’Yan bindiga sun kashe mutum 100 a Benuwe
Published: 15th, June 2025 GMT
An fargabar cewa ’yan bindiga sun kashe akalla mutum 100 a wani hari da suka kai a garin Yelewata da ke yankin Karamar Hukumar Guma a Jihar Benuwe.
Aminiya ta ruwaito cewa maharan sun far ma al’ummar garin na Yelewata ne a cikin daren ranar Juma’a wayewar garin Asabar.
Wutar lantarki ta kashe mutum 5, ta jikkata 13 a Gombe Damina: NiMet ta gargaɗi jihohi 13 kan barazanar ambaliyar ruwaWadanda suka shaida harin na Yelewata sun ce maharan sun mamayi garin ne kafin karfe 12 na dare, inda suka kwashe sama da sa’a biyu suna ta’annati ba tare da wani dauki daga jami’an tsaro ba.
Da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labarai na AFP, wani mai magana da yawun fadar gwamnatin Benuwe, Tersoo Kula, ya tabbatar da faruwar lamarin yana mai cewa maharan sun kone gidaje da dama.
Sai dai ya ce jami’an gwamnati da suka kai ziyara yankin na Yelwata sun samu cewa wadanda aka kashe ba su wuce mutum 45 ba.
Shi ma mai magana da yawun ’yan sandan jihar, Udeme Edet, ya ce jami’ansu sun yi musayar wuta da maharan.
Haka kuma, an wani harin na daban da ya auku an kashe sojoji biyu a garin Daudu, shi ma a yankin karamar hukumar ta Guma.
Wannan harin shi ne na uku a baya-bayan nan a garin Yelewata wanda ke kan iyakar jihar ta Benuwe da Nasarawa a cikin mako daya.
Ana iya tuna cewa a watan da ya gabata ne wasu mahara da ake zargin makiyaya ne suka kashe kimanin mutum 20 a karamar hukumar Gwer ta Yamma a jihar ta Benuwe.
Kungiyar Amnesty mai fafutikar kare hakkin dan Adam ta yi kira ga gwamnatin da ta dauki matakin dakile zubar jini da salwantar rayukan al’umma a kasar.
Amnesty ta ce gazawar gwamnatin Nijeriyar ce ta sanya asarar rayukan al’ummar kasar ta zama ruwan dare.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jihar Benuwe mahara
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan bindiga sun sace fasinjoji a cikin motocin bas a Kogi
Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi garkuwa da fasinjoji a cikin wasu motocin bas Toyota guda biyu a titin Itobe zuwa Ajegwu-Anyigba a Ƙaramar hukumar Ofu ta jihar Kogi.
An samu rahoton cewa, lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da misalin ƙarfe 5 na asubahi a tsakanin ƙauyukan Ojiwo’-Ajengo da Mamereboh da ke kan babbar hanyar.
Gwamnatin Yobe ta ƙaddamar da shirin amfani da ma’adanai Kotu ta dakatar da babban taron PDP na ƙasaAn ce masu garkuwa da mutanen sun yi amfani da wata tirela da aka kama wajen tare hanyar bayan shingen binciken jami’an tsaro, da ke kusa da wurin da lamarin ya faru.
Shedun gani da ido sun ce ɗaya daga cikin motocin bas ɗin mai lamba KG: KPA 622LG na kan hanyarta zuwa Abuja, tare da fasinjoji daga wata tashar mota a unguwar Ankpa da ke yankin Kogi ta Gabas.
Har yanzu ba a iya gano adadin fasinjojin da aka yi garkuwa da su ba zuwa yanzu, sai dai mun iya tabbatar da cewa ɗaya daga cikin motocin na ɗauke da fasinjoji ne daga yankin Ankpa, kamar yadda aka gano wasu takardu da wasu kayayyaki a wurin da lamarin ya faru suka bayyana.
“Motocin bas ɗin guda biyu suna kan hanyar Abuja ne a lokacin da suka ci karo da shingayen ’yan bindiga a safiyar ranar Alhamis. Dukkanin fasinjojin, ciki har da direban motocin bas ɗin biyu an yi awon gaba da su cikin daji,” in ji Unubi Ademu, wani mazaunin Achigili, a ƙauyen da ke maƙwabta.
Al’ummar yankin sun ƙara da cewa, jami’an tsaro da suka haɗa da sojoji da mafarauta da kuma ’yan banga suna ƙoƙarin magance lamarin.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan Jihar Kogi (PPRO), CSP William Aya bai amsa kira da saƙo ba lokacin da aka tuntuɓe shi har zuwa lokacin tattatara wannan rahoto.