Mahara sun kashe mutum 26 a sabon hari a Binuwai
Published: 14th, June 2025 GMT
Aƙalla mutum 26 ne suka rasu sakamakon wasu sabbin hare-haren da aka kai wasu ƙauyuka a Jihar Binuwai.
Hare-haren sun faru ne a yankunan Ƙaramar Hukumar Makurdi da Katsina-Ala tsakanin ƙarfe 12 na dare zuwa 2 na daren ranar Alhamis.
Farashin fetur ya tashi a kasuwar duniya bayan harin Isra’ila a Iran An kashe masu garkuwa da mutane da kuɓutar da wasuA Ƙaramar Hukumar Makurdi, wasu ’yan bindiga sun kai hari ƙauyukan Mtswenem da Akondotyough Bawa, inda suka kashe mutum 25.
Haka kuma, an kashe mutum ɗaya a wani hari daban da aka kai ƙauyukan Kenvanger da Agbami a Ƙaramar Hukumar Katsina-Ala.
Wasu mazauna yankin sun ce ’yan bindigar sun shiga gidajen mutane suna harbin su yayin da suke barci, suna amfani da bindigogi da adduna.
Wani wanda ya tsira mai suna Iorpuu, ya ce mata da yara suna cikin waɗanda aka kashe, kuma har yanzu ana neman wasu da suka ɓace.
Ya ƙara da cewa wasu sun mutu ne a kan hanyarsu ta zuwa asibiti.
Wani ganau ya ce an fara kai harin ne wani ƙauye kusa da Jami’ar Noma da Fasaha ta Makurdi, inda aka kashe mutane huɗu.
Daga nan suka wuce wani ƙauye a kusa da unguwar Low Cost suka ci gaba da kashe mutane har adadin gawarwakin ya kai 25.
A Katsina-Ala, ’yan bindigar sun kai hari ƙauyukan Kenvanger da Agbami da misalin ƙarfe 1 na dare.
An ce sun yi yunƙurin yi wa wasu matan da suka haihu fyaɗe, amma mazan ƙauyen suka kai musu ɗauki.
Wannan ya haifar da rikici inda ’yan bindigar suka buɗe wuta, suka kashe mutum ɗaya tare da raunata wasu.
A ƙauyen Agbami kuma, sun yi wa mutane da yawa dukan kawo wuƙa amma babu wanda ya mutu.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Udeme Edet, ya tabbatar da cewa an tura jami’an tsaro zuwa yankunan da abin ya faru a Makurdi.
Ya ce za su ci gaba da bai wa ’yan jarida bayanai, amma har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu wani ƙarin bayani.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Binuwai hari mahara
এছাড়াও পড়ুন:
Miliyoyin Mutane Sun Gudanar Da Bukukuwan “Idin Gadir” A Tehran Da Sauran Garuruwan Iran
A yau Asabar aka gudanar da bikin ranar ” Idin Gadir” a nan birnin Tehran, wanda ya tashi daga dandalin “Inqilab” zuwa dandalin ” Azadi” mai nisan kilo mita 10. Bisa la’akari da halin yake da ake ciki, an bai wa bikin na bana taken: Iran ce, takobin Zulfikar Na Imam Ali.”
Miliyoyin mutane ne dai su ka cika filin bikin na birnin Tehran da mutane su ka fara taruwa tun da tsakar rana, har zuwa bayan faduwar rana. A bisa kirdado kusan mutane miliyan 3 ne su ka taru a nan Tehran.
A cikin sauran birane da garuruwan Iran an yi wannan irin gangamin na raya ranar Idin Gadir wanda yake tattare da girmama shahidan da su ka kwanta dama sanadiyyar hare-haren ta’addancin HKI. Haka nan kuma mahalarta bikin na Gadir sun jinjinawa dakarun kare juyin musulunci na Iran da kuma sojojin kasar akan martanin da su ka mayarwa da HKI a daren jiya Juma’a da kuma a yau Asabar.