Taron Koli Na Sin Da Kasashen Yankin Tsakiyar Asiya Karo Na Biyu Zai Ingiza Manufar Kara Dunkulewar Sassan Yankin
Published: 14th, June 2025 GMT
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya yi karin haske game da taron koli na Sin da kasashen yankin tsakiyar Asiya karo na biyu, wanda shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarta a Kazakhstan, yana mai cewa, Sin na da yakininta hanyar taro, ita da sauran kasashen yankin tsakiyar Asiya biyar, za su zurfafa dunkulewa, da amincewa da juna, da gina matsaya guda ta fuskar hadin gwiwa, da zurfafa daidaiton dabarun ci gaba, da daga matsayin hadin gwiwarsu a fannoni daban daban, da kara kuzarin gina al’umma mai makomar bai daya ta Sin da kasashen yankin tsakiyar Asiya.
Bisa gayyatar da shugaban jamhuriyar Kazakhstan Kassym-Jomart Tokayev ya yi masa, shugaba Xi Jinping zai halarci taron koli na Sin da kasashen yankin tsakiyar Asiya karo na biyu, tsakanin ranekun 16 zuwa 18 ga watan nan na Yuni. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Sin da kasashen yankin tsakiyar Asiya
এছাড়াও পড়ুন:
Super Falcons sun lashe gasar WAFCON karo na 10 bayan doke Maroko
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta mata ta Najeriya, Super Falcons, ta sake kafa tarihi bayan ta doke ƙasar Maroko da ci 3–2 a wasan ƙarshe na gasar WAFCON.
Yanzu haka Super Falcons ta lashe kofin karo na 10, wanda shi ne adadi mafi yawa da wata ƙasa ta taɓa lashewa a tarihin gasar.
ADC ce kaɗai za ta iya magance matsalolin Arewa — David Mark Dole gyaran kundin tsarin mulki ya haɗa kan ƙasa da shugabanci na gari — AbbaMaroko ce ta fara jefa ƙwallaye biyu cikin mintuna 25 ta hannun Ghizlane Chebbak da Sanaa Mssoudy, lamarin da ya tayar da hankalin magoya bayan Super Falcons a filin wasa na Rabat.
Amma Najeriya ba ta karaya ba.
A minti na 64, Esther Okoronkwo ta warware ƙwallo a bugun fenariti, sannan ta taimaka wajen cin ƙwallo ta biyu da Folashade Ijamilusi ta jefa a minti na 71.
Saura minti biyu a tashin daga wasan, Jennifer Echegini ta ci ƙwallo ta uku, wanda hakan ya sa ta girgiza duniyar ƙwallo.
Wannan nasara ta tabbatar da mamayar da Super Falcons ta yi a Afirka.
Ƙungiyar ta lashe dukkanin wasanim ƙarshe da ta buga a gasar WAFCON, kuma yanzu tana da kofuna 10 a tarihin gasar.