Damina: NiMet ta gargaɗi jihohi 13 kan barazanar ambaliyar ruwa
Published: 14th, June 2025 GMT
Hukumar Kula da Yanayi (NiMet), ta sake fitar da gargaɗi game da yiwuwar ambaliyar ruwa a wasu jihohin a daminar bana.
A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X, hukumar ta bayyana cewa Jihar Akwa Ibom ce ke fuskantar barazana mafi tsanani a halin yanzu.
Gwamnan Kaduna ya bai wa sabon Sarkin Moro’a sandar mulki Farashin fetur ya tashi a kasuwar duniya bayan harin Isra’ila a IranSauran jihohin da abin ka iya shafa sun haɗa da Sakkwato, Zamfara, Filato, Yobe, Bauchi, Bayelsa, Nasarawa, Binuwai, Ogun, Ekiti, Delta da kuma Ribas.
NiMet ta shawarci al’umma, musamman waɗanda ke zaune a cikin waɗannan jihohin, da su tabbatar sun yashe magudanan ruwa domin bai wa ruwa hanyar wucewa.
Haka kuma ta buƙaci mutane da su nisanci wuraren da ke da hatsarin ambaliya, kuma idan ruwa ya fara ƙarfi, su bar irin waɗannan wuraren domin kare lafiyarsu.
Ambaliya dai na daga cikin manyan matsalolin da ke janyo asarar rayuka da dukiyoyi a Najeriya a duk shekara.
A makonnin baya, garin Mokwa da ke Jihar Neja ya fuskanci ambaliya wadda ta yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 230.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ambaliyar ruwa Barazana
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan sa-kai aƙalla 100 da jami’an tsaro 30 sun mutu a bakin aiki a Katsina —Gwamnati
Sama da mutum 100 daga cikin jami’an tsaron al’umma da Gwamnatin Katsina ta samar ne suka suka mutu a yayin aikin karaɗe ’yan bindiga da suka addabi al’ummomin jihar.
Wannan ƙari ne a kan sojoji da kuma aƙalla jami’an ’yan sanda 30 da suka rasu a yayin aikin tabbatar da tsaron rayuwa da duniyoyin al’umma, a cewar ma’aikatar tsaron jihar.
Kwamishinan tsaron jihar, Nasir Mua’zu ya sanar da haka ne a martaninsa kan wasu rahotanni da ke yawo a kafofin sada zumunta, waɗanda ya ce ana amfani da su domin tayar da hankalin jama’a.
Mu’azu ya ce Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Raɗɗa yana yin iya bakin koƙarinsa wajen shawo kan matsalar ’yan ta’adda kuma ana samun nasara a kansu.
Kwamishinan ya ce lokacin da Gwamna Raɗɗa ya karbi shugabancin Jihar Katsina, ƙananan hukumomi aƙalla 24 ne ke fama da matsalar ’yan bindiga, amma kuma sakamakon haɗin kai da jami’an tsaro da kuma ƙirƙiro ƙungiyar ’yan sa-kai ta jihar, an yi nasarar murƙushe su a ƙananan hukumomi 11.
Mu’azu ya ce, matsalar ta kuma yi sauƙi a wasu ƙananan hukumomi tara, in banda Faskari da Ƙankara da Safana da kuma Matazu, da ke ci gaba da dama da hare-hare.
Ya bayyana cewa hakan ba ya nufin cewa gwamnati ta gaza, domin jami’an tsaro na iya bakin ƙoƙarinsu wajen tabbatar da tsaron lafiya da duniyoyin al’umma a wuraren.
A cewarsa, duk da hatsarin da gwamnan ya yi kwanakin baya, bai daina tattaunawa da shugabannin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki a harkar tsaro ba da ke jihar, domin shawo kan matsalar.
Don haka ya buƙaci haɗin kai daga kowanne ɓangare, musamman ganin yadda jami’an tsaron ke sadaukar da rayukansu wajen kare lafiya.