Jami’in Hamas Ya Jinjinawa Iran Kan Kakkausan Martanin Da Ta Mayar Kan Haramtacciyar Kasar Isra’ila
Published: 14th, June 2025 GMT
Jami’in kungiyar Hamas ya bayyana cewa: Kakkausan martanin da Iran ta mayar ya tabbatar da cewa babu mai girman kai da ba zai fuskanci mayar da martani ba
Izzat al-Rishq mamba na ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ya jaddada cewa: Kakkausan martanin da Iraniyawa suka mayar ya tabbatar da cewa; babu mai girman kai da ba zai fuskanci mayar da martani kan zaluncinsa ba, kuma babu wuce gona da iri ba tare da hukunci ba.
Izzat al-Rishq ya yi nuni da cewa: Tabbas makamai masu linzami da jiragen saman yaki marasa matuka ciki na Iran sun yi nasarar kai wa cikin tsakiyar haramtacciyar kasar Isra’ila, duk kuwa da kace-nacen da ake yi na girke na’urorin kakkabo makamai a haramtacciyar kasar Isra’ila musamman Iron Dome, Arrow da David’s Sling.
Al-Rashq ya kuma bayyana cewa: Tsarin tsaron haramtacciyar kasar Isra’ila ya gaza shawo kan hare-haren da Iran suka kai, kuma a halin yanzu gwamnatin mamayar Isra’ila tana fama da gobarar da ta kunna a tsakanin al’ummomin yankin. A karshe ya jaddada cewa: Sakon a bayyane yake: Duk wanda ya yi tsokana, to tantana kudarsa.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Ɗangote zai gina ɗakunan kwanan ɗalibai 250 a Jami’ar Ilorin
Babban attajirin Afirka kuma Shugaban Rukunin Kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Ɗangote, ya ɗauki nauyin gina ɗakunan kwanan ɗalibai masu gadaje 250 da Babban Masallacin Juma’a na Ilorin ya tsara a Jami’ar Ilorin da ke Jihar Kwara.
An kiyasta aikin zai ci kusan naira biliyan 1.1, kuma an ƙaddamar da shi ne domin samar da hanyar samun kuɗin kula da masallacin.
Ana sa ran kuɗaɗen haya da za a samu daga ɗaliban da za su zauna a wurin zai rika shiga asusun kula da masallacin.
Sakataren kwamitin amintattu na masallacin, Alhaji Shehu AbdulGafar, ya shaida wa manema labarai a Ilorin cewa Ɗangote ya riga ya sanar da su cewa zai ɗauki nauyin aikin gaba ɗaya.
Cire tallafin man fetur shi ne abin da ya dace —Sarki Sanusi II NAJERIYA A YAU: Yadda Wasu Al’ummomi Suke Kare Kansu Daga Barnar Ambaliyar RuwaYa ce an riga an rattaba hannu kan yarjejeniya da Jami’ar Ilorin wadda ta ba wa masallacin damar mallaka da gudanar da ɗakin kwanan ɗaliban na tsawon shekaru 21 kafin a miƙa shi ga jami’ar.
Baya ga aikin ginin, Ɗangote ya kuma yi alƙawarin bayar da tallafin Naira miliyan 5 a kowane wata domin kula da masallacin har sai an kammala aikin.
AbdulGafar ya ce wannan taimako zai rage nauyin kuɗin aikin, tare da tabbatar da ɗorewar ayyukan masallacin.
Ya ƙara da cewa ɗakin kwanan zai taimaka wajen rage matsalar ƙarancin wurin kwana ga ɗaliban jami’ar.
Shugabannin al’umma da sauran masu ruwa da tsaki sun yaba wa Ɗangote, sun bayyana wannan mataki a matsayin abin koyi na yadda za a iya haɗa kai tsakanin cibiyoyin addini da ’yan kasuwa wajen ci-gaban al’umma.