Leadership News Hausa:
2025-07-29@15:33:31 GMT

Sarkakiyar Da Ke Tattare Da Zaben 2027 Da Yadda Za Ta Kaya

Published: 14th, June 2025 GMT

Sarkakiyar Da Ke Tattare Da Zaben 2027 Da Yadda Za Ta Kaya

Babu abin da ya rage yanzu, illa babatun zantukan siyasa da ‘yan siyasar ke ta fama yi a kasar, wadanda suka jarabtu da matukar son mulki. Wannan abu da ke faruwa yanzu, ko shakka babu zai canja, zai canja din ne kuwa yayin da ‘yan siyasar ke aiwatar da tsare-tsarensu, sai masu jefa kuri’u a Nijeriya kuma su yanke hukunci.

Shekarar 2027, za ta kasance mai ban mamaki tare da kalubale ga ‘yan Nijeriya.

A bisa dukkan alamu, jam’iyyar APC ta dukufa wajen kara habaka karfinta ne kawai da ganimar ‘yan adawa. Tana ta faman sa kanta cikin rigingimu, har wadanda ba su shafe ta ba a cikin shekaru biyun da ya rage mata ta yi gaba na kunci da tsanani. Maimakon gwamnatin ta mayar da hankali kan nauye-nauyen da ke kanta, na yi wa al’ummar kasa aiki; sai ta buge da yin fada da jam’iyyar adawa, kullum cikin wasa wukarta; a gefe guda kuma gazawar gwamnatin na fitowa fili.

Kura-kuren gwamnatin sun hada da; girman kai wajen tafiyar da al’amuranta, rashin tafiyar da abubuwa yadda ya kamata; tunanin cewa, jawo ‘yan adawa zai ba ta dama tare da karfin yin fada da kuma lashe zabe; ta hanyar zaben shugaban kasa cikin sauki, wanda kowane bangare zai bayar da gudunmawarsa. Amma, babbar matsalar ita ce; shugaban kasar ba shi da kima a kusan dukkanin sassan kasar.

Jam’iyya mai mulki, za ta iya bunkasa damar da take da ita, idan ba ta tsayar da Tinubu a 2027 ba, musamman idan za ta tsayar da matashi, lafiyayye, dan siyasa mai gaskiya da son ci gaba. Hakan kuwa, da alamu ba zai yiwu ba, domin Tinubu shi ne ked a wuka da nama a jam’iyyar.

Shugaban kasa da kansa, ba zai iya bayar da shawarar yadda za a yi gyara ta hanyar kawo wani dan takarar da ya dace ba. Idan Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, zai kasance a matsayin dan takara, APC za ta yi amfani da dukkanin damammakin da take das u, musamman na amfani da kudi wajen sayen kuri’u da masu zabe. Rage Muslman Arewa saboda Kiristocin Arewa, na iya zama hadari, amma wannan shi ne kawai abin da za a iya yi.

Haka zalika, jam’iyyar ta zama dakikiyar daliba, domin babu abin da take karantawa illa yadda za ta samu damammaki iri daban-daban na siyasa kadai. Dandazon da ‘yan siyasa suka yi a cikinta, ba karamar barazana ba ce ga masu bukatu daban-daban, musamman idan aka kasa biya musu bukatunsu.

Ko shakka babu, Arewa za ta yi matukar tasiri a zaben da za a yi. Shi ne yankin day a fuskantar ayyukan ta’addanci da kuma mummunan talauci da ke biye da su har zuwa rumfunansu na zabe. Saboda haka, dole ne jam’iyyar ta yi aiki tukur don kaucewa sake faruwar zaben 2015, lokacin da jam’iyya mai mulki ta fuskanci daukacin yankin da suka yi mata zanga-zanga.

Kudu-maso-yamma, za su iya goyon bayansa idan ya kasance manyan ‘yan adawa sun fitar da wani dan takarar daga Arewa, amma wannan rashin kwanciyar hankali da ake fama das hi, ya kamata a ce ya hana kowa barci.

Tasirin Wike, zai iya raunanawa ko karfafawa; ya danganta da matakin da ‘yan adawa suka dauka game da rikice-rikice a Kudu-maso-kudu, wanda zai iya daidai da bukatunsu; ba abubuwan da suka dace ba. Za a lalata jam’iyyar LP ba tare da Obi ba, a kuma matse shi a matsayinsa na dan takararta.

