Hukumar Lamuni Ta Duniya IMF Da Bankin Duniya Sun Ce Bazasu Taimakawa Lebanon Ba Sai Da Sharudda
Published: 28th, February 2025 GMT
Hukumar bada lamuni ta Duniya IMF da kuma bankin duniya, manya-manyan cibiyoyin kudade a duniya sun ce ba zasu bada kudade don sake gina kasar Lebanon ba, sai sun cika wasu sharudda zuwa wani lokaci. Kuma sune samar da huldar jakadanci da HKI da kuma kwance damarar kungiyar Hizbullah.
Jaridar Al-Akhbar ta kasar Lebanon ta nakalto shugaban hukumar IMF Kristalina Georgieva ta fadawa gwamnan babban bankin kasar Lebanon na riko, Wassim Mansouri a wata haduwa da suka y ikan cewa kasarsa zata sami kudaden sake gidan kasar dag wajenta ne, tare da sharudda.
Rahoton ya kara da cewa kasashen Lebanon da Siriya zasu sami kudade daga cibiyoyin biyu ne kawaii dan sun samar da dangantakar diblomasiyya da HKI. Sannan kasar Lebanon kuma sai ta hada da kwance damara, ko ta kwace makaman kungiyar Hizbullah ta kasar wacce take yakar HKI.
Kafin haka dai ministan kudi na kasar Lebanon Yassin Jabir yace bankin duniya ta warewa kasar Lebanon dalar Amurka billiyon daya don sake gina kasar Lebanon bayan yakin da kungiyar Hizbulla ta fafata da HKI.
Labarin ya kammala da cewa idan kasar Lebanon ta cika sharuddan da kasashen yamma suka shardanta zata sami kudaden a cikin watan Maris mai zuwa.
Haka ma kungiyar tarayyar Turai tana da sharudda nab awa kasar Lebanon Euro miliyon E500 saboda ta taimaka ta hana bakin haure shiga kasashen turai daga kasar.
Wasu kafafen yada labarai a kasar Lebanon sun bayyana cewa kasar tana bukatar dalar Amurka biliyon biliyon 6-7 don sake gida abubuwan da HKI ta lalata a yankin da ta yi da kungiyar Hizbullah a shekara ta 2023-2024.
HKI ta amince da tsagaita wuta a dole bayan da mayakan hizbullah sun yi mata barna mai yawa a yakin.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: a kasar Lebanon
এছাড়াও পড়ুন:
Lebanon: Isra’ila Ta Kai Hari Akan Unguwar Dhahiya A Birnin Beirut
Jiragen yakin HKI sun kai hari a yankin Hangara dake unguwar “Dhahiya” a cikin birnin Beirut. Yankin da jiragen yakin na ‘yan sahayoniya su ka kai wa harin, yana cike da mutane da kuma makarantu biyu.
Jiragen yakin na HKI sun harba makamai masu linzami 3, da hakan ya haddasa tashin gobara.
A sanadiyyar wannan harin, an sami shahidi daya,yayin da wasu da dama su ka jikkata.
A ranar 1 ga watan Aprilu ma dai sojojin HKI sun kai wani harin a unguwar Dhahiya wanda ya yi sanadiyyar shahadar mutane 4 da kuma jikkata wasu da dama.
Tun bayan tsagaita wutar yaki a ranar 27 ga watan Aprilu 2025, HKI ta keta wutar yakin fiye da 2000.