Miliyoyin Mutane Sun Gudanar Da Bukukuwan “Idin Gadir” A Tehran Da Sauran Garuruwan Iran
Published: 14th, June 2025 GMT
A yau Asabar aka gudanar da bikin ranar ” Idin Gadir” a nan birnin Tehran, wanda ya tashi daga dandalin “Inqilab” zuwa dandalin ” Azadi” mai nisan kilo mita 10. Bisa la’akari da halin yake da ake ciki, an bai wa bikin na bana taken: Iran ce, takobin Zulfikar Na Imam Ali.”
Miliyoyin mutane ne dai su ka cika filin bikin na birnin Tehran da mutane su ka fara taruwa tun da tsakar rana, har zuwa bayan faduwar rana.
A cikin sauran birane da garuruwan Iran an yi wannan irin gangamin na raya ranar Idin Gadir wanda yake tattare da girmama shahidan da su ka kwanta dama sanadiyyar hare-haren ta’addancin HKI. Haka nan kuma mahalarta bikin na Gadir sun jinjinawa dakarun kare juyin musulunci na Iran da kuma sojojin kasar akan martanin da su ka mayarwa da HKI a daren jiya Juma’a da kuma a yau Asabar.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
EFCC Ta Kama Mutane 11 Kan Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Akwa Ibom
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp