinta.

Ya kuma kara da cewa, yakama ta gwamnatin Amurka ta sani, yawan kasashen da suke da karfin sojojin ruwa a duniya sun kara, kuma suna gwada karfinsu a wurare da dama a yankin Asiya da kuma wasu wurare a duniya. Ya ce kasashen kungiyar Shanghai da Brics da dama suna da karfin tabbatar da zaman lafiya a yankuna da dama a duniya. Suna da karfin ganin harkokin tattalin arziki na yankunansu da kuma kasashensu suna gudana da kyau.

Ya ce wasu kasashe banda wadannan uku, suna shirye-shiryen hadewa da wannan atisayen nan gaba. Wannan dai shi ne atisay karo na 7th wadanda wadannan kasashe uku China Iran da kuma Rasha, wanda yake karfafa kwarewarsu a tabbatar da tsaro a cikin ruwayen kasashen yankin, har’ila yau akwai wasu kasashe da dama daga yankin da kuma wasu kasashe daga nesa suna a matsayin masu kallo a wannan atisayen.

Banda haka wadannan atisayen zai hana kan wadannan kasashe don cimma manufa guda ta samar da zaman lafiya a dukkan hanyoyin zirga zirgan kasuwanci da hulda ta cikin ruwa a yankin da kuma duniya.

A cikin yan kwanakin nan ne shugaban kasar Amurka take barazanar kaiwa cibiyoyin nukliya na kasar Iran, don hanata, abinda ya kira makamin Nkliya. Ko kuma iran ta amince ta zauna da Amurka ita kadai don ta fada mata abinda zata yi, da abinda ba zatayi ba a fagen makamashin nukliya. Wanda Iran tace ba zata taba zama da Amurka don tattauna batun shirinta na makamashin nukliya ba.

Tun kafin ya sake dawowa kan kujerar shugabancin kasar Amurka, a karo na biyu, shugaban yake barzanar zai tursaswa iran ta amince don tattaunawa da ita kan shirinta na makamashin nukliya.

Amma idan ta ki amincewa zai yi amfani da karfin don wargaza shirinta na makamshin nukliya don ba zata amince iran ta mallaka makaman Nukliya ba.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: a wannan atisayen sojojin ruwa na yankin da kuma kara da cewa

এছাড়াও পড়ুন:

Abubuwan Da Na Gani A Yankin ‘Hero Bay’ Da Ke Cikin Kasar China

kauyuka a China, ana nufin yankunan da suka bunkasa, wadanda suka kasance, sun yi kamance-ceniya da sun anguwanin GRA a Nijeriya da kuma a nahiyar Afirka.

 

A yankin na Hero Bay, an tanadar da tituna inganciyyar wutar lantarki, tsaftatattacen ruwan sha da kuma kafar Inernet

 

Akwai manyan bene masu tsawo a yankin, wadanda tsawonsu ya dara na bene mai hawa biyar, inda kuma aka tanadar wa da yankin, ababen more rayuwa.

 

kananan hukumomi ne, suka gina wadannan matsugunnan, musamman donin a dakile barazanar kwararowa alumma daga kauye, zuwa cikin birane.

 

A gwajin da aka yi na yankunan da su habaka sosai a China, ana buga misali da Hero Bay kan yadda gwamnati ke bai wa alumma kwarin guiwa na su ci gaba da zama a yankunan da suke, musamman ta hayar samar masu tallafin kudi da gidaje.

 

Wannan dabarun, baya ga kara bunkasa fannin aikin noma a kauyukan, sun kuma kara habaka fannin fasaha kimiyya a kauyukan da kuma kara bunkasa tattalin arzikin kasar.

 

Wani mai gudanar da aikin bincike a cibiyar yin bincike a fannin fasaha ta kasar Wang Yongzhong, ya alakanta kauyukan a matsayin guraren da suka yi fice a duniya, da makuntan kasar, suka samar masu da ababen more rayuwa.

 

Samar da hanyoyi na daga cikin ayyukan da gwamnatin China, ke bai wa mahimmanci, musamman domin a samar da damar gudanar da zirga-zirgar gudanar da ayyukan yau da kullum, a cikin sauki.

 

Samar da yankin na Hero Bay, na daga cikin babban misalin mayar da kan gwamnatin kasar, na dakile kwararowar mazauna a karkara, musamman a tsakanin matasa zuwa cikin birane.

