Kudaden Da Ake Karba A Kogin Hadejia Jama’are Daga Hannun Manoma, Ba Haraji Ba Ne – HJRBDA
Published: 14th, June 2025 GMT
Ya kuma bukaci da a ci gaba da hada hannu da masu ruwa da tsaki a fannin, musamman domin dakile kalubalen da ake fuskanta na rashin amfana da albarkatun da ke madatsar ruwan, musamman domin kara bunkasa fannin aikin noma da kuma kara samar da wadataccen abinci.
A nasu martanin daban-daban, wasu daga cikin manoman sun yi kira ga hukumar ta HJRBDA, da ta samar musu da Taraktocin noma a daminar bana da kuma lokacin noman rani.
Tawagar ta hukumar HJRBDA, ta ziyarci wuraren adana ruwa; ciki har da na Challawa, Dam din Gorge, wanda ke adana ruwa mai karfin tsawon zurfin mita miliyan 962 da Dam din Tiga, wanda ke iya adana ruwan da zurfinsa ya kai kimanin mita biliyan 1.968 da madatsar ruwan ta Ruwan Kanya da ke iya adana ruwan da ya kai zurfin mita miliyan 50.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Babban Jirgin Ruwan Kasar Sin Ya Nufi Yankin Tekun Kudancin Kasar Domin Gwaji Da Samar Da Horo
Kakakin ma’aikatar tsaron kasar Sin Jiang Bin, ya ce a baya bayan nan babban jirgin ruwan dakon jiragen sama na kasar Sin mai suna Fujian, ya doshi yankin tekun kudancin kasar, inda ya ratsa ta zirin Taiwan, a kan hanyarsa ta gudanar da gwaje-gwaje da samar da horo.
Jami’in wanda ya bayyana hakan a Talatar nan, ya ce hakan bangare ne na ayyukan da aka saba gudanarwa lokaci-lokaci a wani bangare na kirar jirgin.
Jiang Bin, ya yi tsokacin ne yayin da yake amsa wata tambaya mai nasaba da hakan da aka yi masa, yana mai cewa, bulaguron jirgin ya dace da dokokin kasa da kasa da ayyuka masu nasaba, kuma ba shi da wata nasaba da tunkarar wani sashe. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp