Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Sun Shaida Gamsuwa Da Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Tsakiyar Asiya
Published: 14th, June 2025 GMT
Yayin da taro na biyu na tattauna hadin gwiwar Sin da kasashen yankin tsakiyar Asiya ke kara matsowa, sakamakon kuri’un jin ra’ayin jama’a da kafar CGTN ta kasar Sin ta gudanar, sun nuna gamsuwa da hadin gwiwa bisa matsayin koli dake tsakanin Sin da kasashen nan biyar na yankin tsakiyar Asiya, a matsayin wata hadaka ta al’umma mai kyakkyawar makomar bil’Adama, wadda ke kara shigar da sabon kuzari, na daidaito cikin yanayin duniya dake kara shiga yanayin tangal-tangal.
Tun dai taro na farko na tattauna hadin gwiwar Sin da kasashen yankin tsakiyar Asiya, hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen biyar ya shiga wani sabon zango na ci gaba. Har ma kuri’un na jin ra’ayin jama’a suka nuna yadda kaso 90.4 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyinsu, ke ganin tsarin taron shugabannin Sin da kasashen na tsakiyar Asiya ya taka rawar gani a wannan fanni.
Kazalika, kaso 92 bisa dari na ganin ta hanyar mayar da kasashen tsakiyar Asiya daya daga muhimman jigon diflomasiyyar makwaftanta, Sin ta samar da wasu damammaki ga kasashen tsakiyar Asiya, na cimma burin sauye-sauye, da ci gaba da yin babban tasiri a shiyyarsu. Yayin da yanayin yankunan Turai da Asiya ke kara sauyawa cikin hanzari, kaso 88.1 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyinsu na ganin gina al’ummun Sin da tsakiyar Asiya masu makomar bai daya, na da muhimmancin gaske wajen karfafa tsare-tsaren kasashen tsakiyar Asiya, na samar da ‘yanci da daidaiton shiyyarsu. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: kasashen tsakiyar Asiya
এছাড়াও পড়ুন:
Sabunta Cinikin Ba Da Hidima, Masu Zuba Jari Na Waje Suna Ganin “Damar Da Kowa Ke Bukata A Kowane Lungu Na Sin”
Bikin hada-hadar ba da hidima na Sin wato CIFTIS na bana da ya kare a jiya a nan Beijing ya jawo hankalin kasashe da kungiyoyin kasa da kasa 85 da suka gudanar da baje koli da tarurruka, kusan kamfanoni 500, ciki hadda wasu daga cikin manyan kamfanoni 500 dake sahun gaba a duniya da manyan kamfanoni masu jagorantar bangarorinsu, sun halarci bikin, kuma an cimma nasara a fannoni sama da 900. A yayin da duniya ke fuskantar rashin tabbas, bikin CIFTIS ya karfafa mu’amala da kuma samun riba da juna.
Alkaluma na nuna cewa, a shekara ta 2024, jimillar cinikin ba da hidima na Sin ya fara wuce dala tiriliyan 1 a karon farko, wanda ya zama sabon tarihi, kuma ya kasance na biyu a duniya.
Masu zuba jari na waje suna kara zuba jari a Sin saboda babbar kasuwa. A halin yanzu, Sin ta zama abokiyar ciniki ta uku mafi girma a kasashe da yankuna 157, kuma ita ce kasa ta farko a fannin cinikin kayayyaki da ta biyu a fannin cinikin ba da hidima a duniya. A gun bikin na wannan shekara, Sin ta sanar da matakai da yawa, ciki har da “hanzarta aikin gwaji a yankunan gwajin ciniki cikin ’yanci da kuma yankunan ba da misali kan ayyukan ba da hidima na kasa” da “gaggauta bude kasuwar hada-hadar ba da hidima”. Wannan ya samu karbuwa sosai a wajen kamfanonin kasashen waje.
Ta hanyar tarurrukan baje kolin, duniya ba kawai ta ga sabbin abubuwa na tattalin arzikin Sin ba, har ma ta fahimci azamar Sin na hadin gwiwa da duniya da gina tattalin arzikin duniya mai bude kofa cikin hadin gwiwa. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp