IRGC : Iran ta kai hare hare wurare a kalla 150 a Isra’ila
Published: 14th, June 2025 GMT
Wani babban jami’in sojan Iran ya ce an kai hare-hare a kalla wurare 150 a farmakin ramuwar gayya kan gwamnatin Isra’ila, ciki har da wasu sansanonin soji masu matukar muhimmanci.
Da yake zantawa da gidan talabijin na kasar da sanyin safiyar Asabar, Birgediya Janar Ahmad Vahidi, babban mai ba da shawara ga babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran ya ce, rundunar ta IRGC ta yi nasarar aiwatar da shirinta na Operation True Promise III.
A cewar kwamandan na IRGC, an kuma kai hari kan ma’aikatar harkokin soji da cibiyoyin soji da masana’antu a lokacin da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ke daukar fansa.
Daga cikin wadanda harin ya rutsa da su sun hada da Manjo Janar Mohammad Bagheri, babban hafsan hafsoshin sojojin Iran, Birgediya Janar Amir Ali Hajizadeh, shugaban sashin kula da sararin samaniyar IRGC, da Manjo Janar Gholam-Ali Rashid, kwamandan babban shalkwatar Khatam al-Anbiya ta kasar.
Har ila yau, hare-haren sun yi sanadin mutuwar tsoffin masana kimiyyar nukiliya Mohammad-Mehdi Tehranchi, Fereydoun Abbasi, da Dr. Abdol-Hamid Minoucher, tare da fararen hula fiye da 70 da suka hada da yara da mata.
Duk da haka, ya sake nanata cewa wannan babban “kuskure” ne daga bangaren Isra’ila, yana mai gargadin cewa, “Dole ne su jira sakamakon.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Lebanon Ya Umarci Sojoji Da Su Fuskanci Kutsen Na Isra’ila A Kudancin Kasar
Shugaban Lebanon Joseph Aoun ya yi Allah wadai da keta hurumin kasarsa da Isra’ila ke yi a kudancin kasar, yana mai kira da a dauki tsauraran matakai kan duk wani kutse da sojojin mamaye za su yi a nan gaba a cikin Lebanon.
A lokacin wata ganawa da Kwamandan Rundunar Soja Rodolphe Heikal, Shugaba Aoun ya bayyana cewa dole ne Lebanon ta “fuskanci duk wani kutse da Isra’ila ta yi wa yankunan kudancin da aka ‘yantar don kare filayenmu da kuma tsaron ‘yan kasa.”
Wannan jawabi ya zo ne bayan harin da Isra’ila ta kai wa gundumar Blida, inda sojojin Isra’ila suka kashe wani ma’aikacin gundumar a lokacin wani hari da suka kai kan ginin ofishin karamar hukuma.
Daga baya, karamar hukumar ta tabbatar da cewa Ibrahim Salameh, wanda ya kwana a cikin ginin, ya yi shahada bayan da sojojin mamaya suka harbe shi. Aoun ya yi Allah wadai da kisan, yana mai cewa wani bangare ne na ayyukan “Isra’ila” kan fararen hula kuma ya zo ne ‘yan sa’o’i bayan taron da kwamitin da ke sa ido kan yarjejeniyar dakatar da fadan ya gudanar.
0Please leave a feedback on thisxShare
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label Name* Email* Website Label Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Madagascar Ta Sanar da Kafa Sabuwar Gwamnati Tare da Manyan ‘Yan Adawa October 31, 2025 Iran ta yi fatali da kalamman IAEA Kan Shirin Nukiliyarta October 30, 2025 Trump Ya Umarci Ma’aikatar Yakin Amurka Ta koma gwajin makaman nukiliya October 30, 2025 Isra’ila ta amince da fadada matsugunai a Yammacin Kogin Jordan October 30, 2025 Gaza: hare-haren Isra’ila sun kashe mutane 100 Cikin Kwanaki Biyu October 30, 2025 Sudan : Kasashen duniya na tir da cin zarafi a El-Fasher October 30, 2025 Iran Ta Jaddada Bin Hanyar Diflomasiya Ko Da A Lokacin Yaki Ne Amma Ba Zata Amince Da Bin Umarni Ba October 30, 2025 Qalibaf: Amurka Tana Yaudarar Duniya Da Zaman Lafiya, Alhalin Tana Ci Gaba Da Kai Harin Wuce Gona Da Iri October 30, 2025 Ci Gaba Da Killace Gaza Bayan Tsagaita Bude Wuta Ya Janyo Mutuwar Mutane 1000 A Yankin October 30, 2025 Kungiyar Rapid Support Forces Ta Sanar Da Kafa Kwamitin Bincike Kan Cin Zarafin Al’umma A El Fasher October 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci