A wata hira tare da gidan talabijin na Arise, Obi ya ce duk da cewa cire tallafin mai yana da muhimmanci, amma ya kamata a aiwatar da wannan tsari cikin tsari.

Ya ce ya amince cewa tallafin mai yana cike da ta’asa da cin hanci wanda akwai bukatar a kawo karshensa, amma ya yi suka ga hanyoyin da gwamnatin Tinubu take bi, yana bayyana su a matsayin wadanda aka yi ba bisa kwarewa ba.

Obi ya tambayi jagororin kula da kudin da aka ajiye daga cire tallafin, yana cewa, “Tun da aka ce manatallafin man fetur, ana cewa an cire ne saboda ba a so mu dunga ciyo bashi kuma kudaden za su ba da dama wajen zuba jari a muhimman ababen more rayuwa.

‘’Ina biliyoyin kudaden da aka tara? Ina aka zuba su a muhimman yankunan ci gaba? Kowa na sane da muhimman yankunan ci gaba da suka hada da ilimi, lafiya, da fitar da mutane daga talauci. Shin ko daya daga cikin wadannan abubuwan gda uku ya inganta? A’a.’’

Obi ya ce ya kamata a yi musayar farashi mai da masu ruwa da tsaki da kyau ta yadda zai rage tasirin ga matsalolin da ‘yan kasa ke ciki.

Da yake mayar da martini ga Obi, mai taimaka wa shugaban kasa kan batutuwan tsare-tsare, Daniel Bwala, ya bayyana dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP a matsayin mutum mai son kansa wanda ba ya da ilimin warware al’amuran da suka shafi tattalin arziki da shugabanci.

Bwala, a cikin wata sanarwa da ya wallafa ta shafinsa na sada zumunta na Tuwita, ya bayyana cewa ya yi mamakin yadda Obi ya yarda da manufofin tattalin arzikin Shugaba Tinubu, musamman kan cire tallafin mai da hada-hadar kudaden waje, amma ya jaddada cewa Obi sauran manyan ‘yan adawa suna neman samun iko ne kawai ko ta wani hali a wannan lokaci.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Tinubu bai shirya gudanar da sahihin zaɓe ba a 2027 – Buba Galadima

Jigo a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya yi zargin cewa gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ba ta da niyyar gudanar da sahihi kuma ingantaccen zaɓe a 2027.

Galadima ya bayyana hakan ne ranar Talata a wata hira da aka yi da shi a shirin Prime Time na gidan talabijin na Arise TV, inda ya ce gwamnatin da jam’iyyar APC ke jagoranta ta kankane cibiyoyin gwamnati don amfaninta.

Gwamnati ta fara duba yara marasa galihu kyauta a asibitin Aminu Kano Tun Tinubu yana Gwamna ba abin da ya fi shahara da shi kamar tara haraji – Adebayo

“Wannan gwamnati ba ta shirya gudanar da zaɓen adalci ba. Daga yadda suke tafiyar da al’amura, za ka gane yadda suke tarwatsa jam’iyyun siyasa. Wannan yana nuna cewa ba sa son a samu hamayya a lokacin zaɓe,” in ji shi.

Galadima ya kuma yi gargadi kan shirin nada wani da ya kira mai lam’a a matsayin sabon shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), yana mai cewa hakan na iya jefa ƙasar cikin rudani.

“Ina fatan ba gaskiya ba ne, domin idan wannan mutumin ya zama shugaban INEC, ka tabbata cewa wannan gwamnati na neman tayar da yaƙin basasa,” in ji shi.

Sai dai bai ambaci sunan mutumin ba.

Dangane da batun fara yaƙin neman zaɓe da wuri da wasu jam’iyyu ke yi, Buba Galadima ya zargi INEC da gazawa wajen aiwatar da tanade-tanaden dokokin zaɓe.

“Wannan batun fara yaƙin neman zaɓe kafin INEC ta ba da izini, gwamnatin da ke kan mulki ce ta fara shi. Wannan yana nuna cewa INEC ba za ta iya zama mai adalci a irin wannan yanayin siyasa da muke ciki ba,” in ji shi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • UNICEF Ya Ba Da Tallafin Kayayyakin Aiki Ga Cibiyoyin Lafiya A Kirikasamma
  • Gwamnati ta ƙaddamar da jiragen ruwa na zamani 20 a Sakkwato
  • Tinubu Ya Janye Dokar Ta-baci A Jihar Rivers
  • Gwamna Namadi Ya Taya Malaman Makarantu Da Suka Yi Fice A Jihar Murna
  • Tinubu bai shirya gudanar da sahihin zaɓe ba a 2027 – Buba Galadima
  • Gwamnatin Kano ta gayyaci Mai Dubun Isa da Shehi Tajul-Izzi kan shirya muƙabala
  • Fadar Shugaban Ƙasa Ta Mayar Wa Atiku Martani Kan Cewar ‘Yan Nijeriya Na Fama Da Yunwa
  • Kakakin Majalisar Jigawa Ya Tsallake Rijiya Da Baya, Tawagar Jami’an Tsaronsa Sun Ji Rauni A Wani Hatsari A Jihar 
  • Peter Obi ya kai wa Obasanjo ziyara
  • Dole sai mun tantance wa’azi kafin a yi —Gwamnan Neja