Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Bude Kofofin Jahannama Ga Yahudawan Sahayoniyya
Published: 14th, June 2025 GMT
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bude kofofin wuta a kan haramtacciyar kasar Isra’ila ta hanyar mayar da martani kan harin da yahudawan sahayoniyya suka kai kan kasarta
Iran ta bude kofofin jahannama kan ‘yan sahayoniyya a matsayin mayar da martani ga mummunan zaluncin da suka kaddamar kan lardunan Iran da dama, wanda ya yi sanadiyyar shahadan mutane da dama da jikkata.
Bayan da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada cewa: Wajibi ne gwamnatin mamayar Isra’ila ta jira mummunan hukunci mai tsanani da kuma makoma mai daci kan abin da aikata, kuma bayan da sabon kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci Manjo Janar Muhammad Pakpour ya bayyana cewa: Sojojin kasar Iran za su bude kofofin jahannama kan kisan yara kanana, Iran ta fara kaddamar da hare-haren daukan fansa mai suna “Alkawarin Gaskiya na 3”, inda ta harba makamai masu linzami na ballistic da hypersonic kan yankuna daban daban na haramtacciyar kasar Isra’ila.
A cewar faifan bidiyo da aka wallafa, hakika Iran ta kai hare-hare da makamai masu linzami kan tsakiyar birnin Tel Aviv da kuma cibiyoyi da dama na soji da sansanonin sojin saman haramtacciyar kasar Isra’ila.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Amincewa Da Kasar Falasɗinu: Birtaniya Ta Gindaya Wa Isra’ila Sharuɗɗa
Firaministan Birtaniya, Keir Starmer ya shimfiɗa wa Isra’ila wasu jerin sharuɗan da ya ce idan ba ta cika ba, Birtaniya za ta amince da ƙasar Falasdinu.
A ranar Talata ne Mista Starmer ya ce idan har Isra’ila ba ta cika waɗannan sharuɗa ba zuwa watan Satumba Birtaniya za ta amince da ƙasar Falasɗinu.
Sharuɗɗan da firaministan ya gindaya sun haɗa da:
Amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta Bai wa Majalisar Dinkin Duniya damar sake shigar da agaji Gaza Amincewa da yuarjejeniyar zaman lafiya na dogon lokaci wanda zai ”samar da ƙasashe biyu” Tabbatar da cewa ba za a ci gaba da ƙwace Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da aka mamaye ba
Haka kuma Keir Starmer ya kuma sake jaddada buƙatun da Birtaniya ke da su kan Hamas da suka haɗa da:
Amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta Sakin duka sauran Isra’ilawan da take riƙe da su Amincewa ba za ta saka hannu a tafiyar da gwamnatin Gaza ba Miƙa duka makamantaBBC/Hausa