Ya kamata Isra’ila da Iran su kawo ƙarshen rikicin da ke tsakaninsu
Published: 14th, June 2025 GMT
Gwamnatin Tarayya ta roƙi ƙasashen Isra’ila da Iran da su daina rikici, su zauna lafiya su sasanta tsakaninsu.
A wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Waje ta fitar, ta bayyana damuwa kan yadda rikicin ke ƙara ta’azzara, inda ta nemi ɓangarorin biyu da su kai zuciya nesa don samar da zaman lafiya a duniya baki ɗaya.
Sanarwar ta ce faɗa da ramuwar gayya na jefa rayukan fararen hula cikin hatsari, kuma yana iya haddasa rikici mai muni a yankin Gabas ta Tsakiya, wanda hakan zai iya barazana ga tsaron duniya da kuma ci gaban tattalin arziƙi dunuya.
“Mu a matsayimmu na ƙasa mai son zaman lafiya, muna roƙon ƙasashen da ke rikici da su zauna su tattauna maimakon su ci gaba da faɗa.”
Gwamnatin Tarayya ta kuma yi kira ga ƙasashen duniya, musamman Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya, da su ɗauki matakai don hana yaɗuwar rikicin da kuma samo hanyar warware matsalar.
Sanarwar ta ƙara da cewa amfani da ƙarfin soji ba shi da amfani matuƙa, domin faɗa ba zai kawo sauƙi ba.
Najeriya ta ce a shirye ta ke ta bayar da taimako domin hana yaɗuwar rikicin da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gwamnatin tarayya Iran Isra ila
এছাড়াও পড়ুন:
An Kaddamar da Makon MNCH na 2025, Ya Rarraba Fakitin Bayarwa 6,000, Kayan C/S 500
Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da zagayen farko na makon lafiyar mata da jarirai da jarirai (MNCHW) na shekarar 2025 tare da raba fakiti 6,000 na kayan haihuwa da na’urar (C/S) 500 ga cibiyoyin lafiya a fadin jihar.
Gwamna Abba Kabir Yusuf wanda mataimakinsa, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya wakilta shi ne ya jagoranci bikin kaddamar da shirin a hukumance da aka gudanar a cibiyar lafiya matakin farko na Birji da ke karamar hukumar Madobi.
Ya yi nuni da cewa, wannan aikin ya hada da na rigakafi na yau da kullun ga yara, karin sinadarin Vitamin A, Rarraba gidajen sauro masu maganin kwari ga mata masu juna biyu.
Gwamna Yusuf ya jaddada kudirin gwamnatin sa na karfafa wa shirin rabon gidajen sauro ta hanyar ware naira miliyan 140 domin adana gidajen sauro da aka raba.
Gwamnan ya bukaci mata da masu kulawa da su yi amfani da damar da za a yi na tsawon mako guda don samun muhimman ayyukan kiwon lafiya da ake bayarwa kyauta.
A cikin sakon sa na fatan alheri, shugabar ofishin UNICEF a Kano, Mista Rahama Rihood Mohammed Farah, ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta kara yawan kwanakin hutun haihuwa da ake biyarwa domin kare lafiyar mata da jarirai da kuma inganta shayar da jarirai nonon uwa zalla.
Taron ya samu halartar kwamishinan lafiya, shugaban karamar hukumar Madobi, Hakimin Shanono, abokan cigaba, masu rike da mukaman siyasa da duk masu ruwa da tsaki.
COV/Khadija Aliyu