Sojoji Sun kama ɗan China da wasu 4 kan zargin safarar makamai a Borno da Yobe
Published: 15th, June 2025 GMT
Dakarun Operation Haɗin Kai sun kama mut biyar da ake zargin suna taimaka wa ’yan ta’adda da kayan aiki.
Daga cikinsu har da wani ɗan ƙasar China da ya ce shi mai harkar ma’adinai ne.
Damina: NiMet ta gargaɗi jihohi 13 kan barazanar ambaliyar ruwa Ya kamata Isra’ila da Iran su kawo ƙarshen rikicin da ke tsakaninsu — Gwamnatin TarayyaAn kama su ne a lokacin kai wani samame da aka gudanar daga 5 zuwa 7 ga watan Yuni a ƙananan hukumomin Kukawa da Ngala na Jihar Borno, da kuma Geidam a Jihar Yobe.
A lokacin wannan aiki, dakarun sun ƙwato wasu kayayyaki da suka haɗa da mota, babur, wayoyin salula, fasfo na ƙasar China, da kuma kuɗi Naira 10,000.
Shugaban sashen yaɗa labaran tsaro, Manjo Janar Edward Markus Kangye, ya bayyana hakan a wata ganawa da manema labarai a Abuja.
Ya ce sojojin sun kuma kai farmaki wasu yankuna bisa bayanan sirri da suka samu, ciki har da Gwoza da Abadam a Borno da kuma Nangere a Yobe, daga 6 zuwa 9 ga watan Yuni.
Ya ƙara da cewa daga 6 zuwa 11 ga watan Yuni, wasu maza da mata da yara da dama sun miƙa wuya ga dakarun Najeriya.
Kangye ya bayyana cewa rundunar ta kuma kai wasu hare-hare tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro a Ngala, Marte, Gwoza a Jjihar Borno da Bade da Gujba a Jihar Yobe daga 6 zuwa 10 ga watan Yuni.
A wannan lokaci, sun lalata sansanonin ’yan ta’adda, sun ƙwato makamai da alburusai.
Manjo Janar Kangye ya ce sojojin Najeriya za su ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin ’yan ƙasa tare da tabbatar da doka da oda.
“Mun ƙudiri aniyar kare martabar Najeriya da tabbatar da zaman lafiya a kowane yanki na ƙasar nan. Wannan aiki namu na ci gaba da yin tasiri,” in ji shi.
Ya buƙaci haɗin kan jama’a wajen taimaka wa sojoji su ci gaba da yaƙi da ’yan ta’adda.
Ya ce idan jama’a da hukumomi suka haɗa kai, Najeriya za ta samu zama lafiya da wadata.
“Zamu ci gaba da sanar da al’umma duk wani ci gaba da muka samu wajen yaƙar ta’addanci,” in ji Kangye.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: bayanan sirri dakaru Safara zargi ga watan Yuni
এছাড়াও পড়ুন:
Saudiyya Ta Saki ‘Yan Nijeriya 3 Da Ta Kama Bisa Kuskuren Safarar Ƙwayoyi
Hukumar NDLEA ta bayyana cewa wata ƙungiyar masu safarar miyagun ƙwayoyi ce a filin jirgin sama na Kano ta boye jakunkunan ƙwayoyi a cikin kayan matafiyan.
An kama shugaban ƙungiyar, Ali Abubakar Mohammed (wanda aka fi sani da Bello Karama), tare da wasu abokan aikinsa.
Hukumar ta ce mutanen ukun ba su da laifi kuma an zalunce su ne kawai.
An saki su ne bayan bincike da kuma ƙoƙarin diflomasiyya na tsawon makonni.
Lamarin ya tayar da hankali kan tsaro a filayen jirgin sama a Nijeriya da yadda masu aikata laifuka ke amfani da fasinjoji marasa laifi.
Hukumar ta ce za a ɗauki ƙarin matakai don hana faruwar irin wannan lamari.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp