HausaTv:
2025-07-31@06:41:15 GMT

Oman ta tabbatar da soke tattaunawar Iran da Amurka zagaye na shida

Published: 15th, June 2025 GMT

Ministan harkokin wajen Omani Badr Albusaidi ya sanar da cewa, ba za a gudanar da zagaye na shida na tattaunawar nukiliya tsakanin Iran da Amurka ba.

Yau Lahadi ne aka shirya gudanar da zagaye na gaba na shawarwari a Muscat babban birnin kasar Oman.

A cikin wani sakon da ya wallafa a kan X (tsohon Twitter), Albusaidi ya tabbatar da sokewar, yayin da ya jaddada cewa “diflomasiyya da tattaunawa sun kasance hanya daya tilo ta samun zaman lafiya mai dorewa.

“Tattaunawar Iran da Amurka, wadda aka shirya gudanar da ita a birnin Muscat ranar Lahadin nan, ba za ta gudana a yanzu ba.

Tattaunawar diflomasiyyar da aka faro kan shirin nukiliyar Iran, a watan Afrilu a shiga tsakanin masarautar Oman, ta wargaje biyo bayan mummunan harin da Isra’ila ta kai kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi, a wata tattaunawa ta wayar tarho da shugabar harkokin wajen kungiyar EU Kaja Kalas a ranar Asabar, ya ce ci gaba da tattaunawa da Amurka a cikin danyen aikin da Isra’ila ke yi bai da wata fa’ida.

Babban jami’in diflomasiyyar na Iran ya ce kalaman shugaban Amurka sun tabbatar da cewa matakin da Isra’ila ta dauka kan Iran ya samo asali ne daga goyon bayan da Washington ke baiwa gwamnatin Tel-Aviv kai tsaye.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Iran Ta Ce Amurka Ce Bayan Hare-haren Da Aka Kai Zahidan

Alkalin alkalan JMI Gholamhussain Muhsen Ejei, ya bayyana cewa, babu shakka gwamnatin kasar Amurka tana da hannu a hare-haren da ake dangantawa da kungiyar yan ta’adda ta Jaishul Zulm da ya faru a cikin wani kotu a garin Zahidan na lardin sistan Baluchistan a cikin yan kwanakin da suka gabata.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto alkalin alkalan yana fadar haka a lokacinda ya kai ziyara a gaisuwar wadanda abin ya shafa. Ya kuma bukaci mataimakinsa ya gabatar da dukkan bukatun da wadanda abin ya shafa suka gabatar.

A cikin maganar sa alkalin alkalan ya bayyana cewa, an halaka mutane uku a musayar wuta da yan ta’addan a kusa da kotun. Sannan JMI ta samar da shahidai 6 sannan wasu 22 suka ji rauni.

Yankin Sistan Baluchistan dai ya dade yana fama da hare-hare na wannan kungiyar, kuma tana da sansani a cikin kasar Pakistan wacce take makobtaka da kasar a kudu maso gabacin kasar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