Ma’aikatar Harkokin Wajen Sudan na zargin Janar Haftar na Libiya da goyon bayan hare-haren ‘yan tawayen kasarta

Sojojin Sudan da ma’aikatar harkokin wajen Sudan sun zargi Janar Khalifa Haftar mai ritaya da goyon bayan hare-haren da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces suka kaddamar a kan iyakokin Sudan da Masar da Libya.

A cewar sanarwar da Rundunar Sojin Sudan ta fitar, Dakarun Kai Daukin Gaggawa na Rapid Support Forces da ke samun goyon bayan Bataliyar Salafiyya ta Haftar, sun kai hare-hare kan iyakokin Sudan da Masar da Libya, da nufin kwace wadannan yankuna masu matukar muhimmanci.

Sanarwar ta kara da cewa: Wannan shiga tsakani da dakarun Haftar suka yi kai tsaye ya zama “cin zarafi a fili” ga ‘yancin Sudan da al’ummarta, tare da nuna cewa harin wani bangare ne na makircin kasa da kasa da na yanki bisa cikakkiyar masaniya da fahimtar kasashen duniya.

Sojojin kasar ta Sudan sun jaddada aniyarsu ta tunkarar wannan ta’addanci, ba tare da la’akari da irin makircin da ake kullawa ba, gami  da tabbatar da aniyarsu ta kare ‘yancin kan kasa tare da goyon bayan al’ummar Sudan.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: da goyon bayan

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamna Namadi Ya Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda

Daga Usman Muhammad Zaria

 

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta yi kira ga mazauna jihar Jigawa da su kasance masu bin doka da oda, tare da yin aiki kafada da kafada da rundunar ‘yan sanda domin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a fadin jihar.

Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Jigawa, CP Dahiru Muhammad, ne ya bayyana haka lokacin da ya karɓi sabbin motoci 10 kirar Toyota Hilux da Gwamna Umar Namadi ya bai wa rundunar a Dutse, babban birnin jihar.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Lawan Shiisu Adam, ya fitar, CP Dahiru Muhammad ya yaba da jajircewar Gwamna Umar Namadi wajen tallafa wa hukumomin tsaro domin sauke nauyin da ke kansu a jihar.

Ya bayyana cewa, wannan gudummawa ta nuna cikakken kudirin gwamnatin Gwamna Namadi na ƙara inganta harkokin tsaro da kuma tallafawa Rundunar ‘Yan Sanda ta Najeriya wajen aiwatar da aikinta na kare rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin jihar.

Kwamishinan ya nuna cewa, waɗannan sabbin motoci 10 za su taimaka matuƙa wajen rage lokacin da ake ɗauka kafin amsa kiran gaggawa, tare da ƙara inganta aikin rundunar a fadin jihar.

Ya ƙara da cewa, za a yi amfani da motocin yadda ya kamata, tare da kula da su don tabbatar da ingantaccen  tsaro.

CP Dahiru Muhammad ya kuma sake jaddada aniyar rundunar wajen ci gaba da tabbatar da zaman lafiya, doka da oda, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba
  • Kasar Qatar Ta Ba Da Tallafin Gaggawa Ga Al’ummar Sudan Bayan Gumurzun El-Fasher
  • Shin Mene Ne Matsalar Liverpool A Wannan Kakar?
  • Gwamna Namadi Ya Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda
  • Kwamitin Tsaron MDD ya goyi bayan shirin Morocco game da yankin Yammacin Sahara
  • An Tube Yarima Mai Jiran Gado Na Birtaniya Bayan Da Aka Tabbatar Da Laifinsa
  • Sudan Ta Yi Kira Ga Kwamitin Tsaro Da Ya Ayyana RSF A Matsayin Kungiyar ‘Yan Ta’adda
  • Masar da Eritrea Sun Tattauna Bukatar Tallafawa Kasar Sudan
  • Xi Jinping Ya Halarci Kwarya-Kwaryan Taron Shugabannin APEC Na 32 Tare Da Gabatar Da Jawabi
  • Madagascar Ta Sanar da Kafa Sabuwar Gwamnati Tare da Manyan ‘Yan Adawa