Burin Obi yanzu, ya wuce batun jam’iyyar LP; amma akwai barazanar samun raguwa a matsayinsa na dan siyasa, idan ya yanke shawarar da za ta iya raba mabiyansa. Kudu-maso-gabas, sun kagu su ga sun samu mukamin shugabancin kasa, wanda hakan ke nuna kishinta na samun daidaito. Hakan, na iya yiwuwa ta hanyar samun daidaito, ana iya samun hakan ta hanyar yarjejeniya a tsakanin yankunan da ake da su.

Da alamu dai, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ne ke da babbar matsala. Ya yi rauni da yawa da zai iya ja da bukatar Tinubu na neman wa’adi na biyu. Don haka, sake barin jam’iyyar PDP tare da neman wata jam’iyyar daban, hanya ce kawai ta kasha makudan kudade da bata lokaci da sauran makamantansu.

PDP a halin yanzu, na zub da jini ne sakamakon zagon kasan da jam’iyya mai mulki ke yi mata. Babbar kadararta shi ne Atiku, amma kuma shi ne babbar matsalarta. Matsayinsa na farko a jam’iyyar, shi ne ke haifar da korafe-korafe da rudani, zai yi wuya PDP tare da Atiku su shiga yarjejeniyar da za ta bayar da dama a karo na biyu.

Idan da PDP za ta iya gyaruwa ta samu nasara a kan APC, dab a ta damu da neman biyan bukatun da suka fi muni ko kawo rudani ba. Jam’iyyar da ta taba yi wa al’ummar kasar barazana, yanzu kuma tana cikin sadar kafa tarihi wajen rubuta ta a matsayin wacce da fi bayar da gudunmawa wajen samun nasarar APC 2027.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: a jam iyyar

এছাড়াও পড়ুন:

Sin Ta Samar Da Manyan Manhajojin AI Sama Da 1500

Kasar Sin ta fitar da manyan manhajojin AI har 1,509, matakin da ya sanya ta kaiwa matsayi na daya cikin jerin sassan duniya da suka fitar da jimillar irin wadannan manhajoji 3,755. Masana na ganin bunkasar sashen masana’antun fasahohin AI na kasar Sin zai ingiza sabbin nasarori a fannin.

A jiya Lahadi, yayin taron karawa juna sani na kasa da kasa game da AI na shekarar 2025, an gudanar da baje kolin nasarori da aka cimma a fannin masana’antun AI na Sin. Kuma a cewar sashen lura da bayanai na cibiyar bincike game da harkokin sadarwa ta Sin, adadin kamfanonin AI na sassa daban daban na duniya ya kai sama da 35,000, yayin da Sin ke da irin wadannan kamfanoni har 5,100, adadin da ya kai kaso 15 bisa dari na jimillar wanda ake da shi a duniya baki daya.

Rahotanni na cewa, adadin masana’antun fannin na ta karuwa ta fuskar kayayyakin more rayuwa, da kayayyakin da yake samarwa domin amfani a masana’antu. Kazalika, akwai jimillar kamfanonin AI masu daraja da yawansu ya kai 271 a duniya baki daya, ciki har da 71 na kasar Sin, adadin da ya kai kaso 26 bisa dari na jimillar wadanda ake da su a duniya. (Mai Fassara: Saminu Alhassan)

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ‘Yan Sanda A Kano Sun Kama Kasurgumin Dan Fashin Nan Barga Da Wasu Mutum 14
  • Sin Ta Samar Da Manyan Manhajojin AI Sama Da 1500
  • SDP Ta Kori Tsohon Gwamnan Kaduna El-Rufai
  • Lebanon: Za A Yi Jana’izar  FItaccen Mawakin Gwagwarmaya Da Kishin Kasa Ziyad Rahbani A Yau Litinin
  • Arewa za ta kayar da Tinubu a zaɓen 2027 —Babachir
  • Sin Ta Samu Ci Gaban Aikin Jigilar Kaya A Rabin Farko Na Bana
  • Gwamnatin APC ta jefa ’yan Najeriya cikin ƙangin talauci — Shugabar LP
  • LP za ta ceto Nijeriya daga halin da APC ta jefa ta — Nenadi Usman
  • ADC ce kaɗai za ta iya magance matsalolin Arewa — David Mark
  • Sin Ta Gudanar Da Gasar Kirkire-kirkire Ta Daliban Kasa Da Kasa A Yankin Afirka Karo Na Farko