Gwamnati Ta Yi Barazanar Matakai Masu Tsauri Kan Masu Fasa Bututun Mai
Published: 14th, June 2025 GMT
Gwamnatin Tarayya ta bayyana aniyar ɗaukar matakai masu tsauri kan duk wanda aka samu da hannu a harkar fasa bututun mai da satar ɗanyen mai a yankin Niger Delta. Daraktan Tsaron Makamashi a Ofishin Mai baiwa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Tsaro (ONSA), Hon. Ojukaye Flag-Amachree, ne ya bayyana haka yayin wani taron masu ruwa da tsaki da kamfanin Pipeline Infrastructure Nigeria Limited (PINL) ya shirya a birnin Fatakwal.
A cewarsa, tuni sama da mutum 100 da ake zargi da hannu a wannan haramtacciyar harka an gurfanar da su a gaban kotu. Ya ce duk wanda aka kama, komai muƙaminsa, za a hukunta shi bisa doka. Ya kuma roki shugabannin al’umma da su ja kunnen matasa da yara kada su shiga lalata bututun mai.
Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin Fadar Shugaban Kasa Da Peter Obi Kan Tallafin Mai Ƴansanda Sun Damke Ango Da Abokansa Bayan Mutuwar Amarya A JigawaYa ce: “Muna roƙonku da ku yi magana da ‘yan uwanmu. Muna sanin mutanen da ke wannan harka, ku shawarce su su daina. Yanzu abubuwa ba kamar da ba ne. Fiye da mutum 100 tuni an hukunta su. Ko kai Soja ne, ko Janar ne, muddin aka same ka da laifi, za ka fuskanci hukunci.”
A nasa ɓangaren, Jami’in hulɗa da jama’a na PINL, Tarilah Alamieseigha, ya bayyana cewa kamfanin ya amince da bayar da tallafin karatu har guda 646 da wasu ƙarin shirye-shirye ga al’ummomi 215 da ke kusa da bututun Trans Niger Pipeline (TNP). Ya yaba da haɗin kan da ke tsakanin kamfanin da al’ummomi, wanda ya taimaka wajen bunƙasa samar da mai a ƙasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Kakakin Majalisar Jigawa Ya Tsallake Rijiya Da Baya, Tawagar Jami’an Tsaronsa Sun Ji Rauni A Wani Hatsari A Jihar
“Sauran motocin da ke cikin ayarin, ciki har da wacce ke ɗauke da shugaban majalisar, da ƙyar suka iya tsayawa wanda tsakaninsu mitoci kaɗan ne daga wurin da haɗarin ya afku,” in ji wani ganau.
Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa, an garzaya da jami’an ‘yansandan da suka samu raunuka zuwa babban asibitin Gumel a sume amma daga baya sun farfaɗo.
Da yake magana kan lamarin, mataimakin shugaban majalisar, Aqeel Akilu, ya yi godiya ga Ubangiji cewa, ba a rasa rayuka ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp