Wakilin Sin: Matakin Amurka Game Da Harajin Kwastam Bai Yi La’akari Da Rarar Cinikayyar Hidimomi Ba
Published: 14th, June 2025 GMT
Kungiyar cinikayya ta duniya wato WTO, ta gudanar da taron shekara-shekara na biyu, na hukumar zartaswar cinikayyar hidimomi a birnin Geneva dake kasar Switzerland a jiya Juma’a, inda bangaren Sin ya yi nuni da cewa, matakin Amurka game da harajin kwastam na tattare da rashin fahimta da rashin gaskiya a wasu fannoni, don haka ya bukaci bangaren Amurka da ta bi ka’idojin kungiyar WTO, da daidaita matsaloli ta hanyar yin hadin gwiwa a tsakanin bangarori daban daban, da dakatar da daukar matakai daga bangare daya, don tabbatar da tsarin ciniki na duniya tare da bangarori daban daban.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Najeriya Na Asarar Dala Biliyan 10 Bayan Girbi Duk Shekara- Gwamnatin Tarayya
Gwamnatin Tarayya ta ce Najeriya na rasa sama da Dala Biliyan 10 duk shekara sakamakon asarar amfanin gona bayan girbi.
Ministan Noma Sanata Abubakar Kyari ne ya bayyana haka a wajen kaddamar da shirin Hanyar Inganta Noma da Kayayyakin Mire Rayuwa a Yankunan Karkara G.R.A.I.N a ƙaramar hukumar Birnin Kudu ta Jihar Jigawa.
Ya ce asarar na faruwa ne saboda rashin ingantattun wuraren ajiya, karancin ababen more rayuwa, sauyin yanayi da kuma ambaliya.
Kyari ya bayyana cewa noma na bada gudunmawar kashi 24 bisa 100 na Jimillar Darajar Kayayyaki da Ayyuka da Kasa ta Samar a Cikin Shekara GDP, inda ƙananan manoma ke samar da sama da kashi 70 bisa 100 na abincin da ake ci a ƙasa.
Ya jaddada cewa gwamnati za ta tallafa musu da kayan noma na zamani da wuraran kasuwanci domin inganta tattalin arziki.
A nasa jawabin, Gwamna Umar Namadi na Jigawa ya yaba da samun Cibiyar Cigaban Karakara ta Pulse ta farko a Jigawa, yana mai cewa za ta kawo sauyi a harkar noma da rayuwar jama’ar karkara.
Haka zalika, shi ma Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, ya ce haɗin gwiwar gwamnati da masu zaman kansu zai taimaka wajen ci gaban tattalin arziki.
Shugaban ƙaramar hukumar Birnin Kudu, Alhaji Builder Muhammad Uba, ya jaddada goyon bayansa ga shirin Renewed Hope Agenda na Shugaba Tinubu tare da yabawa gwamnatin Namadi kan sauya fasalin noma a jihar.
Usman Muhammad Zaria