Ambaliyar Mokwa: An sake gano gawar mutum bayan kwanaki 8
Published: 13th, June 2025 GMT
Kwanaki takwas bayan wata mummunar ambaliyar ruwa da ta mamaye garin Mokwa, hedikwatar Ƙaramar hukumar Mokwa a Jihar Neja, an gano gawar mutum ɗaya daga cikin waɗanda lamarin ya rutsa da su.
Mazauna garin sun shaida wa Daily Trust cewa, an tsinci gawar ne a ranar Alhamis a wata gona da ke kan hanyar wucewa kusa da wani wuri da aka fi sani da ‘dam’.
A cewar shaidun gani da ido, an kasa tantance wanda abin ya shafa saboda gawar ta lalace. An binne shi ne a inda aka gano gawarsa.
Wata mazauniyar yankin mai suna Tswata Mai Rubutu da ta zanta da Aminiya ta wayar tarho, ta ce an tsinci gawar a kan hanyar da ruwa ke wucewa.
“Gawar wani babban mutum ne, amma ba za mu iya gane shi ba saboda tuni ya fara lalacewa. An binne shi a wurin tun da ba a iya motsa gawar,” in ji shi.
An yi ƙoƙarin jin ta bakin Darakta Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja, Abdullahi Baba Arah, domin ƙarin bayani lamarin ya ci tura.
Tun da farko hukumar ta tabbatar da mutuwar mutane 161, yayin da wasu da dama suka ɓace bayan iftila’in ambaliyar.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Sojojin HKI Sun Ci Gaba Da Kashe Kawunansu
A cikin kwanakin bayan nan ana samun karuwar sojojin HKI da suke kashe kawunansu saboda tabuwar kwakwalensu sanadiyyar yakin Gaza.
Kafafen watsa labarun HKI sun kunshi rahotanni da suke bayani akan yadda sojojin mamayar da su ka yi yaki a Gaza, suke samun tabuwar hankali, da hakan yake sa su kashe kawukansu bayan sun baro Gaza.
Wasu rahotannin sun ambaci cewa, sojojin na HKI suna rayuwa ne a cikin tsaro da ranaza saboda munanan ayyukan da su ka aikata marasa kyau.