Iran : Halin da ake ciki ba zai iya bada damar tattaunawa da Amurka ba
Published: 14th, June 2025 GMT
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmail Baghaei, ya zargi Isra’ila da yin zagon kasa ga diflomasiyya ta hanyar tsallaka jajayen layukan kasar Iran, da kuma ta’azzara rikici da kasashen yammacin duniya, yana mai bayyana cewa, ba za a iya yin shawarwari a halin da ake ciki ba.
Sanarwar dai na nuni da koma baya sosai a yunkurin diflomasiyya na Iran da kasashen Yamma, musamman yadda tashe-tashen hankula ke kara ta’azzara bayan matakin sojin Isra’ila.
Matakin na Isra’ila da hadin kai tare da Amurka na a matsayin kokari na kawar da duk wata dama ta cimma sakamakon shawarwari.
“Ba za a iya shawarwarin ba yayin da a lokaci guda ake barin gwamnatin kisan kare dangi ta kai hari kan Iran.”
“Ba Isra’ila za ta aikata irin wadannan laifuka ba tare da amincewar Amurka ba.”
Iran dai na kallon hare-haren da Isra’ila ta kai a baya-bayan nan a matsayin wani hari kai tsaye ga ‘yan kasarta.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Wulayati: Hanyar Zangezur Wata Shirin Amurka Ne Don Matsa lamba Kan Iran Da Rasha
Mai ba da shawara ga Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci ya bayyana cewa: Hanyar Zangezur wata shiri ne na Amurka don matsawa kasashen Rasha da Iran.
Ali Akbar Velayati mai ba wa Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran shawara kan harkokin kasa da kasa, ya dauki aikin Zangezur (arewa maso yammacin Iran) a matsayin wani aikin Amurka na matsawa kasashen Rasha da Iran lamba.
A cikin wani sako na tunawa da Sheikh Safi al-Din Ardebili, Velayati ya yi tsokaci kan batutuwan da suka shafi Azarbaijan da mashigar Zangezur, yana mai cewa, “Makiya Iran karkashin jagorancin ‘yan sahayoniyyan duniya da Amurka, suna neman ta hanyar tsare-tsare irin su mashigar Zangezur, don ciyar da manyan ayyukan siyasa a karkashin fakewa da wadannan tsare-tsare.”
Ya kara da cewa, manufar farko ita ce raunana gwagwarmaya da yanke alakar Iran da yankin Caucasus da kuma killace Iran da Rasha ta kasa a kudancin yankin.
Ya bayyana cewa: “Wannan aikin ba wai kawai wani bangare ne na shirin Amurka na maye gurbin Ukraine da yankin Caucasus a matsayin wani sabon fage na matsin lamba kan Rasha da Iran ba, amma ana aiwatar da shi ne tare da goyon bayan kungiyar tsaro ta NATO da kuma wasu kungiyoyin ‘yan kishin kasa na Turkiyya (Pan-Turkist).