Amfanin ‘Ya’yan Gwanda Da Yadda Ake Sarrafa Su
Published: 14th, June 2025 GMT
Ciwon Olsa
Ga mai fama da ciwon Olsa, sai ya nemi garin ‘ya’yan Gwanda cokalin shayi daya; ya zuba a kunu sau daya a rana, har tsawon kwana bakwai, za a rabu da ita da yardar Allah.
Ruwan Maniyyi
Ga masu fama da karancin ruwan maniyyi, sai ya nemi garin ‘ya’yan Gwanda da Madara ya hada ya rika sha, wannan hadi na matukar kara ruwan maniyyi.
Ciwon Siga: Shan garin ‘ya’yan danyar Gwanda cokali daya a ruwan dumi, na sauke Siga cikin kankanin lokaci a jikin mutum da izinin Allah.
Hana Daukar Ciki
Ga masu son yin tsarin iyali, shan garin ‘ya’yan Gwanda cokalin shayi daya a ruwan dumi bayan yin jima’i, na hana ciki ya shiga.
Taifot Da Maleriya
Ana kiba ‘ya’yan Gwanda a tace a ruwa, kimanin lita hudu (Galan daya), a zuba zuma kimanin cokali 10 a sha rabin kofi sau biyu a rana har ya kare, za a samu lafiya in sha Allah.
Cutar Daji (Cancer)
Shan ruwan ‘ya’yan Gwanda da aka kirba aka tace kofi daya a rana sau daya, yana rigakafin kamuwa da ciwon Daji.
Amma fa ban da masu jinjirin ciki ko kuma wadanda ba su da daya daga cikin wadannan cutuka. Sannan, har masu ciwon Hanta ma za su iya yin amfani da shi in sha Allah.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: ya yan Gwanda
এছাড়াও পড়ুন:
Taron APEC Na 2026 Da Za A Shirya A Kasar Sin Zai Bude Sabon Babin Na Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik
Bayan an mika damar karbar bakuncin taron kungiyar APEC, kasashen duniya sun soma zura ido kan kasar Sin. Ana sa ran cewa, taron APEC da za a gudanar a Shenzhen, zai kara habaka hadin gwiwa, da samun ci gaba, da wadata tare a shiyyar, kana zai shaida yadda kasar Sin ke kara samar da sabbin damammaki ga yankin Asiya da Pasifik, bisa ga sabbin nasarorin da take samu ta hanyar zamanantarwa irin ta kasar Sin. (Mai fassara Bilkisu Xin)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA