Martanin sojojin Iran ga Isra’ila zai zama mafi muni idan aka ci gaba da kai hari (Pezeshkian)
Published: 15th, June 2025 GMT
Shugaban aksar Iran, Massoud Pezeshkian, ya bayyana cewa martanin sojojin kasarsa ga Isra’ila zai zama mafi muni idan hare-haren Isra’ilar suka ci gaba.
A wata tattaunawa ta wayar tarho da firaministan Pakistan Shehbaz Sharif, shugaban kasar Iran Massoud Pezeshkian ya tabbatar da cewa dakarun gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta Iran za su dauki kwararan matakan mayar da martani mai tsauri idan har gwamnatin Isra’ila ta ci gaba da kai farmaki kan Iran.
“Masu da’awar kare hakkin bil’adama ba wai kawai suna goyon bayan zaluncin gwamnatin sahyoniyawa ba ne, har ma suna karfafa mata gwiwar aikata wadannan munanan ayyuka ta hanyar ba ta makamai da kayan aiki,” in ji shi.
Mr. Pezeshkian ya kara da cewa gwamnatin Isra’ila da ke samun goyon bayan Amurka da kasashen yammacin Turai ta sabawa dukkanin dokokin kasa da kasa.
A nasa bangaren, firaministan Pakistan ya bayyana goyon bayan kasarsa ga al’ummar iran, yana mai yin Allah wadai da keta hurumin kasar Iran da ‘yancinta, wanda ya zama cin zarafi ga dokokin kasa da kasa da kuma kundin tsarin mulkin MDD.
Sharif ya sake jaddada cewa Iran na da cikakken ‘yancin kare kanta a karkashin doka ta 51 na kundin tsarin mulkin MDD inda ya bayyana fatan ganin an dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Ce Amurka Ce Bayan Hare-haren Da Aka Kai Zahidan
Alkalin alkalan JMI Gholamhussain Muhsen Ejei, ya bayyana cewa, babu shakka gwamnatin kasar Amurka tana da hannu a hare-haren da ake dangantawa da kungiyar yan ta’adda ta Jaishul Zulm da ya faru a cikin wani kotu a garin Zahidan na lardin sistan Baluchistan a cikin yan kwanakin da suka gabata.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto alkalin alkalan yana fadar haka a lokacinda ya kai ziyara a gaisuwar wadanda abin ya shafa. Ya kuma bukaci mataimakinsa ya gabatar da dukkan bukatun da wadanda abin ya shafa suka gabatar.
A cikin maganar sa alkalin alkalan ya bayyana cewa, an halaka mutane uku a musayar wuta da yan ta’addan a kusa da kotun. Sannan JMI ta samar da shahidai 6 sannan wasu 22 suka ji rauni.
Yankin Sistan Baluchistan dai ya dade yana fama da hare-hare na wannan kungiyar, kuma tana da sansani a cikin kasar Pakistan wacce take makobtaka da kasar a kudu maso gabacin kasar.