Araghchi: Gwamnatin Amurka ta haramta wa Irakawa samun wutar lantarki
Published: 11th, March 2025 GMT
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya yi Allah-wadai da matakin da gwamnatin Amurka ta dauka na haramtawa al’ummar Iraki ‘yancinsu na samun wutar lantarki, da ma wasu ababen more rayuwa.
“Muna tare da al’ummar Iraki, kuma mun tabbatar da alkawarinmu ga gwamnatin Iraki na ba da hadin kai wajen tinkarar matakan da Amurka ta dauka ba bisa ka’ida ba,” in ji Araghchi a wani sakon da ya wallafa a shafin X.
Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto wani babban jami’an makamashi a kasar Iraki yana cewa, a halin yanzu Iraki ba ta da wasu hanyoyin da za su maye gurbin makamashin da ake shigowa dashi daga kasar Iran, lamarin da zai haifar da babban kalubale wajen biyan bukatar wutar lantarki a cikin gida musamman a lokacin bazara.
Tun da farko a ranar Lahadin da ta gabata, wani jami’in Amurka ya tabbatar da cewa Washington ta yanke shawarar kin sabunta yarjejeniyar da ta bai wa Iraki damar sayen wutar lantarki daga Iran.
Wani babban jami’in ma’aikatar wutar lantarki ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa “Gwamnati ta fara aiwatar da matakan gaggawa don rage tasirin matakin da Amurka ta dauka kan samar da wutar lantarki a Iraki.”
Wa’adin ya kare a ranar Asabar din da ta gabata, yayin da kumama’aikatar harkokin wajen Amurka ba ta tsawaita wa’adin ba, kamar yadda wata sanarwa daga ofishin jakadancin Amurka da ke Bagadaza ta bayyana.
Wannan shawarar wani bangare ne na matakin matsin lamba na Shugaba Donald Trump kan Iran, da nufin dakatar da abin da yake kira barazanar nukiliyar Iran, da dakile shirinta na makami mai linzami da kuma hana ta tallafawa kungiyoyin ‘yan gwagwarmaya a yankin.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: wutar lantarki
এছাড়াও পড়ুন:
Kano Pillars Ta Dakatar Da Babban Kocinta Bisa Rashin Katabus A Kakar Wasa Ta NPFL
Hukumar gudanarwa ta ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars ta sanar da dakatar da Mai Ba da Shawara a harkokin koyarwa na ƙungiyar, Ogenyi Evans, da Babban Koci, Ahmed Garba (Yaro Yaro), saboda rashin gamsasshen sakamako da ƙungiyar ke samu a farkon kakar wasa ta 2025/2026 Nigeria Premier Football League (NPFL).
A cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, ta bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne sakamakon jerin sakamakon wasanni marasa kyau da suka gaza cika tsammanin masoya da masu ruwa da tsaki a ƙungiyar.
Ya yanzu dai, kungiyar ta Sai Masu Gida ta buga wasanni takwas, inda ta samu nasara a biyu kacal, ta kuma tashi kunnen doki a wasanni 2, sannan suka sha kaye a wasanni huɗu — sakamakon da ƙungiyar ta bayyana a matsayin abin da bai dace da ƙungiya mai irin wannan matsayi ba.
A halin da ake, tsohon kyaftin ɗin ƙungiyar kuma mataimakin koci, Gambo Muhammad, zai jagoranci harkokin koyarwa tare da kocin masu tsaron raga, Suleiman Shuaibu, yayin da Coach Garzali Muhammad (Kusa) daga Junior Pillars zai shiga cikin tawagar masu koyarwa ta wucin gadi har sai an bayar da umarni na gaba.
Hukumar ta kuma jaddada aniyarta ta sake gina ƙungiyar domin samun sakamako mafi kyau da kuma ci gaba da kare martabar ta a matsayin ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa a Najeriya.
Daga Khadijah Aliyu