Ambaliya: Gwamnatin Kano ta fara tsaftace magudanan ruwa
Published: 13th, June 2025 GMT
Yayin da damina ke ƙara ƙaratowa, Gwamnatin Jihar Kano, ta fara wani aikin tsaftace manyan magudanan ruwa domin daƙile aukuwar ambaliyar ruwa.
An fara aikin ne a yankin shataletalen Baban Gwari, ɗaya daga cikin wuraren da ambaliya ke yawan aukuwa a Birnin Kano.
Harin Isra’ila a kan Iran ya jefa yankin Gabas ta Tsakiya cikin zama dar-dar NAJERIYA A YAU: Rashin Aikin Yi Da Hanyoyin Magance Su A NajeriyaMa’aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi ce ke jagorantar aikin tsaftace magudanan ruwan.
Wannan mataki na daga cikin shirin gwamnatin jihar na kare rayuka, dukiyoyi, da kuma inganta ababen more rayuwa.
A lokacin ƙaddamar da aikin, Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi, Hashim Muhammad Dahiru, ya bayyana cewa an zaɓi Baban Gwari saboda muhimmancinsa da kuma yadda wajen yake a lokacin damina.
Ya ce wajen ya daɗe da zama wajen zubar da shara barkatai da kuma toshe hanyoyin ruwa.
Ya ƙara da cewa wannan wajen ba wai kawai muhimmiyar mahaɗa ba ce, amma kuma yana ɗaya daga cikin manyan hanyoyin ruwa da ke da alaƙa da ruwan Jakara da Kwarin Gogau.
Kwamishinan ya bayyana cewa mazauna yankin da masu wucewa sun sha fuskantar ambaliya da ta shafi rayuwarsu, lafiyarsu da kuma zirga-zirgarsu.
Ya ce wannan aikin ba na al’ada ba ce, illa alama ce da ke nuna cewa gwamnatin jihar ta ɗauki matakin kare muhalli da kuma samar da birni mai jure sauyin yanayi da ambaliya.
Ya yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa jagoranci da goyon bayan da ya bai wa ma’aikatar wajen aiwatar da wannan aiki.
Ya ce gwamnatin ta amince da sanya tsaftace magudanan ruwa a matsayin aikin da za a riƙa gudanarwa a kowace shekara domin tabbatar da tsaftar hanyoyin ruwa a faɗin jihar.
Haka kuma, gwamnatin ta bayar da kwangilar gyaran shataletalen Baban Gwari domin inganta zirga-zirga da rage yawan ambaliya, ta hanyar gina sabbin hanyoyin ruwa.
Kwamishinan ya bayyana cewa waɗannan matakai suna nuna irin hangen nesa da damuwar gwamnan jihar kan lafiyar jama’a da kuma kare su daga illolin da ke zuwa da ambaliya da sauyin yanayi.
Ya buƙaci jama’a da su daina zubar da shara barkatai, musamman a cikin magudanan ruwa, ya kuma buƙaci su riƙa ɗaukar nauyin tsaftace muhallinsu.
Ya ce gwamnatin za ta yi nata aikin, amma ana buƙatar haɗin gwiwar kowa da kowa domin a cimma nasara.
Ya kuma buƙaci ma’aikata da abokan aikin muhalli da su gudanar da aikinsu da kulawa da gaskiya, yana mai cewa aikin ba wai tsaftace magudanan ruwa ba ne kawai, amma aikin ne na kare rayuka, daƙile haɗura da kuma gina sabuwar Kano mai tsafta da lafiya.
A ’yan shekarun nan, yankin Baban Gwari ya yi ƙaurin suna wajen yawan aukuwar ambaliya, har ma da rasa rayuka da dukiyoyi.
Wannan ya sa gwamnatin jihar ta ɗauki matakin gaggawa domin magance matsalar kafin saukar daminar bana.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ambaliyar ruwa Kwamishina magudanan ruwa shara tsaftace magudanan ruwa gwamnatin jihar hanyoyin ruwa Baban Gwari
এছাড়াও পড়ুন:
Jami’ar Jihar Gombe za ta fara sabbin darussa 6 a fannin noma
Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC) ta amince da fara karɓar dalibai a sabbin darussa guda shida a fannin noma a Jami’ar Jihar Gombe (GSU) a shekarar karatun 2025/2026.
Za a gudanar da shirye-shiryen ne a sabuwar Tsangayar Noma da aka kafa a garin Malam Sidi da ke Karamar Hukumar Kwami.
A ranar Litinin bayan taron majalisar gudanarwar jihar, Kwamishinan Noma da Kiwo, Barnabas Malle, ya bayyana cewa an amince da fara aikin sabuwar tsangayar aikin nomar ce ranar 21 ga Watan Mayu, 2025.
Sabbin darussan da aka amince da su sun haɗa da digir a bangaren Noma, Digiri a bangaren Gandun Daji da Dabbobin Jeji, Digiri a Kimiyyar Noma da Digiri a Kimiyyar Kasa, sai Digiri a fannin Tattalin Arzikin Noma.
Wani mutum ya mutu yayin raba faɗar ma’aurata ’Yan bindiga sun kashe mutum 5 a sabon hari a AlkaleriBarnabas Malle ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta ware filin gona mai girman hektar 365 a Garin Tafida da ke Karamar Hukumar Yamaltu Deba, domin bincike da aikin gwaji na ɗalibai.
Ya kara da cewa ana kokarin samun ƙarin fili a Garin Kurugu da ke Karamar Hukumar Kwami, don fadada ayyukan kwalejin a nan gaba.
Kwamishinan Ilimi Mai zurfi, Shettima Gadam, ya kuma tabbatar da cewa NUC ta ba da cikakken izini ga jami’ar don fara daukar daliban ne a wadannan darussa daga shekarar karatun 2025/2026.