Birgediya Pakphur: Nan Gaba Kadan Za A Budewa “Isra’ila” Kofofin Jahannama
Published: 13th, June 2025 GMT
Sabon kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran Birgadiya Muhammad Pakphur ya aike wa da jagoran juyin musulunci na Iran wasika da a ciki ya bayyana cewa:
” Laifukan ta’addanci da HKI ta aikata, wanda ya yi sanadiyyar shahadar manyan kwamandojin da kuma malaman Nukiliya, haka nan mata da kananan yara da ba su ji ba su gani ba, ba zai wuce ba tare da mayar da martani ba.
Bugu da kari sabon kwamandan dakarun kare juyin musuluncin ya ce; Ba da jimawa ba, Za a buwa wa wannan haramtacciyar kasa kofofin jahannama.”
Birgeriya Muhamad Pakphur ya kuma kaddamar da ta’aziyya da kuma taya murnar shahadar kwamandojin, ya kuma yi godiya ga jagora da ya gaskata dakarun juyin.
Har ila yau Birgediya Pakphur Muhammad ya ce; Abinda ‘yan sahayoniyar su ka yi, wuce gona da iri ne da keta hurumin tsaron kasar Iran da zaman lafiyar jamhuriyar ta Iran, don haka ba zai wuce ba tare da mayar da martani ba.
Haka nan kuma ya ce: Kamar yadda jagoran juyin musulunci na Iran ya yi alkawali, wannan haramtacciyar kasar za ta fuskanci bakar makomarta da kuma mummunan sakamako.”
Wani sashe na wasikar sabon kwamandan dakarun kare juyin musuluncin na Iran ya kunshi cewa; Bisa dogaro da Allah, da kuma cika alkawalin da jagora ya yi, sannan kuma da daukar fansar jinanen shahidai kwamandoji, da masana da ‘yan kasa da ba su ji ba su gani ba, za a buewa wannan haramtacciyar kasa kofofin jahannama ba da jimawa ba.”
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Yi Furuci Da Halakar Sojan Guda Da Ya Jikkata A Zirin Gaza
Sojojin mamayar Isra’ila sun yi furuci da halakar daya daga cikin sojojinsu sakamakon raunukan da ya samu a Zirin Gaza
Majiyar sojojin mamayar Isra’ila ta tabbatar a ranar Asabar din da ta gabata cewa: Wani soja ya mutu sakamakon raunukan da ya samu kwanakin baya -bayan nan sakamakon tashin bam a kan hanyar wata motar soji a zirin Gaza.
Tun da farko, sojojin mamayar Isra’ila sun amince da mutuwar Sajan Reserve Vladimir Loza, mai shekaru 36, daga matsugunin Ashkelon.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan gwagwarmayar Falastinawa ke ci gaba da kai hare-hare da kuma kwantan bauna kan sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila a fagage da dama a zirin Gaza, lamarin da ya janyo hasarar rayuka da na dukiyoyi ga ‘yan mamayar.
A ‘yan kwanakin da suka gabata, rundunar sojin Qassam bangaren sojin kungiyar Hamas ta bayyana a ta bakin kakakinta, Abu Obeida, cewa: Dabarunta a wannan mataki ita ce ta “kokarin halaka makiya, da gudanar da hare-hare masu inganci, da kuma neman kame sojoji a matsayin fursunonin yaki.