Wutar Lantarki Mai Ƙarfi Ta Yi Ajalin Mutum Biyar A Gombe
Published: 14th, June 2025 GMT
Aƙalla Mutane biyar sun kwanta dama wasu huɗu kuma sun jiggata sakamakon tsinkewar igiyar lantarki bayan dawo da wutar lantarkin mai ƙarfi a unguwar Tudun Wadan Pantami, ta jihar Gombe.
Kamar yadda wani mazaunin yankin Adamu Abubakar Kulani, ya shaidawa manema labarai, mummunan lamarin ya faru ne a daren ranar Juma’a yayin da aka kawo wutar lantarkin bayan sun kwashe kwanaki babu ita.
Ya ƙara da cewa sanadiyar wutar ta zo da ƙarfi ne ta haifar da tartsatsi, kana ta tsinka igiyar babban layin lantarkin wanda ta faɗa kan mutanen.
Tuni jama’ar yankin aka garzaya da waɗanda suka jiggata Baban Asibitin Ƙwararru na Jihar Gombe, domin duba lafiyarsu da basu kulawa kana sauran kuma da suka riga mu gidan gaskiya aka yi jana’izarsu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Wutar Lantarki
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnonin Nijeriya Sun Yi Ta’aziyyar Waɗanda Suka Rasu A Ambaliyar Ruwa A Adamawa
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp