Uganda Ta Aike Da Sojoji Zuwa Sudan Ta Kudun Domin Kare Babban Birnin Kasar
Published: 11th, March 2025 GMT
Kasar Uganda ta sanar da aikewa da sojojinta zuwa birnin birnin kasar Sudan Ta Kudu, Juba saboda ba shi kariya. Sai dai har yanzu gwamnatin Sudan din ba ta tabbatar da hakan ba.
Babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Uganda Janar Muhoozi Kainerugaba ya bayyana cewa; Rundunar musamman ta Ugandan ta shiga cikin birnin Juba, domin ba shi kariya.
Janar Muhoozi Kainerugaba ya kuma ce: “ Za mu kare dukkanin kasar Sudan Ta Kudu, kamar yadda za mu kare kasarmu. A wurinmu Salva Kiir ne mu ka aminta da cewa halartaccen shugaban kasar Sudan Ta Kudu,don haka duk wanda zai shelanta yaki akansa, ya shelanta yaki ne akan Uganda.”
Har ila yau janar din na Uganda ya kuma ce; “ Wadanda su ka aikata laifuka za su dandana kudarsu.”
A cikin kwanakin bayan nan an shiga dambaruwar siyasa a kasar Sudan Ta Kudu bayan da gwamnatin shugaban Salva Kiir ta kama jami’an soja da kuma na siyasa masu alaka da mataimakin shugaban kasar Reik Machar. Hakan ya biyo bayan barkewar wani sabon bore ne na ‘yan kabilar Nuer da su ka yi fada da sojojin gwamnati.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kasar Sudan
এছাড়াও পড়ুন:
Za a Yi wa Yara 194,000 Rigakafin Cutar Shan Inna a Karamar Hukumar Birnin Kudu
Karamar hukumar Birnin Kudu dake Jihar Jigawa ta bada tabbacin ci gaba da kulawa da harkokin rigakafi da kiwon lafiya baki daya.
Shugaban karamar hukumar, Builder Muhammad Uba ne ya bada wannan tabbacin lokacin taro da ake gudanarwa a kowace rana kan al’amuran rigakafin cutar Polio da aka gudanar a fadar Hakimin Birnin kudu.
Yace karamar hukumar zata kara da bada fifiko wajen tallafawa harkokin rigakafi domin dakile yaduwar cututtuka a yankin.
A don haka, Builder Muhammad Uba ya bukaci iyaye su kara himma wajen bada hadin kai da goyon baya ga jami’an lafiya a duk lokacin da ake gudanar da rigakafi.
A jawabin da ya gabatar mai kula da al’amuran rigakafi na yankin, Malam Abubakar Alhassan Garki yace ana sa ran yiwa kananan yara 194,000 rigakafin cutar shan inna a karamar hukumar.