Na’im Kassim: Harin HKI Akan Iran Ba Abinda Zai Jawo Mata Sai Kaskanci
Published: 13th, June 2025 GMT
Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta Lebanon Sheikh Na’im Kassim ya yi Allawadai da harin da HKI ta kai wa Iran, wanda ya bayyana shi da cewa; Yana da hatsarin gaske, kuma ‘yan sahayoniyar sun yi hakan ne bisa cikakken goyon bayan Amurka.
Sheikh Na’im Kassim ya kuma bayyana cewa; Harin na ‘yan sahayoniya ba shi da wani dalili da ya wuce a rufe bakin gaskiya wanda yake taimakawa al’ummar Falasdinu a Gaza da ake yi wa kisan kiyashi, haka nan kuma taimakawa da goyon bayan gwgawarmayar Lebanon da dukkanin wannan yankin.
Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya kuma kara da cewa; Wannan harin da wuce gona da irin za iyi tasiri mai girma a cikin wannan yankin, sannan ya kara da cewa: Wannan harin ba zai wuce ba tare da fuskantar martani daga jamhuriyar musulunci ta Iran.
Haka nan kuma Na’im Kassim ya kara da cewa; Isra’ilawa makiya tare da Amurka ba za su taba yin tasiri akan hanyar da Iran ta zabarwa kanta ba ta gwgawarmaya ko kuma rawar da take takawa a cikin wannan yankin.
Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya ce; Hizbullah da magoya bayanta, suna ci gaba da riko da tafarkin gwagwarmaya da kuma goyon bayan jamhuriyar musulunci ta Iran wajen kare hakkokinta.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Dakarun Yemen Zasu Kara Daukan Matakai Kan Jiragen Ruwan Da Ke Hulda Da Isra’ila
Dakarun kasar Yemen sun sanar da sabbin zabukan kara rurutan bude wuta kan makiya a matsayin martani ga abubuwan da suka faru a Gaza
Dakarun sojin kasar Yemen sun bayyana a cikin wata sanarwa da suka fitar a yammacin jiya Lahadi cewa: Suna tunanin zafafa yakin da suke yi da ‘yan mamaya dangane da abin da ke faruwa a Zirin Gaza na kisan kare dangi da kakaba masifar yunwa kan al’ummar yankin.
Rundunar sojin kasar ta Yemen ta tabbatar da fara aikin killace teku kashi na hudu a kan makiya, inda zasu kai hari kan dukkanin jiragen ruwan kamfanonin da ke aiki a tashar jiragen ruwa na Isra’ila, ba tare da la’akari da kasarsu ba, da kuma duk inda sojojin suka isa.
Sanarwar da Rundunar Sojin ta fitar ta ce, bisa la’akari da ci gaban da ake samu a Falastinu da aka mamaye, musamman a zirin Gaza, ci gaba da yakin kisan kiyashi, da kuma shahadar dubun dubatar al’ummar Falastinu sakamakon wuce gona da iri da aka shafe tsawon watanni ana yi, da ke lashe rayukan al’ummar Falasdinu cikin abin kunya na Larabawa, Musulmi da kuma duniya kan irin wannan mummunan shiru, lallai kasar Yemen, zata kalubalanci irin wadannan munanan hare-hare da ake kai wa na kisan kiyashi, wanda ba a taba ganin irinsa ba a tarihin wannan zamani, kasar Yemen ta samu kanta a matsayin wajibin fuskantar wani nauyi na addini da ɗabi’a, da kuma jin kai ga waɗanda ake zalunta a kullum rana.