Mulkin Tinubu ya fi kowane muni tun bayan dawowar mulkin farar hula — Dalung
Published: 13th, June 2025 GMT
Tsohon Ministan Matasa da Wasanni, Solomon Dalung, ya ce shekara biyu da Bola Ahmed Tinubu ya yi a matsayin shugaban ƙasa sun fi kowane lokaci muni tun bayan dawowar mulkin dimokuraɗiyya a ƙasar.
Yayin da yake magana da BBC a ranar Dimokuraɗiyya da Najeriya ke cika shekaru 26 tana mulkin farar hula, Dalung ya ce ba wani abin arziƙi da talaka ya amfana da shi daga wannan gwamnati.
Ya ce: “Kawai abin da talaka ya samu daga gwamnatin Tinubu shi ne tsadar rayuwa, yunwa, wahala da matsalar tsaro.”
Ya zargi gwamnatin da cewa cire tallafin man fetur ba tare da shiri ba, kuma hakan ya jefa mutane cikin ƙuncin rayuwa.
“Talakawa na mutuwa saboda yunwa, amma idan an tambayi Shugaba Tinubu, sai ya ce bai yi nadamar cire tallafin ba,” in ji Dalung.
Gwamnatin Tinubu dai ta ce ta cire tallafin ne domin hana wasu tsiraru ci gaba da cin gajiyarsa da kuma bunƙasa tattalin arziƙin ƙasa.
Amma Dalung ya ce gwamnatin ba ta talaka ta ke ba: “Idan ba canza motoci da jirage da gina sabon gida ga mataimaki ba, to babu wani abu da talaka ya gani.”
Dalung ya ce dimokuraɗiyya na cikin mawuyacin hali tun zuwan Tinubu, ya zargi gwamnati da kama waɗanda ke sukar ta da kuma sayen abokan hamayya wajen komawa APC.
“Mun ga yadda ake kama ‘yan gwagwarmaya saboda kawai sun faɗi ra’ayinsu. Kuma wasu na komawa jam’iyyar APC bayan an saye su,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa gwamnati na barazana ga ci gaban ƙasa idan ba a gyara lamarin ba.
Dalung, ya ce duk da rahoton Bankin Duniya da ke cewa tattalin arziƙin Najeriya na bunƙasa, bai yarda ba.
“Ta yaya za ku ce tattalin arziƙin da ke cikin matsin lamba yanzu yana bunƙasa? Wannan fa ba gaskiya ba ce.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Dimokuraɗiyya Matsin Tattalin Arziƙi
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Daliban Makarantar Kudi Suka Fi Na Gwamnati Kokari
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Duk da cewa gwamnati na da dubban kwararrun malamai a makarantunta, har yanzu ana ganin ɗaliban makarantun gwamnati na kasa da na makarantun masu zaman kansu wajen ƙoƙari da kuma sakamakon jarabawa.
Wannan matsala ta daɗe tana jawo muhawara tsakanin iyaye, malamai da hukumomin ilimi.
Wasu na ganin matsaloli ne da ba za su rasa nasaba da rashin kulawa da watsi da harkar ilimi da gwamnati ta yi ba.
Ko wadanne dalilai ne suka daliban makarantun masu zaman kansu suka fi kokari idan aka kwatanta da daliban makarantu na gwamnati?
NAJERIYA A YAU: Shin Ko Sauya Hafsoshin Tsaro Zai Kawo Karshen Aikin Ta’dda A Najeriya? DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa PDP Ta Ki Sayarwa Sule Lamido Fom Din Takarar Shugaban Jam’iyyaWannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.
Domin sauke shirin, latsa nan