 

Wasu biranen sun kasance cike suke da manyan rukunonin gidage, amma wannan sabanin haka ne, a Hero Bay, duba da yadda aka samar da gidaje, ga ‘yan kauyen da ke da ra’ayin zama a cikinsu, wanda kuma za su iya habaka kasuwancinsu da gudanar da aikin noma, tare da kuma samar da makarantu, Asibiti da jami’an tsaro da sauransu.

 

Daura da Hero Bay, akwai masana’antar kera motoci, wadda kuma ke samar da ayyukan yi ga mazauna yankin, ta hanyar goyon bayan ayyuakn shirye-shirye na kananan hukumomi.

 

A cewar Mataimakin Daraktan shirin bayar da horo China, Mista Wu Hao, gwamnatin kasar ta samar da wadannan ababen more rayuwar ne, domin a dakile kwararar mazauna kauyukan zuwa cikin biranen kasar.

 

daya daga cikin mazauna yankin Madam Yang Baozhen, ta tabbatar da wannan maganar ta Mista Wu Hao, inda ta ce, ana karfafawa, musamman matasa guiwa domin su shiga a dama da su, a fannin hada-hadar kasuwancin yankin, wanda hakan ka samar da kauyukan kudaden shiga.

 

Kazalika, mazauna kauyukan da ba su da bukatar shiga fannin noma ko yin aiki a masana’anta, su kan bude gidajen sayar da abinci ko kuma yin wasu kanannan sana’oi.

 

A kauykan, ana kuma bayar da ilimin zamani kyauta, tun daga matakin Firamare zuwa na Sakandare.

 

Bisa tsarin mallakar filaye a kauyukan ba za ka sayi fili ko kuma ka sayar da shi ba, amma za ka iya bayar da jinginarsa, har zuwa tsawon shekaru 50 zuwa 70, wanda daga baya, za ka sabunta jinginar.

 

A cewar wani mai zagaya wa masu yawon bude ido, “A kasar duk wani fili da ke kasar, mallakar gwamnatin kasar ne, wadda kuma kowanne fili, an tsara abinda za a yi a kansa,”

 

A yayin da ake ci gaba da tattauna wa kan batun bunkasa nahiyar Afrika ciki har da Nijeriya, akwai bukatar a rungumi irin wannan tsarin na China, duba da cewa, abu ne, da kwalliya za ta biya kudin Sabulu.

 

Kazalika, ta hanyarin yin hadaka da tsarin samar da hanyoyi na BRI na China hakan zai samar da wata ingantacciyar hadaka ga kasashe masu tasowa da kuma ga cibiyar bunkasa kasuwanci ta kasa da kasa ta AIBO da ke a karkashin ikon ma’aikatar bunkasa kasuwanci ta China, musamman wajen bayar da horo kan dabarun zamani na bunkasa kasuwanci.

 

Hakazalika, ta hanyar rungumar wannan tsarin China, Afirka za ta iya magance yawan kwararowar mazauna karkara, zuwa cikin birane, wanda hakan zai kuma taimaka wa kasashen da ke a Afrika, wajen kara bunkasa tattalin arzikinsu da samar wa da ‘yan Afrika, alkibla mai dorewa.

 

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Araghchi : Za’ayi Tattaunawar Iran da Amurka ta gaba a Rome bayan taron E3
  • Iran ta sha alwashin ci gaba da aiwatar da manufofinta na raya dangantakarta da Nijar
  • Ma’aikatar Sharia A Nan Iran Zata Bayyana Abinda ya farsu A Tashar Jiragen Ruwa Na Shahid Rajae
  • Iran Da Iraki Sun Ce An Kammala Shimfida Layin Dogo Daga Shalamcheh Zuwa Basra
  • Riza’i: Babu Hannun  Waje A Cikin Hatsarin Da Ya Faru A Tashar Ruwa Ta Shahid Raja’i
  • Abubuwan Da Na Gani A Yankin ‘Hero Bay’ Da Ke Cikin Kasar China
  • Karin Wata Kasa Da Bai San Ta Ba A Doron Duniya
  • Shin Amurka Na Iya Komawa Kan Kadaminta A Matsayin Cibiyar Masana’antun Duniya?
  • Shugaban Kasar Yana Maraba Da Masu Zuba Hannun Jari A Kasarsa Daga Kasashen Waje
  • Jagora Ya Bada Umurnin A Gudanar Bincike Mai Zurfi A Fashewar Tashar Jiragen Ruwa Na Shaheed Rajae